TARIHI: TUNAWA DA YAK'IN BASASAR KANO
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
4/Dec/2016
"Galadima Yusufu mutane ke so ba Alu ba. A garin Garko yake kuma acan ya mutu. Kafin rasuwar sa, kowa yayi amannar cewa shine zai zamo Sarki, amma sai ciwo ya kamashi har ya mutu a Garko.
Daga nan sai sarakunan bayin Sarki da 'ya'yansu sukace yanzu menene abinyi? Sai wasu sukace abu d'aya ya kamata muyi, mutum d'aya ne kurum zai iya jagorantar mu zuwa Kano. Shine Mallam Babba, Alu kenan. Daga nan suka aika masa, sannan suka ɗora shi a gadon Mulkin Yusufu.
Bayan sunyi haka, da dare suka binne Yusufu da hasken fitilu. Suka kawo Alu suka zaunar dashi akan karagar mulki. Suka yi masa nad'i. Sai kuma suka ce da sauran fadawa kowa yazo yayi mubaya'a. Kaji yadda Alu ya zamo Sarki. Kuma shine dalilin da yasa da yaji turawa na tafe ya tafi sokoto domin ziyartar hubbalen Shehu ta yadda Sarkin Musulmi zai amince da zamowar sa Sarki tare da goya masa baya.
Jama'ar gari, mafarauta da maharba ne suka yi bore ga Sarki Alu a lokacin da yakin Basasa ya ɓarke.
Basasa anan na nufin yaƙin da akayi don ɗora Alu akan karagar mulki. Anyi shine a Ramli shekarar 'Ba-Sa-Sha'. 'Sha' a ilimin Hisabi na nufin 1000, 'Sa' na nufin 300, 'a' na nufin 1, yayin da 'ba' ke nufin 2. Idan ka hada lissafi zai baka shekara ta 1303 kenan bayan Hijira. (Dai-dai da 1894 miladiyya).
Ana kiran Alu da suna 'Mallam Babba' (Ma'ana babban malami), domin a wurin mu duk wani dan Sarki Mallam ne koda bai koyi karatu ba. Amma da zarar Sarki ya bashi wata sarauta sai a daina cewa Mallam, a koma kiran sa da wannan sarauta.
Alu ya shiga Kano ranar wata Laraba. A wannan lokacin mutane da yawa sun bar Kano izuwa Kamri wajen Tukur, domin shi akafi so.
An kashe Tukur ne a Gurum (Kamri da Gurum wasu kauyuka ne dake kusa da juna a kasar katsina). Naji labarin cewa anji masa raunika sannan aka kawo shi gaban Sarki Alu. Ance Sarki Alu yayi fushi sosai har yake cewa don me zasu yiwa ɗan uwansa na jini haka? Sarki Alu yace "kuyi maza ku kawo masa ruwa yasha". Amma sai Sarki Tukur yace "kada a kawo min ruwa, azumi nake yi, bazan sha ruwa ba". A haka kuwa Allah ya amshi ransa. Allahu Akbar!!!
A garin Gurum aka binne Sarki Tukur, shi yasa ake Kiran sa da 'Maje-Gurum' kamar yadda ake kiran Galadima Yusufu 'Maje-Garko', ake kiran Sarki Abbas kuma 'Maje Nasarawa'".
Marigayi Alhaji Mahmud Koki tafinta ne na turawa, ya kasance yana cikin birnin kano a lokacin da yaƙin Basasa ya tashi, shine kuma ya bamu wannan labari na sama. An rubuta labarin a cikin tarihin sa wanda aka wallafa a shekarar 1977.
ASALIN YAKIN BASASA
Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi shine ɗa na biyu ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya rasu a wajajen shekara ta 1882 miladiyya a wani gari mai suna Karofi a ƙasar katsina akan hanyar sa ta zuwa Ƙauran-Namoda. Sai Ƙaninsa Muhammad Bello (shima dan Marigayi Ibrahim Dabo ne) ya hau karagar mulki.
Ance Sarki Muhammad Bello ya rinka kokarin karɓe muƙamai daga hannun 'ya'yan 'yanuwansa yana dasa 'ya'yansa na cikin sa. Sannan ya ƙara yawan jakadu masu tattara Haraji, abinda yayi sanadiyyar jefa talakawa cikin matsi kenan, tare da janyo masa bakin jini a gurinsu. Ance tun a lokacin ya fara sharewa dansa Muhammad Tukur hanyar zama Sarki bayan ya rasu. Ya rinka aikawa da Kyaututtuka izuwa Sokoto domin neman goyon bayan Sarkin Musulmi.
Shi kuwa Sarkin Kano Muhammad Tukur, sarkin musulmi Abdurrahman (Ɗanyen kasko) ne ya naɗa shi bayan mutuwar mahaifin Tukur din, watau Sarkin Kano Muhammad Bello. Wasu sunce bai kai shekaru arba'in ba aka naɗa shi mulki, Wasu kuma sunce bashi da karsashin Riƙe mulki.
A wannan lokacin, sai dan uwansa Galadima Yusuf, wanda yake ɗa ga marigayi Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi tare da jama'ar sa suka gudu izuwa garin Takai wadda ke kudu maso gabashin Kano.
Mutuwar Galadima Yusuf a garin Garko a jan hanyar su ta zuwa Kano tare da ƙwace sarauta itace sanadin ɗora Sarkin kano Alu a mazaunin sa. Sannan a hankali suka rinka cinye garuruwan gabashin kano da yaki suna ƙarfafa rundunar su. A haka har sai da rundunar su tayi karfi, suka shigo kano a ranar wata Laraba, 19 ga watan agusta na shekarar 1894 miladiyya, ana buga tambura na sarauta bayan ya samu nasara akan Sarki Tukur, wanda ya gudu ya bar Kano don gudun zubar jinin mutanen kano idan har za a buga yaƙi alhali yana cikin birnin kano.
Sarki Alu ya cigaba da sarautar kano har lokacin da turawa suka karɓe iko da ita tare da danƙa sarauta ga ɗanuwansa Sarki Abbas.
Dafatan Allah ya jikansu duka amin, kuma da fatan zamu amfanu da darussan wannan labari.
No comments:
Post a Comment