Yaki ya Kare da Turawa
Kamar yadda aka nuna a baya kadan, bayan da aka kashe Waziri Amadu, sai dakarun yakin Kanawa suka rarrabu. Wasu suka bi Galadima Mamuda, wasu Wambai Abbas, wasu kuma Madaki Kwairanga, dukkansu suka nufi Kano.
Shi kuwa jagoran yakin Turawa Lugga ya umurci sojoJin sintiri kada su sake auka wa jama'a masu dawowa Kano daga
Sakkwato, domin yana kokarin daidaitawa da Wambai Abbas wanda zai 6ullo ta wajen Gwarzo. Dama can Wambai Abbas ya aika wa Lugga takarda cewa zai dawo gida Kano. Nan da nan Lugga ya amince da wannan takarda cikin gaggawa wadda aka rubuta ranar 6 ga watan Maris 1905. Abbas ya shigo birni tare da mabiyansa ta kofar Kansakali. An kiyasta Wambai ya shiga Kano da kusan mutane dubu goma (10,000) har gami da wasu ragowar mutanen Waziri Amadu wadanda suka tsira.
Da suka iso suka sauka daga kan dawakinsu, sai suka isa damfamin Gwamna da farin ciki, Gvwamna Lugga ya fada wa Abbas shi fa ba ya fushi da wadanda suka yi yaki da mutanensa, muddin dai sun yi wannan yaki a kan gaskiyarsu. Nan da nan Lugga ya yi taron gaggawa shi da sauran mutanensa, sai ya umarci Wambai ya je ya zo da magoya bayansa wadanda suka mika wuya ga Turawa, kuma su bayar da kayan fadansu. A wannan taron ne Gwamnan farko a Nijeriya "Lord Luggard" ya tabbatar wa da Abbas ya zama sarkin kano na riko.
A nan kuma ya sanar da su matsayin Turawa a cikin mulkinsu da cewa, Turawa ba za su shiga harkar addininsu ko
al'adarsu ko dokokinsu ba, muddin dai ba su kauce wa tsarin Turawa ba. Lugga kuma ya tabbatar musu da cikakken mulkin Ingila a kan mulkin kasar gaba daya. Bayan Gwamna Lugga ya ba Wambai Abbas shugabancin Kanawa kafin a zabi sabon sarki, sai Wambai da jama'arsa suka
shigo cikin birnin Kano tare da wake-wake. Kidan badujalar soja ya koma kidan kamar haka:
Gajere bakin cikí,
An kirga kudi,
Ga mai su ya iso.
Tana kasa tana dabo,
An ki shukar maiwa,
Ga maiwar ta fito!
A lokacín da Gwamna Lugga yake nada Wambai Abbas ya zama Makaddas, ya karanta masa wasu sharuɗɗa na zama tsakanin su da turawa (Mani, 1978: 98-100).
Gwamna Lugga yace, "'yanzu tun da Turawa ke mulki a ƙasar nan, kuma sune zasu zaɓi wanda zai yi kowacce irin sarauta, amma za a bar mutame su yi abinsu kaɓar yadda suka gada. Zartar da al'amura duka yana wurin Gwamna kuma Gwamna yana iya tube sarki saboda rashin iya mulki.
Haka kuma a game da addinin Musulunci, Turawa ba zasu hana ci gaba da yadda ake yi ba. Dukkan gidajen shari'a da majalisar sarakuna za a tabbatar da ikonsu bisa ga yadda Razdan ya ga ya kyautu. Yi wa mutane azaba da tura daruruwansu cikin kurkuku ba imani, duk ba za a yarda da wannan ba. Kuma ba za a yarda akashe kwabo ba sai da sanin Razdan. Za a hana toshiya da cin hanci da mummunan zalunci duka. Wadansu irin laifuffukan kuwa a
hukunta su a dakin shari'a na lardi, wato shari'ar da ta shafi mutane da su ba 'yan kasar nan ne ba, ko ma'aikatan gwamnati duka can zaa kai su a yi musu shari'a. Gwamnati kuma za ta aza kudin harajin ta
bisa ga yadda Gwamna ya ga ya dace, sai dai harajin da Za a saka, ba za a bar zalunci ya shiga cikinsa ba. Masu fatauci da 'yan kasuwa duk za a taimake su yadda za su ci gaba da sha'anoninsu, arziki ya karu. Sarki ba zai saka musu harajin kome ba, sai irin abin da Gwamna ya ce ga yadda za a aza musu. Za a bar kowa ya yi anfani
da wurin da yake rike da shi, in gona ce ko gida, sai fa in gwamnati ta ga tana da bukatar wurin don yin wani aiki wanda zai amfani kasar baki daya.
Gwamna Lugga ya ci gaba da cewa, "Na ba da karfí a kan hana cinikin bayi, balle fa zuwa harinsu, amma ba zan ce kome akan
bayin da kowa yake da su a yanzu ba." Sai dai su ma wadanda suke bautar yanzu, in sun ga ana kwarar su, to, suna iya kai kara wurin Razdan. In an tabbatar lallai ana kwarar su, sai a kubutar da su a yanta su dole".
Gwamna Lugga ya kara bayyanawa Wambai cewa, ba yaso yaga masu zaman banza, kowa ya yi aiki. Ba ya kuwa son bara irin duk mai jin karfi lalle ne ya yi aiki, kuma a biya shi lada a aikinsa. Kuma zuwa gaba, ba sarkin da aka yarda ya ajiye rundunar masu yaki. ldan har sarki ya sa talakawansa su yi wani abu, sa an na ya ga sun ki bin umurninsa, to, abin da zai yí shi ne ya je ya fada wa Razdan. Kuma duk makamai ba a son a ga kowa da su, sabodahaka KOwa sal ya mika nasa a tara wuri daya.
Kuma wanda duk aka gani da makami muddin bai sami izini daga wurin Razdan ba, to, a a hukunta shi. Kuma duk irin abin da aka kai don sayarwa ga soja, to Su saya su biya dole. Ita Sakkuwato kuwa ita ce gaba, amma ba Za akai mata gaisuwar bayi ba.
Gwamna Lugga ya rufe jawabinsa da cewa, "Gwamnati ba ta da niyyar tayar da mutane daga kan al'adunsu." Ya ce burinsu shi ne
su yi kokarin yadda za su san al'adun wannan kasa har su fahimce su
SOsai, su gane abin da jama'a suke so da wanda ba su so. A nan ne Gwamna Lugga ya tabbatar wa da Wambai cewar Turawa fa sun zo kenan ba kuwa za su tafi ba."
No comments:
Post a Comment