Zuwan Turawa na Farko Kano
Tun zamanin Sarkin Kano Ibrahim Dabo Turawa suka fara zuwa Njeriya ta Arewa domin wasu dalilai kamar sayen bayi da neman dukiya da mulki.
Turawa Sun somashigowa Nijeriya ta ruwa ne ruwa ta Libya suka biyo ta Katsina suka zarce har suka iso Kano. Su ma TuraWasun zo Wannan kasa ne
Kungiyoyi daban- daban da kuma a daidaiku.
Misalin-
Turawa da suka zo Kano akwai Dr. Barth da kuma Mr. Clappertom da Mr. Denham da Mr. Oudney, Wasu dag cikinsu ma sunzo ne da shiga irin ta Larabawa ta yadda ba za a gane su ba.
Mr. Clapperton ya ce, da isowarsa kasaitacciyar ganuwar gari ta Kano, ya yi matukar murna da farin ciki. Amma ya yi mamaki, maimakon ya fara ganin manya-manyan gine-gine irin na Larabawa a cikin gari, tun daga shiga cikin badala, sai da ya yi tafiya mai nisa kafin ya isa ga gine-
ginen cikin gari. Ba kamar yadda ya sami labari ba, shi dai birnin (Kano) mai girman gaske ne, ga jama'a masu yawa, wasu suna shiga wasu suna fita, amma kuma ba su kula da shi ba, saboda irin shigarsa da launin fatarsa.
Ya ce, saboda rashin kulawa da shi, shi ma bai kula da mutanen ba, ballantana ya ba da labarinsu.
Ya ci gaba da cewa, hakika ko a wancan lokacin akwai mutane masu yawan gaske da gine-gine a birnin Kano. Yawan mutane a Kano ya fi na kowanne daga cikin garuruwan da ya gani a Afirika, Akalla a cikin garin akwai mutum dubu talatin (30,000) ko dubu arba'in (40,000) a hautsine da bakin mutane daga nahiyoyin Afirika wadanda suka zo ciniki.
Garin kuma yana da yawan kududdufai. Daga Arewacin garin akwai wasu fitattun duwatsu guda biyu wato Dala da Goron Dutse, kowanne kuwa tsawonsa ya kai kafa 200. A dab da kofar gari kuwa wato à cikin badala akwai babban dakali wanda 'yangadi suke hawa su hango wajen gari.
A tsakiyar gari cikin wani kurmi akwai wata ƙasaitacciyar kasuwa tana cike da manya-manyan fatake da dillalan bayi. Sannan kuma suna yin ciniki ne ta hanyar furfure. Alal misali, wani ya zo da gishirinsa tafi daya, sai suka yi musaya da mai kifaye biyar. Wani kuma da ya kawo tunkiya aka saye ta da adadin wuri masu yawa."
Daga littafin
DAULAR FULANI A KANO, na Alh Nasidi Umaru (Galadiman Daji)
No comments:
Post a Comment