A wannan kasuwa akwai kayan sayarwa irin na Masar da Mali da Libya da Moroko da na Aljeriya. Wadannan kaya na Kasashen waje suna tsakiyar kasuwa, kuma akwai kayan gida kamar wadanda aka saka ko aka kera, wadansu kuma aka rina da kuma kayan sawa wadanda aka dinka kamar riguna da taguwoyi. Kyallayen tufafi da 'yan turamen sukari da ake sayarwa da gishiri da manda da 'yan kayayyaki na gabas duk akwai su a kasuwar.
Ga kuma tukurwa da ake daura gadon amarya da dirkoki da zana da
ingirici da shuci duk suna a bangare daya. Ga kuma kayan aiki irin
su garma da fartanya da lauje da wuka jefi-jefi. Akwai awaki da
tumaki da shanu da dawaki har da rakuma na sayarwa. Ga tayakan
hatsi da dai sauran kayayyakin sayarwa da yawa ko'ina barkatai a
cikin kasuwa.
Har wa yau, a kasuwar Kurmi, akwai manya-manyan dillalai masu saye da sayar da kayan kasashen waje. Duk kayan da aka sayar
za a rubuta sunan dillalan a kan kayan da Arabiyya, bayan an tafi da
kayan idan an ga wani ha'inci sai a dawo wa da dillalin da ya sayar
da kayan ya biya kudin. Saduwa da sarki ta fi fatauci, ta fi a duƙawa gona noma.
Baturen ya ce, ya sadu da sarki ido-da-ido domin lokacin da suka isa
Kano Sarki ba ya nan, ya yi hawan salla ya tafi Dala. Bature ya ce,
lokacin da sarki ya dawo, sai ya tsaya a kan doki ya yi wa mutanensa
huduba. Sarki ya ce, lalle mutane su dage haikan kan daukaka
addinin Musulunci babu karkata, su yi imani da Allah daya, su fitar
da zakka su tsayar da salla su yi layya ga wanda ya sami iko. Bature
ya ce, bai ankara ba sai ya ji an sake cewa Sarki ba ya nan. Wato
Dayan hudubar da ya yi, ya juya ya tafi Fanisau, wani gida da ya
shirya a matsayin sansanin yaki, mil biyar daga birni. Bature ya nemi
abokan tafiyarsa wadanda suka rako shi, su ne El-Wardee da
latsallah wasu Larabawa, suka raka shi Fanisau. Ya ce da shigar sa
Cikin garin Fanisau sai ya fara ganin mayakan sarki sahu-sahu cike
da gari. Aka ce da shi idan Sarki ya gama hada rundunarsa ta yaki zai tafi domin yaƙar Malam Dantunku.
Bature ya ce, haba! Tun kafin su iso nake
ganin gidajen mayaka na kan hanya cike da mayaka, idan dukkan mayakan da ya gani sun hadu za su bi sarki har ya yi mamakin ganin wasu daga cikin abokan ayarin su sun zo fanisau wurin sarki sun taho masa da dawaki na sayarwa. Su
Da isar wannan Bature aka fara kai shi gidan Wambai domin
masa iso a sada shi da Sarki. A nan ya dakata kafin ya sami ganin
Sarki, da ya bi Wambai gidan sarki kafin su shiga ya fara ganin gidajen masu gadi gefe da gefe daga waje. Yana shiga sai ya ga abin mamaki dukkan katangar gidan daga ciki an lullube ta da fatar garkuwar yaki. Kofar gidan kuwa akwai dubban jama'a suna harkokinsu. Ana ta kade-kade da bushe-bushe, bayan an wuce wani
fili akwai wani katon daki inda ya hangi mutane suna kewaye da
Sarki, an rataye takobi a bango, bayi suna yi masa fiffita. Da ganin
Sarki hakika ka san Bafulatani ne mai cika ido da kwarjini. Dogo ne kwarai, fari a jikinsa kamar tagulla. Hamshakin Sarki, kamilalle,yana sanye da kayan zina irin na Masar, A hagu da dama, bayi da
ya'yan sarki da manyan mutane suna zaune a kewaye da shi,
shikuma yana zaune a kan gado. Baturen ya ci gaba da cewa, yadda yaga Sarki ya san malami ne masani, mai ilimi, yana ma ta Larabci tare da Larabawa da suka raka shi, Ya mika wa Wambai takardar Shehun
Barno tare da agogon da ya aiko wa Sarki. Sarki yana Karata takardar a zuciyarsa, sai ya ga yana ta murmushi da yake nuna Sarki yana farin ciki da aiken Shehu. Sai ya ce, agogon a ba wa wani balarabe don ya koyi sanin lokaci, shi kuma ya sanar da Sarki lokaci. Daga nan kuma baturen ya fito da tasa gaisuwar ta takobi da faranti na shan shayi da kwanuka 5 na faranshi da yadin zani rawaya 25 da yadi 4 na siliki da kwanuka 5 da madubi mai kawo nesa da kananan akwatuna guda 3 da wukake 4 da reza 2 da da farin rawanl da
tagullolin wasan yara da karyayyen ma'aunin zafi 2 da sanyi da almakashi. Sarki yayi murna kwarai da gaske, ya yi godiya yi, Sarki yace da wambai a kai baturen masauki, idan Allah ya dawo da shi lafiya da daga fagen gama zai haɗa shi da Muhammadu Bello ya yi ziyara ya dawo lafiya.
Da Baturen Musulmi ya isa masaukin sa sai ya tarar har sarki ya sa an kai masa
shinkafa buhu 2 da raguna kiwatattu 2 da tandun mai 2 da sukari 2 da kayan cefane da kudi a matsayin shiɗa a gare shi.
Da Sarki ya dawo daga yaki sai ya haɗa shi da jama'a suka kai shi Sakkwato suka dawo da shi Kano. Daga nan ne kuma ya tafi Borno zuwa Libya sai gida (Clapperton; 1829).
No comments:
Post a Comment