Kanawa sun Gwabza da Nasara
Tuni an ba da labarin zuwan Turawa na farko a zamanin Sarki Ibrahim Dabo, an kuma yi bayanin zuwan Dakta Miller da zimmar ya yaɗa addinin Kirista a kasar Kano. A wannan dan karamin sashe kuma an samu jin yadda Turawan Mulkin Mallabe suka gwabza gwagwarmayar
da irin kokarin Turawa wajen ganin sun ci Kwantagora da Bidda da yaƙi, nan da
labarun yadda aka ci wadannan birane ya bazu a ko'ina a kasar Hausa.
Saboda haka dole babban birni irin na Kano su ma su shiryawa zuwan Turawa. Turawa sun iso kogin kofar Zariya sun sauka, Kanawa sun sami labari akan haka.
Kuma dukkan kasashen Arewa dole su zuba wa Kano ido wadda itace babbar cibiyar Arewacin Nijeriya. Domin babu wani gari mai cikakkiyar ganuwa da tsaro da dakaru masu yawa da kuma
kayayyakin yaki irin na Kano. To, amma abin da ya kawo zuwan
Turawa Kano da wuri shi ne, Magajin Garin Kafin Ɗanyamusa ne ya
kashe Rasdan din garinsa wanda ake kira Kyaftin Maloney.
To, sai ya gudo Kano inda Sarkin Kano ya karbe shi, ya ba shi mafakar siyasa.
Dadin dadawa, Turawa sun sami labarin wai Kano tana ta shirye-shirye ta afka musu da yaki. Wannan shi ne dalilin da yasa hankalin Turawa ya koma kan Kano kurum, kuma suna tsammanin
yakin Kano zai fi na ko'ina wahala, saboda girman mayakanta. Turawa sun dakata a Zariya sai da suka haɗa
babbar runduna mai yawan hafsoshi ashirin da shida (26) da kanana(13) da likitoci (2) da dakaru bakar fata (800)
dabindigogi hudu (4) masu karfin milimita (75) da manyan bindigogin yaki biyar (5), sannan suka nufo Kano da sanyin Safiya.
To, a ranar 29 ga watan Janaiu 1903, Kanar Morland wanda ake kira Maimadubi ya jagoranci wadanda za su yi yaki da kano.
A ranar da sukanfara tahowa daga wannan ƙauye zuwa wannan kauye, har suka iso Bebeji wani gari wanda bashi da nisa da iyakar Zariya zuwa Kano. Daga nan Turawa suka fara fahimtar ba a yi maraba da zuwan su ba.
Da ma Sarki ya umarci sarakunansa da kada wanda ya buɗewa Nasara kofa idan sunzo garin sa. Da isowar Turawa Bebeji aka soma faɗa dasu, suka kashe sarkin BABEJI JIBIR.
Da jin abin da ya faru a Bebeji, saindukkan kauyukan da ke kan hanyar zuwa birnin kano suka karaya, sai suka rika gudu suna shiga cikin Birnin Kano.
Kanar Morland da dakarunsa sun yi kokarin su karya kofar birni abin ya fasKare su. To, sai suka ci gaba zuwa wata kofar wadda da ma wani Bature soja, Laftana Gyar, ya isa tare da jama'arsa. Ita ma ta gagare su budewa. Ana nan a kan haka, sai wani soja ya yi dabara ya jefa igiya
kan garun badala saboda ya yi kokari ya leka cikin gari. Da dai jama'a suka hangi jar hularsa, sai suka rika shekawa a guje cikin gari.
Da soja suka ga banza ta fadi sai suka harbe kyauren ya fadi, suka
rika bin mutane suna harbewa. Mutane suka rude, garin gudu wannan ya buge wannan, da haka su da kansu suka rika yi wa junansu rauni.
Sallama Jatau da Sarkin Shanu Dangwari, wadanda Sarki ya bar wa jiran gari, suka fito suka tari Turawa. Da suka
fahimci abin ba mai sauki ba ne, sai Sallama Jatau ya nufi gidan
sarki inda ya debe wasu daga cikin iyalin sarki ya fita da su. Sarkin
Shanu kuwa ya hau kan bene ya dinga harbin Turawa, su ma suna
harbin sa har dai suka yi nasarar harbe shi. Sannan soja suka wuce, suka isa har gidan sarki, amma sai Sarkin Gida ya ce, babu wanda ya isa ya shiga gidan. Ana cikin
Wannan ja-in-ja sai Sarkin Gida ya zare takobi ya sari wani Bature a
hannu ya yi masa mummunan rauni. Nan take aka harbe Sarkin Gida
ya mutu. Da ganin Turawa sun shiga cikin gidan, sai wata kuyanga ta
yi kokarin ta sanya wuta a taskar sarki, inda yake ajiye kayan
yakinsa, amma sai wata 'yar'uwarta ta hana ta. Haka dai sojan nan suka bi ko'ina cikin gidan sarki suka bincike, sannan suka je suka bude gidan yari duka fursunoni suka fita. Turawa suka kame Kano ta koma karkashinsu.
No comments:
Post a Comment