Tuesday, 14 December 2021

KWAZAZZABON YAR KWANDO

 LABARI NA GASKIYA DANGANE DA KWAZAZZABON 'YAR KWANDO



Labari na gaskiya dangane da Kwazazzabon 'Yar Kwando da kuma saukar Shehu Mujaddadi a K'asar Dugabau.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Hakika Labarin da ake fada dangane da kwazazzabon 'yar kwando gaskiya ne. Ita 'yar kwandon ai aljana ce, watakila tana cikin jinsin fararen aljannu don kuwa bamu samu labarin wani data taɓa cutarwa ba.

Amma dai mutanen Dugabau dake ƙasar Kabo ta jihar Kano sun bada shaidar cewa ana yawan haɗuwa da Aljanna 'yarkwando a daf da wannan kwazazzabon.

Akwai wanda yace min takan fito da sigar tsohuwa ko Budurwa, har ma zata iya neman wani taimako daga gareka, ko ka ganta tana wani uzuri nata, amma dai ba zata yarda kaga fuskar ta ba.

Ance ta taɓa fitowa wani mutum a siffar tsohuwa, sai tace masa ya taimaka ya tsallakar da ita ta haye ruwa, amma sai mutumin yaƙi. Juyawar da zaiyi sai hangota yayi kanta a cikin ruwa, ƙafufuwanta suna kaɗawa a sama, a haka ta tsallake ruwan.

Wani mutum kuma mai noman rani a daf da wannan kwazazzabo ya shaida min cewa suna yawan ganin abubuwan mamaki dangane da aljanna Ƴar kwando. Har yace min ba'a yi musu satar amfanin gona, domin kuwa ita aljanar ke musu gadi, sannan kuma yace gidan ta yana kusa da wani ƙaton rimi da aka sare acan kan tudu idan an haye ruwa, ragowar surkukin kuma na ɗauke ne da gidajen 'ya'yanta.

Shi dai wannan kwazazzabo da ake kira 'kwazazzabon 'yarkwando' a kusa da garin Dugabau din yake, waje ne mai girman gaske dake hayin ƙorama, yana da tarihi kuma, domin kuwa anan ne akace magoya bayan Shehu Usmanu Bn Fodio (Allah yajikan sa da rahama) suka taɓa sauka a sa'ar da ake buga yaƙin Jihadi a k'asar hausa (wajajen 1804).

Marubuci Ibrahim Bala Gwarzo ya ruwaito a littafinsa 'Mazan kwarai' cewa a wannan wuri mai suna kwazazzabon Yarkwando Shehu Usmanu ya sauka ya huta ya kuma ƙara ƙarfin rundunar sa. Daga nan ya afkawa masarautar Karaye da yaƙi, sannan ya afkawa birnin kano.

Tarihi ya tabbatar mana da cewa Shehu Usmanu Danfodio bai sauka a wannan yanki na Dugabau ba, amma magoya bayan sa Malamai da suka jagoranci yaƙi da Sarkin Kano na zamanin watau Alwali, anan suka yi hijira tare da haɗa gagarumar rumduna.  Zuwa yanzu dai akwai tsohon masallacin jumu'a da magoya bayan shehun suka buɗe wanda akace wani mutum mai suna Isyaka ne ya gina shi acikin garin na Dugabau. Sama da shekaru ɗari da tamanin da faruwar wannan lamari, wannan masallaci ne babba a yankin, saboda an gina shi ya ginu, an kuma ƙawata shi da ado dai-dai da wayewar maginan ƙasa na wancan zamani.

Na tambayi wani Tsoho akan ko zamu samu wata shaida takamaimiya wadda aja taskance kamar misalin Littafi Alkur'ani maigirma, takobi ko wani abu wanda ya fito daga magoya bayan shehu Usmanu mujaddadi a halin saukar su a wannan yanki ?.. Sai dai hakan bai samu ba, watakila saboda jimawar zamani ko kuma gushewar Dattijan da suka kiyaye ainihin abinda ya faru a wancan zamanin gwargwadon yadda suka samu labari, amma dai ya tabbatar min da ingancin wannan labari, ya kuma k'aramin da cewa akwai wata Katuwar kuka mai suna 'JARMA' (wadda a yanzu ta fadi da kanta) wadda ke daura da kwazazzabon 'yarkwando, itama ada can jarumai da sarakunan kasar Katsina na sauka a wurinta kafin su riski birnin Kano don kai harin yaƙi ko aiwatar da wata buƙata tasu.

Shikuwa kwazazzabon 'yarkwando, nan ne filin yaƙin da aka gwabza gagarumin faɗan nan da ake ambata da suna 'YAƘIN ƊAUKAR GIRMA', wanda gagarumar runduna ta taso daga kano da nufin murƙushe tsirarun mayaƙan da suka yi hijira zuwa wurin masu biyayya ga Shehu Usmanu Danfodio, amma cikin ikon Allah sai ƙaramar rundunar ta samu galaba gagarima akan waccan gagarumar runduna.

  Labari ya samu gare mu cewar wajen tun a baya dandali ne, watakila ƙoramar dake gudana adaf da kwazazzabon ke jan ra'ayin matafiya masu shigewa daga ƙasar katsina, sokoto da sauran wurare su yada zango a wajen. Tunda wani tsoho ya ƙara min da cewa ada, wajen maɗeba ce, watau ya taɓa zamowa dandali wanda masu sana'ar Su suka kakkafa rumfuna suke kuma tururuwar zuwa domin kamun kifi.

Zuwa yanzu dai, Bamu san alaƙar wannan aljana da rundunar Fulani masu jihadi ba, ko wadancan matafiya masu yada zango a wajen ba, ma'ana, tun a wancan zamanin an san da ita ko kuwa daga baya ne labarinta ya fito?, sannan idan akwai ta wanne taimako ko akasarin haka ta basu..? To amma dai ko a yanzu mun kara sanin ɗaya daga manyan hanyoyin da matafiya ke bi daga kano zuwa katsina ko Sokoto a zamanin da ya shuɗe. Don haka muna yiwa Allah godiya domin kuwa hakika ko a yanzu mun ƙara Sani..

# SadiqTukur Gwarzo

No comments:

Post a Comment