Tuesday, 21 December 2021

MATSAYIN YESU KIRISTI: ƊAN UBANGIJI KO KUWA 'DAN AIKEN SA NE?

 MATSAYIN YESU KIRISTI: ƊAN UBANGIJI KO KUWA 'DAN AIKEN SA NE?

  

SADIQ TUKUR GWARZO

    


A duk Ranar 25 ga watan disamba na kowacce shekara, mabiya addinin Yesu Kiristi suna bikin tunawa da ranar Haihuwar Annabi Isa A.S

  Haka kuma, Mabiya addinan Islama da na kiristanci, dukkansu sun amince da wanzuwar Yesu Almasihu, kuma suna darajanta shi.

  Sai dai, yadda mabiyan kowanne daga addinan biyu suka ɗauka game dashi na da bambamci.

   A addinin musulunci, ya zo cewa Yesu Kiristi Mutum ne mai daraja, wanda Ubangiji Allah abin yiwa bauta ya aiko domin yayi wa'azi da kaɗaita shi.

  Haka kuma mahaifiyarsa, an yabeta a matsayin mace mai gaskiya. A duba Alkur'ani (3:45) da (19:17)

   Sai dai a kiristance, ba haka abin yake ba.

   Domin kuwa da yawan mabiya addinin suna ɗaukar Yesu Almasihu a matsayin Ubangiji, yayin da wasu ke ɗaukarsa a matsayin ɗa-ga Ubangiji.

   Don haka, wannan saɓani, zai warwaru ne kurum idan mukayi duba izuwa littattafai masu tsarki na waɗannan addinai guda biyu.

  Da fari dai, acikin Suratu Maryam cikin littafin Alqur'ani mai girma, maganar Ubangiji ta faɗi labarin yadda aka haifi Yesu kiristi ba tare da Uba ba, har mutane ke tuhumar mahaifiyarsa da cewa "yake 'yar uwar Haruna, hakika kinzo mana da bakon abu, gashi kuwa mahaifinki ba fasik'i bane, mahaifiyarki kuma ba mai bin mazaje bace".

   Sai kuwa Maryamu tayi musu nuni da Jaririn tana nufin su nemi ba'asi daga gareshi. Har suke cewa gareta "tayaya zamuyi magana fa wanda ya ke cikin zanin goyo?"

  Ai kuwa Sai Yesu Almasihu da ke zanin goyo ya amsa da cewar "Ni bawan Ubangiji (Mai suna Allah) ne, ya bani littafi ya kuma sanyani Annabi".

   "Ya sanya albarka a gareni a duk inda na kasance, yayi mini wasicci da Sallah da Zakkah matukar ina raye".

  "Kuma aminci ya tabbata a gareni a ranar haihuwata, da ranar mutuwata, da ranar da za'a tashe ni rayayye".

  Sai Ubangiji yace "wannan fa shine Isa Dan Maryamu.."(karanta har karshen Aya)

 Maryamu: 26-34


A littafin Babil mai tsarki, nan ma ana iya cewa yazo a wurare daban-daban cewar Yesu Almasihu ba shine Ubangiji ba.

   Sahabban Yesu kiristi irinsu Matthew, Mark, da Luke waɗanda suka ruwaito zantukan sa har suka haɗa zantukan izuwa littafin Babil, sun tafi akan cewa Yesu kiristi bai taɓa kiran kansa da suna Ubangiji ba. A duba Matthew 10:18, da Matthew 19:17.

   Abinda wasun su suka yadda shine: shi ɗan Ubangiji ne, saboda haihuwarsa da akayi babu uba da kuma karamomin da ya nuna a zamanin rayuwarsa.

   Haka kuma, ɗaukarsa a matsayin ɗan Ubangiji na nufin kasancewarsa Mutumin kirki nagartacce, don haka ba shi kaɗai ba, duk wani nagartaccen bawa su kan kira shi 'ɗan Ubangiji'. A duba Matthew 23:1-9 don a tabbatar.

   Shikuwa Paul, wanda shima Maruwaicin Babil ne, ya aminta da cewar Yesu Kiristi ba Ubangiji bane.

  A cewar sa, Yesu kiristi ne wanda Ubangiji ya soma halitta, don haka yayi amfani da shi wajen halittar sauran halittu kamar yadda yazo a Colossians 1:15 da 1 corinthians 8:6.

     Saboda haka, kasancewar Paul, John da sauran manyan maruwaitan littafin Babil mai tsarki, sun tafi akan cewar Yesu Almasihu shine halittar Ubangiji na farko kuma mafi daraja, har ma Paul ɗin ya ruwaito a Babil cewa yaji Yesu na faɗin "The Father is greater than I". Watau "Uban, ya fificeni" sai waɗanda suka biyo bayansu sukayi shishshigin ɗora masa laƙabin shi ɗan ubangiji ne, wasu kuma suka ce shi Ubangiji ne kachokan.

  Ga kaɗan daga ayoyin Babil da suke nuna Yesu Kiristi ba Ubangiji bane, bawan Ubangiji ne kamar yadda muka kawo Yesu ɗin ya faɗa da bakinsa daga Alkur'ani:-

   "Men Of Israel, listen to this:Jesus of Nazareth was a Man accredited by God to you by miracles.." Acts 2:22

 "God Has raised this Jesus"

 Acts 2:32

 "God Raised up his Servant"

 Acts 3:26

  "The Lord of Abraham, Isaac, and Jacob, the Lord of our fathers, has your holy servant Jesus"

 Acts 3:13

  A wani kaulin ma, shi da kansa Yesu Almasihu ya faɗi cewa bai san ranar da za'a tashi alkiyama ba, don haka shi fa bawan Ubangiji ne (Matthew 24:36).

 A Wani wajen kuma an ruwaito Yesu Kiristi yana neman taimakon 'Eloi', ko 'Eloh' wajen tabbatuwar ayyukansa, kamar yadda akace ya faɗa yayin da Yahudawa zasu halaka shi cewa "ELOI, ELOI, LAMA SABACHTANI  (Markus 15:34. ) 

Ma'ana,  "Ubangijina,  Ubangijina, don me ka yasassheni?"

  Don haka, idan har Yesu ya kasance ubangiji, me zaisa ya rinka neman taimakon wani kuma, sannan me zaisa ya rinka faɗawa mutane da kansa cewar shi bawa ne ga ubangijinsa ELOHIM?

  Koda yake, wannan ƙin gaskiyar karamin aiki ne ga manyan malamai mabiyansa idan muka kalli Babil, Song of Songs (5:16), inda kai tsaye akayi busharar zuwan wani Annabi mai suna 'מַחֲמַדִּים' cikin harshen yahudawa (wanda aka fassara haruffan da m-ħ-m-d-y-m, ake kuma furtasu da meħmadim ko

maħammaddīm don girmamwa bisa karin 'im'), amma kai tsaye sai sukace sam kalmar ba Annabi Muhammad take nufi ba, wai tana nufin wani wanda kowa keso ne ko kuma wani mafi cancanta..


MENENE SUNAN SA?

Marigayi Sheikh Ahmad Deedat ya yi dogon nazari akan sunan Ubangiji kamar yadda yazo a cikin littafin Babil mai tsarki har ya wallafa littafi a game da haka wanda ya sanyawa suna 'MENENE SUNAN SA?, ga kaɗan daga abinda shehin Malamin ya ke cewa:-

Akwai wasu Mutane 'yan ɗarikar Jehovah daga cikin ɗarikun kiristoci masu zagayawa gida-gida ga 'yan uwansu kiristoci suna tambaya menene sunan sa? (Suna nufin menene sunan Ubangiji)

 Sai kaji kirista yace "Ubangiji"

  Sai suce "Ubangiji ai ba suna bane, abin bauta ne".

  Sai su kara tambaya, "to menene sunan sa?"

  Sai kaji kirista yace "Sunan sa Uba (Baba God)"

  Sai suce masa "shin Ubanka Ubangiji ne?"

  Nan take kirista zaice "A'a".

  Sai su sake tambayarsa, "to menene sunan sa?"

  Idan yayi shiru babu amsa, sai suce  "Jehovah shine sunan sa".

  Waɗannan kalmomi guda huɗu da ake kira Tetragammation, sun hana kowa yabisu dalla-dalla don zakulo asalin ma'anarsu.

   Amma idan ka tambayesu, menene 'Je-ho-va-h', sai suce maka 'Y-H-W-H', watau kalmomi huɗu da suka zo a littafin Babil mai tsarki na yaren Ibraniyanci.

  Kasancewar tsohon rubutun Ibraniyanci da Larabci babu wasulla, waɗancan kalmomi na YHWH (ko JHWH saboda matsalar J da ake sauyata da Y a larabci, kamar misalin Jacob da Yakub, Jesus da Yesus, Joseph da Yusuf, W kuwa har yau a wasu yarukan da lafazin V suke ambatonta) kaɗai sunzo da maimaicin akalla sau 6,823 acikin Babil.

 Saboda haka, mabiya ɗarikar jehovah sun gamsu cewar Kalmar JHVH (YHWH) sunan Ubangiji ne daya kira kansa da kansa a littafi mai tsarki sama da sau dubu shidda, to amma kalmar ELOHIM (YHWH ELOHIM) ce ke tare da waɗancan haruffa a mafi yawan lokuta.

   Idan muka kalli kalmar 'ELOHIM', zamuga kalmomi ne biyu a haɗe, watau ELOH da kuma IM.

  Da Fari, ita IM, ɗango ne na girmamawa ga ELOH a yaren Annabi Ibrahim A.S. misali, idan za'ace Ibrahim yana da girma, sai a kara masa IM, ya zamo 'Ibrahimim', kamar yadda idan aka lura har yanzu yaren yahudanci da wasu yaruka na bin wannan tsari.

   Saboda haka 'ELOH' shine sunan, wanda shima zamu gane ainihinsa idan muka kalli yadda Larabci ke kiran duk abinda Ibraniyanci ya kira da 'EL' da lafazin 'AL'.

  Don haka, kalmar 'Eloh' ta yaren Ibraniyanci na nufin 'Aloh' kenan a larabci.

  Kalmar da idan mukaci gaba da mai-mai-ta-ta a zukatanmu zamuga ta sauya daga Eloh, Eloh, Zuwa Aloh Aloh.. Zuwa Allah Allah..

 Wannan ke nuni da cewa kalmomin 'YHWH ELOHIM' da suka zo a Babil na Ibraniyanci ba komai suke nufi ba sai 'YA HUWA ALLAH' a larabci, kusan Aya kenan ta farko a Suratul Ahad, da Ubangiji yace "Qul Huwallah..." (watau kace shine Allah)

   To waɗannan kalmomin fa, sune sukazo a Babil sama da sau dubu shidda.. Abinda Allah ke faɗawa Manzonsa Annabi Isah A.S shine "ka sanar musu da cewa Ubangijinka Shine Allah.." Kuma abinda Yesu Kiristi yayi ta sanarwar kenan, amma har zuwa yanzu Ubangiji baisa 'yan uwanmu kiristoci sun gane cewar Allah ne sunan ubangiji abin bauta da gaskiya ba.

   Marigayi Sheik Ahmad Deedat Rahimahullah yana Cewa dangane da wannan batu "Idan da Malaman kiristoci zasu sanar da Mabiyansu wannan abu, tabbas da lokaci yayi wanda musulmai da kiristoci zasu haɗu wajen bautawa Ubangiji makaɗaici".

   Daɗi akan haka, shine kalmar nan ta ELLELUYA, wadda babu kiristan dabai santa ba.

  Har ma sukan ambace ta aduk sanda suka so godewa Ubangiji, kamar yadda Musulmai ke faɗin Allahu Akbar don tsarkake Ubangiji.

   Ya kuwa ishemu misali idan muka kalli kalmar Ibraniyanci ta ELLELU-YA muka musanya ta da zubin larabci izuwa ALLELU-YA.. (muka sauya EL da AL)

  Sai mu kalli waɗannan kalmomi:-

  ALLELU YA

  YA ALLELU 

  ALLAHU YA 

  YA ALLAHU

  Ku tambayi kanku, don girman Allah akwai banbanci ko babu?

  Sheikh Deedat, Zakir Naikh da sauran malumman musulunci duk sun tabbtar da cewa Ya Allahu shine asalin Kalmar Elleluya.

  Don haka, aduk sanda kaji malaman kiristoci na faɗin "Praise the Lord!" sukuma suna amsawa da "ElleluYa!!!" kasani cewa "Ya Allahu" kurum suke ambata a sauye.

  Allah da aka ambata a Linjila, shine aka sake ambata a Alqur'ani mai tsarki, amma k'alilan daga mutane ke fuskantar haka.

  Hakika, Tsarki ya tabbata ga Ubangiji mai tsarki da Buwaya. Allah kayi daɗin tsiranka ga Shugabanmu Annabi Muhammad (s.a.w) da sauran Annabawan Allah masu tsarki. Amin.

Tuesday, 14 December 2021

KWAZAZZABON YAR KWANDO

 LABARI NA GASKIYA DANGANE DA KWAZAZZABON 'YAR KWANDO



Labari na gaskiya dangane da Kwazazzabon 'Yar Kwando da kuma saukar Shehu Mujaddadi a K'asar Dugabau.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Hakika Labarin da ake fada dangane da kwazazzabon 'yar kwando gaskiya ne. Ita 'yar kwandon ai aljana ce, watakila tana cikin jinsin fararen aljannu don kuwa bamu samu labarin wani data taɓa cutarwa ba.

Amma dai mutanen Dugabau dake ƙasar Kabo ta jihar Kano sun bada shaidar cewa ana yawan haɗuwa da Aljanna 'yarkwando a daf da wannan kwazazzabon.

Akwai wanda yace min takan fito da sigar tsohuwa ko Budurwa, har ma zata iya neman wani taimako daga gareka, ko ka ganta tana wani uzuri nata, amma dai ba zata yarda kaga fuskar ta ba.

Ance ta taɓa fitowa wani mutum a siffar tsohuwa, sai tace masa ya taimaka ya tsallakar da ita ta haye ruwa, amma sai mutumin yaƙi. Juyawar da zaiyi sai hangota yayi kanta a cikin ruwa, ƙafufuwanta suna kaɗawa a sama, a haka ta tsallake ruwan.

Wani mutum kuma mai noman rani a daf da wannan kwazazzabo ya shaida min cewa suna yawan ganin abubuwan mamaki dangane da aljanna Ƴar kwando. Har yace min ba'a yi musu satar amfanin gona, domin kuwa ita aljanar ke musu gadi, sannan kuma yace gidan ta yana kusa da wani ƙaton rimi da aka sare acan kan tudu idan an haye ruwa, ragowar surkukin kuma na ɗauke ne da gidajen 'ya'yanta.

Shi dai wannan kwazazzabo da ake kira 'kwazazzabon 'yarkwando' a kusa da garin Dugabau din yake, waje ne mai girman gaske dake hayin ƙorama, yana da tarihi kuma, domin kuwa anan ne akace magoya bayan Shehu Usmanu Bn Fodio (Allah yajikan sa da rahama) suka taɓa sauka a sa'ar da ake buga yaƙin Jihadi a k'asar hausa (wajajen 1804).

Marubuci Ibrahim Bala Gwarzo ya ruwaito a littafinsa 'Mazan kwarai' cewa a wannan wuri mai suna kwazazzabon Yarkwando Shehu Usmanu ya sauka ya huta ya kuma ƙara ƙarfin rundunar sa. Daga nan ya afkawa masarautar Karaye da yaƙi, sannan ya afkawa birnin kano.

Tarihi ya tabbatar mana da cewa Shehu Usmanu Danfodio bai sauka a wannan yanki na Dugabau ba, amma magoya bayan sa Malamai da suka jagoranci yaƙi da Sarkin Kano na zamanin watau Alwali, anan suka yi hijira tare da haɗa gagarumar rumduna.  Zuwa yanzu dai akwai tsohon masallacin jumu'a da magoya bayan shehun suka buɗe wanda akace wani mutum mai suna Isyaka ne ya gina shi acikin garin na Dugabau. Sama da shekaru ɗari da tamanin da faruwar wannan lamari, wannan masallaci ne babba a yankin, saboda an gina shi ya ginu, an kuma ƙawata shi da ado dai-dai da wayewar maginan ƙasa na wancan zamani.

Na tambayi wani Tsoho akan ko zamu samu wata shaida takamaimiya wadda aja taskance kamar misalin Littafi Alkur'ani maigirma, takobi ko wani abu wanda ya fito daga magoya bayan shehu Usmanu mujaddadi a halin saukar su a wannan yanki ?.. Sai dai hakan bai samu ba, watakila saboda jimawar zamani ko kuma gushewar Dattijan da suka kiyaye ainihin abinda ya faru a wancan zamanin gwargwadon yadda suka samu labari, amma dai ya tabbatar min da ingancin wannan labari, ya kuma k'aramin da cewa akwai wata Katuwar kuka mai suna 'JARMA' (wadda a yanzu ta fadi da kanta) wadda ke daura da kwazazzabon 'yarkwando, itama ada can jarumai da sarakunan kasar Katsina na sauka a wurinta kafin su riski birnin Kano don kai harin yaƙi ko aiwatar da wata buƙata tasu.

Shikuwa kwazazzabon 'yarkwando, nan ne filin yaƙin da aka gwabza gagarumin faɗan nan da ake ambata da suna 'YAƘIN ƊAUKAR GIRMA', wanda gagarumar runduna ta taso daga kano da nufin murƙushe tsirarun mayaƙan da suka yi hijira zuwa wurin masu biyayya ga Shehu Usmanu Danfodio, amma cikin ikon Allah sai ƙaramar rundunar ta samu galaba gagarima akan waccan gagarumar runduna.

  Labari ya samu gare mu cewar wajen tun a baya dandali ne, watakila ƙoramar dake gudana adaf da kwazazzabon ke jan ra'ayin matafiya masu shigewa daga ƙasar katsina, sokoto da sauran wurare su yada zango a wajen. Tunda wani tsoho ya ƙara min da cewa ada, wajen maɗeba ce, watau ya taɓa zamowa dandali wanda masu sana'ar Su suka kakkafa rumfuna suke kuma tururuwar zuwa domin kamun kifi.

Zuwa yanzu dai, Bamu san alaƙar wannan aljana da rundunar Fulani masu jihadi ba, ko wadancan matafiya masu yada zango a wajen ba, ma'ana, tun a wancan zamanin an san da ita ko kuwa daga baya ne labarinta ya fito?, sannan idan akwai ta wanne taimako ko akasarin haka ta basu..? To amma dai ko a yanzu mun kara sanin ɗaya daga manyan hanyoyin da matafiya ke bi daga kano zuwa katsina ko Sokoto a zamanin da ya shuɗe. Don haka muna yiwa Allah godiya domin kuwa hakika ko a yanzu mun ƙara Sani..

# SadiqTukur Gwarzo

Saturday, 11 December 2021

TUNAWA DA YAKIN SANTOLO

 TUNAWA DA YAKIN SANTOLO

(YAKI DON TABBATAR DA MUSULUNCI A KASAR HAUSA)

9/12/2017

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

       08060869978

Hakika, idan har Tarihin kasar hausa ba zai cika ba har sai an kalli tarihin kano, to haka ma tarihin kano da zuwan musulunci ƙasar kano bazai taɓa kammaluwa ba har sai an sanya wani yanki daga yaƙin Santolo.

   Santolo tsohuwar daular hausawa ce, tsohuwar masarauta ce wadda salsalar ta take tukewa da salsalar asalin hausawa.

   A cikin zantuka masu yawa na maruwaitan tarihin kano, an gamsu cewar wani mai suna 'Dala' shine wanda ya soma zama akan dutsen da ayau ake kira da suna 'Dala', a wajajen shekarar 700 miladiyya, tun a wancan lokacin kuma wasu na ganin akwai mutane dake rayuwa a kan wani dutse mai suna 'santolo', wanda shi ma da alama, sunan ya samo asali ne daga mutumin da ya soma rayuwa a saman dutsen.

   Zuwa yanzu, babu takamaimen tarihin asalin kafuwar Santolo, sannan kuma yana da wuya a iya lissafa tsawon zamanin da mutane suka soma rayuwa akan dutsen santolo, to amma tarihi ya auna cewar mazauna Santolo da na Dala dake kano suna da alaƙa da juna. Alaƙar kuwa na iya zamowa ta jinsi, ko ta addini ko kuma ta duka gaba ɗaya, tunda har ma an samu cewa acan baya alakar kasuwanci na shiga tsakanin mazauna waɗannan duwatsu biyu. Wasu kuma na ganin Santolo tayi shaharar da har daga Borno ake zuwa yin fatauci a koma, to amma daga baya sai Allah ya fifita yankin Dala sama da ita Santolon.

    Babban abin tunawa dangane da Santolo shine 'Yakin Santolo' wanda aka gwabza tsakanin Sarkin Kano Ali Yaji ɗan Tsamiya da kuma shugaban Santolo mai laƙabin 'Magajin Santolo' wanda ya karɓi bakuncin takwaransa 'Magajin Dala' bayan sarkin Kano ma goma sha ɗaya Ali Yaji ɗan Tsamiya ya karya tsumburbura da ke saman dutsen Dala, sannan ya kori Magajin Dala da mutanen sa.

    Tarihi ya nuna cewa asalin garin Kano ya faro ne daga dutsen dala, inda ake bautar gunkin wata aljanna mai suna 'tsumburbura' dake saman dutsen, amma daga baya maɗatai ta kafu, har Bagauda yazo ya soma sarautar ɗaukacin yankunan maɗatai da na yankin Dala, waɗanda suka haɗe da sunan kano.

   Haka kuma, tsawon zamani a kano babu addinin musulunci, daga masu bautar tsunburbura karkashin ikon magajin dala (wanda yayi gadon Barbushe) sai kuma maguzawa waɗanda basa bautar komai irin su Bagauda da salsalarsa da ke sarautar kano. 

  A haka kano ta taho har aka zo kan mulkin Sarki Ali yaji ɗan Tsamiya a wuraren shekara ta 1349-1385 miladiyya, wanda ya karɓi bakuncin kabilar fulani Wangarawa daga Kasar Mali, waɗanda suka kawo musulunci zuwa garin kamar yadda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya faɗa a littafinsa da yayi magana akan tarihin kano da tarihin zuwan wangarawa birnin.

   To, bayan sarki Ali Yaji ya karɓi addinin musulunci, sai kuma ya jagoranci karya gunkin tsunburbura tare da umartar masu bauta masa su dawo musulunci, amma sai wasun su suka ce sam-sam ba zasu bar addinin kaka-da-kakan-nin su ba suyi addinin dungure, don haka sai suka gudu izuwa Santolo domin cigaba da bautar da suka saba.

Ga abinda yazo a littafin Kano Chronicle game da wannan yaƙi:-

Sarki ya umurci dukkan garururuwan Kanawa su yi salla, sai suka yi. Ya gina masallaci mai-kusurwa hudu a karkashin itaciyar da muka ambata a baya, suna salla a cikinsa wakati biyar, suna komawa gidajansu. shi ko, Sarkin Gazarzawa ya kan zo da jama'arsa, suna yin najasa suna shafe dukan masallaci da ita. Saboda wannan aka sa Dan-buje ya rika gewaya masallaci da dukan makamai iri iri tun daga lisha har hudowar alfijr, yana kururuwa.   

  Kai duk da haka suka yaudare shi da mutanensa, wadansu suka bi maganar arna, shi da sauran jama'a suka ki. Ba su daina najasa cikin masallaci ba, har Sheshe da Famore suka ce, "Babu maganin wadannan kafirai sai rokon Allah." Sauran suka ce, "Hakanan ne." Sa'an nan suka taru cikin masallaci daran Talata, tun daga magariba har hudowar rana suna addu'a a kan kafiran. Sa'an nan suka fito suka koma gidajansu suna masu rauni.

 A cikin wannan rana Allah ya karbi rokonsu,

ya makantad da idanun babbansu, da kuma dukan wanda yake yin wannan aiki ya makance, duk da matansu. Daga nan sai sauran kafirai sukaji tsoro. 

Sa'an nan Yaji ya tuɓe babbansu daga sarautarsa, ya ce masa, "Kai ne Sarkin Makafi."

An ce a cikin zamanin Yaji ne Sarkin Dabi da Sarkin Daf da Sarkin Gano suka zo da dawaki cikin wannan gari, amma wannan zance ba shi da karfi.


Bayan haka sai Sarkin Kano Yaji ya ce da Wangarawa,"Ina so ku taimake ni da addu'a domin in rinjayi Santolo, idan na rinjaye ta

dukan garuruwa za su bi ni, domin ita ce ƙusar Kasashen Kudu. Suka ce, "To, ma taimake ka da addu'a amma ba za mu yi addu'ar ba sai a

bakin ramin ganuwarta. Sa'an nan Sarki ya fita tare da Wangarawa zuwa Santolo, mayakan da ke tare da shi mutum ɗari da goma sha

ɗaya, hamsin na fuskar Wangarawa, sittin na fuskar Sarki. 

Na farko daga cikin jarumawansa: Jarmai Gobara-daga-sama, da Jakada Kwalo, da Ragamar-giwa, da Makama Butaci, da Madawaki Kuamna, da Barde Shege, da Sarkin Zaura Gamaji, da Dan-buram Gantaroro, da Ɗan-makoyo Dagazau, da Galadima Tuntu, da Sarkin Sirdi Maguri, da Gauji, da Garuji da Tankarau, da Kargage, da Karfashi, da Kutunku, da Toro da Kamfashe, da Gwauron-giwa shine

Galadima, da Zaki, da Bambauri, da wadansu na Cikwan sittin.

Yayin da Suka kai Santolo, sarKI ya zauna a Duji (Sunan mutum ne.) Da duhun dare ya tashi ya tafi tare da Wangarawa zuwa Santolo, suna kewaye ta suna yi mata addua har hudowar alfijir, sa'an nan suka komo sansani. Sa ad da rana ta hudo suka taso zuwa gare ta da niyyar yaki Mutanen Santolo suka fita suka tare su a sarari, suka soma yaƙi tun daga hudowar rana har faduwa ta ba wanda ya rinjayi wani.

Kanawa suka koma Duji, mutanen Santolo suka koma gida. Sarkin Kano kuwa ya yi bakin ciki. Famore ya ce, "kada ka yi bakin ciki, ma rinjaye Su in Allah ya so." Sarkin Kano ya yi farin ciki saboda wannan magana. Daga nan Ƙosa bawan Sarkl, yace "Ya Ubangijina, ni na san asirinta. Akwai waɗansu mutum takwas

cikinta, in ba a kashe su ba ba wanda zai iya shiga ramin ganuwarta".

Famore ya ce, Ka san sunan mutanen nan?"  Ƙosa Ya ce, "I na san sunan su". Sai Famore yace, "Kaka sunayansu?" sai ya ce, "Sunan babbansu Hambari, da kuma Goshin-Ɓauna da Ka-fi-wuta, da Gugan-karfe, da Gandar-giwa, da Hamburkin-toka da Zangada-kere, da Gumbar wake" Goje yace, "Idan na ga Hambare na kashe shi in Allah ya so".

Sa'ad da alfijir ya hudo Sarkin Kano ya fita tare da rundunarsa, zuwa dutsen Santolo da mashi a hannunsa, yana mai daurariyyar fuska, GoJe yana gaban sa, Zaite yana damar sa, Famore yana hagun sa, Sheshe yana bayansa, sauran Wangarawa da Kanawa suna binsa.

Sa'ad da suka iso Santolo dukan kafirai suka fito. Da Goje ya ga Hambare sai ya zage dantsan sa ya zabura zuwa gareshi, dukan kafirai Suka zaburo wa Goje, sai ya yi musu tsawa suka watse. Sa ad da ya kai wurin Hambare ya soke shi da mashi, Hambare kuma ya ribce wuyansa ya fizgo shi daga kan doki, sai Goje ya fid da ƴar wuka ya soke shi da ita a ciki, ya mutu. Daga nan ya hau dokinsa

ya shiga cikin ganuwar Santolo, Kanawa suka bi shi suka ci birnin dukansa. Sarki ya yi umurni a yanka dukan wanda aka samu a cikinta, Sai mata da kananan yara. Goje kuma ya shiga cikin gunkinsu tare da Kosa da Gurgu, suka sami kuge da ƙaho biyu da barandami da mari.

Goje ya dauki kugen da kahon nan biyu, Kosa ya dauki barandamı da mari, Gurgu ya dauki mari.

 Yaji ya zauna a cikinta kwana bakwal, ya rushe ta sarai, ta zama babu gini ko itace. Bayan wannan ya komo garinsa, ya ce da Goje, "Fadi dukan abin da kake so, na ba ka. Goje yace "ba ni son kome sai ka naɗa mini sarautar Madawakin Kano".

Sarkin Kano ya ce. "Kai ne Madawakin Kano. Ya tube Madawaki Gasatoro, ya fita ya gina gida a gawo; saboda haka aka Kira shi da suna Madawakin Gawo, domin a rarrabe tsakaninsu.

   Dutsen Santolo gagarumi ne, faffaɗa da doro, tsayinsa ya tafi kamar hawan bene daga baya, daga gabansa kuwa goshi yayi mai faɗi da santsi, tsakiyarsa yana da faɗi harma akwai koguna da akace dabbobin daji misalin su kyarkeci, dila da macizai na rayuwa a ciki.

  Ko da yake, bamu ji sunan gunki da aljanar da aka ce akwai a saman dutsen santolo ba, amma har yanzu mutanen dake zagaye da wurin sun kiyaye cewar kakanninsu sun basu labarin cewar a zamanin da, ana taruwa ahau kan wannan dutse don neman wata biyan bukata. 

   Sannan kuma akwai wata rijiya zuzzurfa dake saman dutsen mai suna 'Rijiyar Giɗaɗo', wadda akan hana mutane zuwa kusa da ita saboda kuɓuta daga k'wank'waman dake wurin masu halaka mutane.

   Zuwa yanzu garin santolo ya kasu biyu, akwai sabon garin santolo wanda kanawa (kabilar hausawa) ke ciki, sai kuma santolon fulani, amma dukkan su suna karkashin ikon dagaci mai suna Santolo Da'u. 

    Haka kuma dutsen yana nan a tsakiyar kauyukan sabon garin santolo, santolon fulani, Madawa, Koɗe, kyarmawa, da Tsakuwa waɗanda dukkanin su suke cikin gundumar Dawakin Kudu ta Jihar Kano.





Sunday, 5 December 2021

Tunawa da Yaƙin Basasar Kano

 TARIHI: TUNAWA DA YAK'IN BASASAR KANO


DAGA SADIQ TUKUR GWARZO


4/Dec/2016


"Galadima Yusufu mutane ke so ba Alu ba. A garin Garko yake kuma acan ya mutu. Kafin rasuwar sa, kowa yayi amannar cewa shine zai zamo Sarki, amma sai ciwo ya kamashi har ya mutu a Garko.

   Daga nan sai sarakunan bayin Sarki da 'ya'yansu sukace yanzu menene abinyi? Sai wasu sukace abu d'aya ya kamata muyi, mutum d'aya ne kurum zai iya jagorantar mu zuwa Kano. Shine Mallam Babba, Alu kenan. Daga nan suka aika masa, sannan suka ɗora shi a gadon Mulkin Yusufu.

   Bayan sunyi haka, da dare suka binne Yusufu da hasken fitilu. Suka kawo Alu suka zaunar dashi akan karagar mulki. Suka yi masa nad'i. Sai kuma suka ce da sauran fadawa kowa yazo yayi mubaya'a. Kaji yadda Alu ya zamo Sarki. Kuma shine dalilin da yasa da yaji turawa na tafe ya tafi sokoto domin ziyartar hubbalen Shehu ta yadda Sarkin Musulmi zai amince da zamowar sa Sarki tare da goya masa baya.

   Jama'ar gari, mafarauta da maharba ne suka yi bore ga Sarki Alu a lokacin da yakin Basasa ya ɓarke.

   Basasa anan na nufin yaƙin da akayi don ɗora Alu akan karagar mulki. Anyi shine a Ramli shekarar 'Ba-Sa-Sha'. 'Sha' a ilimin Hisabi na nufin 1000, 'Sa' na nufin 300, 'a' na nufin 1, yayin da 'ba' ke nufin 2. Idan ka hada lissafi zai baka shekara ta 1303 kenan bayan Hijira. (Dai-dai da 1894 miladiyya).

   Ana kiran Alu da suna 'Mallam Babba' (Ma'ana babban malami), domin a wurin mu duk wani dan Sarki Mallam ne koda bai koyi karatu ba. Amma da zarar Sarki ya bashi wata sarauta sai a daina cewa Mallam, a koma kiran sa da wannan sarauta.

    Alu ya shiga Kano ranar wata Laraba. A wannan lokacin mutane da yawa sun bar Kano izuwa Kamri wajen Tukur, domin shi akafi so.

   An kashe Tukur ne a Gurum (Kamri da Gurum wasu kauyuka ne dake kusa da juna a kasar katsina). Naji labarin cewa anji masa raunika sannan aka kawo shi gaban Sarki Alu. Ance Sarki Alu yayi fushi sosai har yake cewa don me zasu yiwa ɗan uwansa na jini haka? Sarki Alu yace "kuyi maza ku kawo masa ruwa yasha". Amma sai Sarki Tukur yace "kada a kawo min ruwa, azumi nake yi, bazan sha ruwa ba". A haka kuwa Allah ya amshi ransa. Allahu Akbar!!!

   A garin Gurum aka binne Sarki Tukur, shi yasa ake Kiran sa da 'Maje-Gurum' kamar yadda ake kiran Galadima Yusufu 'Maje-Garko', ake kiran Sarki Abbas kuma 'Maje Nasarawa'".

   Marigayi Alhaji Mahmud Koki tafinta ne na turawa, ya kasance yana cikin birnin kano a lokacin da yaƙin Basasa ya tashi, shine kuma ya bamu wannan labari na sama. An rubuta labarin a cikin tarihin sa wanda aka wallafa a shekarar 1977.

    ASALIN YAKIN BASASA

Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi shine ɗa na biyu ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya rasu a wajajen shekara ta 1882 miladiyya a wani gari mai suna Karofi a ƙasar katsina akan hanyar sa ta zuwa Ƙauran-Namoda. Sai Ƙaninsa Muhammad Bello (shima dan Marigayi Ibrahim Dabo ne) ya hau karagar mulki. 

   Ance Sarki Muhammad Bello ya rinka kokarin karɓe muƙamai daga hannun 'ya'yan 'yanuwansa yana dasa 'ya'yansa na cikin sa. Sannan ya ƙara yawan jakadu masu tattara Haraji, abinda yayi sanadiyyar jefa talakawa cikin matsi kenan, tare da janyo masa bakin jini a gurinsu. Ance tun a lokacin ya fara sharewa dansa Muhammad Tukur hanyar zama Sarki bayan ya rasu. Ya rinka aikawa da Kyaututtuka izuwa Sokoto domin neman goyon bayan Sarkin Musulmi.

   Shi kuwa Sarkin Kano Muhammad Tukur, sarkin musulmi Abdurrahman (Ɗanyen kasko) ne ya naɗa shi bayan mutuwar mahaifin Tukur din, watau Sarkin Kano Muhammad Bello. Wasu sunce bai kai shekaru arba'in ba aka naɗa shi mulki, Wasu kuma sunce bashi da karsashin Riƙe mulki.

   A wannan lokacin, sai dan uwansa Galadima Yusuf, wanda yake ɗa ga marigayi Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi tare da jama'ar sa suka gudu izuwa garin Takai wadda ke kudu maso gabashin Kano. 

   Mutuwar Galadima Yusuf a garin Garko a jan hanyar su ta zuwa Kano tare da ƙwace sarauta itace sanadin ɗora Sarkin kano Alu a mazaunin sa. Sannan a hankali suka rinka cinye garuruwan gabashin kano da yaki suna ƙarfafa rundunar su. A haka har sai da rundunar su tayi karfi, suka shigo kano a ranar wata Laraba, 19 ga watan agusta na shekarar 1894 miladiyya, ana buga tambura na sarauta bayan ya samu nasara akan Sarki Tukur, wanda ya gudu ya bar Kano don gudun zubar jinin mutanen kano idan har za a buga yaƙi alhali yana cikin birnin kano.

  Sarki Alu ya cigaba da sarautar kano har lokacin da turawa suka karɓe iko da ita tare da danƙa sarauta ga ɗanuwansa Sarki Abbas.

  Dafatan Allah ya jikansu duka amin, kuma da fatan zamu amfanu da darussan wannan labari.