HIKAYAR SAIFUL MULUKI DA ALJANNA BADI'ATUL JAMALI
NA ƊAYA
A zamanin da, anyi wani sarki daga cikin sarakunan Ajamawa a Hurusan, sunan sa Muhammadu ɗan Sabbaki. Kowacce shekara yakan kai yaƙi ƙasashen Hindu, da Sindu, da Sinnu dama wasu ƙasashen na Ajamawa. Shi kuwa adalin sarki ne, ga shi kuma da jarumtaka kamar ache ya fi kowa. Al'adarsa kuwa itace yana matuƙar son labaru da hikayoyi da waƙoƙi da firarraki da labarun mutanen da ke gare shi.
A haka har sai da ya kasance duk wanda ya samu baƙon labari ba ya zamewa ko ina sai wurin sa, idan kuwa har labarin ya gamshe shi, sai aga ya cika mutum da kyaututtukan dinari da tufa guda dubu da ƙwarƙwara da taka-haye a matsayin sallamar sa.
Labarin wannan sarki ya shahara a cikin alƙaryu.
Sai dai kuma wannan Sarki, yana da wani mugun waziri, bahili, mai yawan hassada ga mutane. Idan sarki ya yi wa mutane alheri sai ya rinƙa yin hassada, ya riƙa cewa: "Irin abin nan da kake yi, shi yake ƙarar da dukiya, har gidaje su risbe".
Sarki kuwa ya kan mayar masa da martanin cewa " wannan hassadar kace waziri, al'amari dukkan sa ga Allah yake".
Ana nan rannan Sarki yaji labarin wani malamin mawaƙi, attajiri mai yawan alheri, sunan sa Hassan. Wanda darajar sa ta ɗaukaka, mutane sai yabon sa suke yi, suna cewa babu tamkar sa a wajen hikima da da-ɗa-ɗan hikayoyi. Sai kuwa Sarki ya aika aka kirawo masa shi.
Da zuwan Hassan, sai sarki yace masa " Ya Hassan, kayi sani cewa waziri na ya saɓa mini alkawari, ya zama maƙiyina domin dukiyar da nake baiwa mawaƙa da masu hikayu. Ina son yanzu ka gaya mani wani baƙon labari mai-ban al'ajabi wanda ban taɓa jinsa ba.
Idan har ya ƙayatar dani, zan baka yankin ƙasa ta guda ɗaya, kuma in sanya dukkan abin da na mallaka cikin hannun ka, in ɗora ka bisa kan waziri na dama gare ni, ka zamo mai yin hukunci ga talakawa.
Idan kuwa baka zo mini da abin da na ce maka ba, zan washe ka, in kore ka daga ƙasata".
Hassan yace "Ran sarki ya daɗe, an gama.. Amma idan ka yarda, kayi hakuri, ka bani jinkiri na shekara ɗaya tak. Bayan haka, zan baka labari wanda baka taɓa jin kamar sa ba, wanin ka ma bai taɓa jinsa ba daɗai a ƙasar nan idan Allah yaso".
Sarki yace "Jeka nayi maka wannan jinkiri, amma da sharaɗin banda fita, banda hawa, sannan kada kazo guri na sai bayan shekara ɗaya".
Daga nan Hassan attajiri ya durƙusa yayi bankwana da saeki ya wuce gida.
Da komawar sa gida sai ya zaɓi mutane biyar malamai marubuta mahankalta acikin bayin sa. Yace dasu " Ban neme ku ba sai don wannan rana mai kamar ta yau, ina so ku taimake ni bisa ga biyan buƙatar sarki, ku tsamar dani daga hannun sa"
Suka ce " Rayukan mu fansa ne gareka ya sidi, me kake da buƙata a tare damu?".
Attajiri Hassan yace " Ina son kowanne ɗayanku ya shiga ƙasashe, ya binciki malamai da ma'abota labaru da hikayoyi, ku tono mini labarin Saiful Muluki..
Ko a gurin wa kuka same shi, kuyi ƙoƙarin da ya baku labarin ku ruwaito shi gare ni, ko da dinare dubu ya nema a gareku ku bashi, ina son kuzo mini dashi.
Wanda duk a cikin ku yazo mini da wannan labarin a cikin ku, na ƴanta shi, zan bashi komai na duniya guda dubu, kuma zai zama shine wakilin gidana duka".
Daga nan bayi suka ɗauki guzurin tarin dukiya sannan suka bazama cikin duniya suna masu neman hamshaƙin labarin Saiful Muluki da Aljanna Badi'atul Jamali.
Ɗaya daga cikin su ya nufi Hindu da Sindu, na biyun su ya nufi ƙasar Ajami da Sinu, na ukun su ya nufi ƙasar Yamma, na huɗun su ya nufi ƙasar Sham, sai na biyar ɗinsu ya nufi ƙasar Masar. ..
mungode muna jiran kashina 2
ReplyDelete