Monday, 15 February 2021

03. ZUWAN TURAWA KANO: MAHANGA TA 3

 Dokta Miller Kano

Bayan yakin Basasa da yakin Damagaram na daya da na biyu, Dakta Miller ya iso  Kano, Babu ma wanda ya gane Bature ne, domin ya yi shigar tufafi irin na mutanen wannan kasa. Dokta Miller

shi ne Wanda ya kawo addinin Kirista nan Kano har kuma ya tsufa ya mutu a Ɓukur, Miller sanannen Baturen Mishan ne a Kano. Miller ya iso ne tare da wasu Turawa da ayarin wasu 'yan kasa suka taso tun

daga Ikko da nufin zuwa Kano. Tafiyar wata biyu suka yi da Kafafuwansu, sannan suka iso Kano da bazara, Sarkin Kano Aliyu ya sauke su a gidan baki, A yayin da suka zo Kano sun yi murna da

ganin ganuwar birni mai girma fiye da yadda ma aka ba su labari.

Dokta Miller ya ce har da dai Sarki ya sauke su, amma bai yi musu karɓar kirki ba. Sun gaya wa Sarki cewa su masu wa'azi ne na Kirista kuma zasu gina makarantu da dakin shan magani. Sarki ya ce bai yarda ba, domin kuwa kowane irin magani akwai shi a Alkur'ani. 

Da suka koma masauki, saboda ganin Sarki bai amince da zuwansu ba, mutanen gari suka rika tsammanin ma za a kai su Jakara a sare su.

Sai yaransu masu daukar musu kaya suka rika zare jiki sunna guduwa.

Anan Waziri Amadu ya baiwa Sarki shawara kada ya kashe su tun da

yake sun taho da amana, a bar su su koma inda suka fito. Sarki ya umarce su dasu bar masa ƙasar sa.  To, yaransu duka sun tsorata sun gudu. Waziri ya roƙar musu ka  Sarki ya ba su jakuna dari (100) masu daukar musu kaya.

No comments:

Post a Comment