TAKOBI A HANNUN MATA: TARIHIN FITATTUN MATA DA SUKA YI IKO DA KANO
Sadiq Tukur Gwarzo
1.0 GABATARWA
Ɗumbin Tarihi, ƙasaitacciyar masarauta, dogon zamani, sharafi, nasibi, iko da nufi, tumbatsa da nasara, duk sun tabbata ga kano. Mutane da dama sun yiwa kano kirari mai nuna kwarzantakar ta gami da ɗaukaka a tsawon zamunna, amma watakila mafi daɗaɗa rai shine wanda Farfesa Sani Zahraddin, babban limamin kano ya kawo yayin ta'aliƙin sa ga littafin Tarihin Kasuwanci da ƴan kasuwar kano wanda marigayi marubuci Maje Ahmad Gwangwazo ya wallafa, yana mai cewa: ana yiwa kano kirari da:- '
Ka misulu alfin,
Jalla babbar Hausa,
Gari ba kano ba dajin Allah,
ko dame kazo an fika'.
Manufar wannan rubutu shine zaƙulo wasu fitattun mata waɗanda suka taka rawar gani wajen iko da kano, ko ace waɗanda suka samu gagarumar nasarar aiwatar da muradun zukatun su sabili da nasabar su da masu zartar da iko a kano. Wannan birni na kano mai tsohon tarihi bai taɓa samun jagora mace ba a iya abinda muka riska, amma kwatan-kwacin mulkin da turawan mulkin mallaka suka aiwatar a ƙasar hausa (in-direct rule) ta hanyar sarakunan gargajiyar lokacin su, akan iya cewa an samu zamunnan da mata ke irin wancan mulki a sakaye. Don haka wannan rubutu zai bi diddigin irin waɗannan mata ne tun daga zuwan Bagauda kano har zamanin da muke ciki (2021) da yardar Allah.
2.0 KAƊAN DAGA TARIHIN KAFUWAR KANO DA SOMA IKO DA ITA
Akwai mabanbantan zantuka game da tarihin kano.
Amma dai ama iya cewa shekaru sama da dubu biyu da suka gabata, sun tabbatar da cewa akwai mutane masu rayuwa a Afirka ta yamma. Waɗannan mutane basu da wata sana'a sama da farauta. A wancan lokacin sana'ar noma bata shahara ba a duniya, don haka mutane suka fi dogaro da farautar namun daji a matsayin aikin yi. Lokaci yana tafiya, har labarin wani babban dutse ya fara zama shahararre a kunnuwan mafarauta. Dalili shine, akwai namun daji masu yawa a yankin da dutsen yake. Sannan ana iya haƙo Tama sinadarin haɗa ƙarfe a wurin. Waɗannan abubuwan suna daga mafi daraja a wancan lokaci. Domin akasarin kayayyakin farautar waɗannan mutane da duwatsu aka sassaƙa su, don haka suke da matuƙar buƙatar kayayyakin ƙarfe masu daraja da sauƙi wajen sarrafawa. Sunan wannan dutse DALA.
A bisa wata mahangar ta masana, wasu na ganin yankin Dala a matsayin wuri ne wanda k'abilu daban-daban (kazo-na-zo) ke taruwa domin shiga dajin dake kusa dashi don yin farauta. Shine har wasu ke ganin babu takamai_miyar ƙabilar da ta fara zama a yankin.
Haka kuma babu takamaiman wanda ya fara zuwa bakin wannan dutsen, wasu sunce mambobin wata ƙabila da suka taso daga wani birni mai suna Dahlak dake Habasha (daga baya sunan ya koma Dala) ce ta fara zama a wurin, daga nan aka sanyawa dutsen suna Dala, wasu kuma suka ce sunan wanda ya fara gina gida akan dutsen tare da fara rayuwa akai shine Dala. Don haka ake yiwa dutsen kachokan laƙabi da sunan sa.
Daga bisani dai, sai mutane suka fara zama kadan-kadan a gefen dutsen domin neman arziki. Maƙera na zuwa don haƙo tama da ƙarfe tare da sarrafawa, mafarauta kuma na zuwa don siyen ƙarafa tare da shiga farauta a dajin dake bayan dutsen Dala, kamar dai yadda yake a tarihi, za'a ga cewa mutanen da suka gabacemu sunfi rayuwa a wuri mafi daraja. Watau sa'ar da ruwa yake da tsada a wuri, sai kaga mutanen sun gina gari a wurin da ruwa yake, kamar yadda ya faru a garuruwan Makkah da wasun su.
Waɗanda suka ce Dala ne ya fara zama akan dutsen, sun cigaba da cewa ya rayu tsawon shekaru masu yawa akan wannan dutse, tare dashi akwai matarsa da 'ya'yansu bakwai, huɗu maza uku mata. Wani mai suna Garegaji aka bayyana a matsayin babban ɗansa, shine kuma akace uban wani ƙaƙƙarfa mai suna Nuzamu, Nuzamu kuwa ance shine ya haifi Barbushe. Barbushe mutum ne ƙaƙƙarfan gaske, wanda akace yakan iya kashe giwa ya saɓota a kafaɗa duk girmanta.
Littafin Tarihin Kano 'Kano chronicle' ya faro tarihin kano ne daga lokacin Barbushe. Shine ma har wata masaniyar tarihin Nigeria mai suna Elizabeth Isichei tayi hasashen cewa Barbushe ɗan k'abilar Sao ne saboda yadda akace girmansa da ƙarfin sa yake yafi kamanceceniya da ƙabilar ta sao. Ƙabilar sao kuwa itace tsohuwar ƙabilar da tarihi ya nuna cewa al'ummar kanembou (Kanem) sun samo tsatso daga garesu.
Tarihi dai ya nuna cewa a lokacin Barbushe shine sarkin mutanen dake zaune a zagayen dutsen Dala. Kuma suna da al'adar bautawa wani gunki mai suna 'Tsumburbura' wanda yake can kan saman dutsen dala, akan wata bishiya wadda take zagaye da katangu mai suna Shamus. Ance babu mai shiga wurin dodon tsafi tsumburbura sai barbushe. Duk kuwa wanda ya shiga sai ya mutu. Barbushe kuwa ance a saman dutsen yake rayuwa abinsa. Yana saukowa ga mutanen sa sau biyu a shekara domin gudanar da bikin bauta na al'ada. A lokacin mutane ke taruwa sosai a bakin dutsen na Dala suna jiran saukowar sarkinsu barbushe. Wanda yake saukowa gabanin faduwar rana. Yana mai buga ganguna. Sai yayi kirari da yabo ga tsumburbura, mutane suna tayashi. Daga nan akace sai yahau sama mutanen na biye dashi a baya har izuwa saman dutsen na dala. Wanda akace daf da isarsu saman dutsen sai mutanen su yanka hadayar da suka kawowa tsumburar, abinda sukan yanka kuwa shine ; bakin kare, bak'ar kaza, ko bak'ar akuya. Idan suka isa bakin d'akin bauta kuwa, sai kowa ya tsaya. Barbushe ne kadai ke shiga. Kafin shigarsa ance sai yayi kirari da kuwwa. Yana cewa "Sai ni magajin dala. Mutane dole su bini, ko sunƙi ko sun so". Daga bisani idan ya fito, sai ya jagoranci yin bautar tsumburbura, wadda ake zagaya dakin bauta ana rawa da kiɗa tsirara.
Idan an kammala kuma sai aci asha a wurin. Sannan sai barbushe ya fadi saƙon da tsumburbura ya bashi. Saƙon da a mafi akasari akace labari ne na abubuwan da zasu faru a shekara mai zuwa.
Duk waɗannan abubuwa ana hasashen sun faru ne a shekaru ƙasa da shekara ta 900AD (miladiyya) bayan wafatin Annabi Isah AS. Koda yake Marubucin littafin Kitab Al-buldan mai suna Al'yaqubi bayan yawace-yawacen sa da yayi a yammacin Afirka, ya ruwaito a shekarar 872-873 cewa "akwai wata masarauta awani wuri dake tsakanin masarautar kanem da tafkin kwara (dai-dai da ko kuma kusa da inda kano take a yanzu), mai suna 'HBSH'. Sunan mai mulkinta 'MRH' sunan birnin ta 'ThBYR'. Rashin wasulla a waɗannan kalmomi yasa shakku da jayayya a tsakanin masana tarihi. Domin wasu na hasashen sunan masarautar shine Hausa, (domin kuwa sunce HBshH na nufin Habasha ne), sunan da ake tsammanin daga cikinsa aka samo sunan Hausa. Wasu kuma na hasashen cewa masarautar ta auku ne a kusa da kano, amma daga baya kafuwa da ƙarfin da kano tayi ya rusa ta, ya kuma yi sanadiyyar komawar mutanen ta zuwa kanon.
Koma ya abin yake, daga baya littattafan tarihi na kano misalin 'Kano chronicle' (har yanzu ana taba-bar wanda ya rubuta shi), sun ruwaito cewa wani mai suna Bagauda ne ya zama sarkin kano na farko a tarihi a shekarar 999AD. Shi kuwa Bagauda wasu na cewa jikan Bayajidda na Daura ne, kuma daga garin Gaya suka taso shi da al'ummar sa, wai sunan su shine 'Abagayawa' (waɗanda suka zo daga gaya) ko ɗaya daga Gaudawa, shiyasa kuma ake kiransa da 'Bagauda', ma'ana, mutumin- Gaudawa, kamar yadda mallam bahaushe ya fitar da Bakibɗe daga Kibɗawa.
Wasu kuma suka ce sam, Bagauda ba jikan Bayajidda bane, yazo yankin Dala ne tare da wata runduna mai yawa kamar yadda Barbushe ya taɓa bada labarin zuwan su, kuma ainihin sunan sa shine kano, don haka daga sunan sa kano ta samo asalin sunan ta. Amma kuma wasu sun tafi akan cewa Kano, sumam waninshahararren mautum ne mainsana'ar ƙira wanda yayi sharafi a gefen tsaunin Dala, wanda har ɗaukakar sa ta sanya ake kiran gurin baki ɗaya da sunan sa. Don haka a mahangar su Bagauda daban, Kano daban.
3.0 FITATTUN MATA DA SUKA YI IKO DA KANO..
No comments:
Post a Comment