Sunday, 21 February 2021

GARIN DANMAJE

 Garin Ɗan Maje


Sadiq Tukur gwarzo

A yankin Dawakin Kudu, cikin ƙasar Kano, akwai wani tsohon gari da ake kira Ɗan maje.

Babu takamaimen lokacin da garin ya kafu, amma an tabbatar da cewa sa'ar da mutane suka soma zama a wannan gari garin kano bai samu kafuwa ba.

 Wani mai suna Maje daga maguzawan farko ne yafi shahara acikin mazaunan garin na farko, shine kuma ya zama shugaba a garesu, daga bisani sai ɗansa  ya gajeshi wanda ake kira Ɗan Maje.

Daga nan garin ya samo asalin sunan sa.

Labarin Rijiyar Gidan Matage

Akwai babban abin mamaki game da wannan rijiya. Ana iya cewa itace silar kafuwar garin.

Wannan rijiya ta samu kafuwa shekaru masu tarin yawa da suka gabata, babu labarin wanda ya haƙe ta, amma ana danganta ta da ƙwanƙwamai wajen bayyanuwar wasu ababen mamaki, ana kuma haɗata da rijiyar Kusugu ta Daura wajen nuna tsufan ta,  sannan har yanzu babu wani abu na zamani da take karɓa.

Ba'a ɗebo ruwa da gugan ƙarfe ko na fata har yau daga cikin wannan rijiya, idan kuwa mutum ya so jarraba haka, anan take zai ji an fisge gugan daga cikin ta, idan akayi rashin sa'a ma har da shi kansa za a haɗa a fizga daga cikin rijiyar.

Sannan duk wani yunkurin da akayi wajen yi mata ɗaurin baki da bulon siminti na zamani yaci tura.

 Ance sau tari idan abu ya ɓata a kogin wudil, har akayi nema aka rasa, wannan rijiyar ake zuwa a bincika sannan a ganshi. 

  Akwai labarai mabanbanta da aka ji dangane da ɓullar kwale-kwale a ƙasan rijiyar a lokuta daban-daban, wanda hakan ke nuna kai tsaye idon rijiyar haɗe yake  yake da kogi.

  Akan jiyo kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a wasu lokutan daga cikin wannan rijiya, da kuma wasu abubuwa na mamaki masu hana bacci da bada firgici.

Babu ganuwa irin ta kano a garin Ɗanmaje wanda ke nuni da raahin tumbatsar sa a tsawon lokaci, amma dai idan labarin yaki ya iso garin, Dawakin kudu, Tamburawa da Kano mutane ke guduwa domin tsira.

Akwai abubuwa masu yawa a tattare da ita wanda sannu a hankali bincike zai fito dasu


 

No comments:

Post a Comment