TUNAWA DA YAKIN SANTOLO
(YAKI DON TABBATAR DA MUSULUNCI A KASAR HAUSA)
9/12/2017
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978
Hakika, idan har Tarihin kasar hausa ba zai cika ba har sai an kalli tarihin kano, to haka ma tarihin kano da zuwan musulunci ƙasar kano bazai taɓa kammaluwa ba har sai an sanya wani yanki daga yaƙin Santolo.
Santolo tsohuwar daular hausawa ce, tsohuwar masarauta ce wadda salsalar ta take tukewa da salsalar asalin hausawa.
A cikin zantuka masu yawa na maruwaitan tarihin kano, an gamsu cewar wani mai suna 'Dala' shine wanda ya soma zama akan dutsen da ayau ake kira da suna 'Dala', a wajajen shekarar 700 miladiyya, tun a wancan lokacin kuma wasu na ganin akwai mutane dake rayuwa a kan wani dutse mai suna 'santolo', wanda shi ma da alama, sunan ya samo asali ne daga mutumin da ya soma rayuwa a saman dutsen.
Zuwa yanzu, babu takamaimen tarihin asalin kafuwar Santolo, sannan kuma yana da wuya a iya lissafa tsawon zamanin da mutane suka soma rayuwa akan dutsen santolo, to amma tarihi ya auna cewar mazauna Santolo da na Dala dake kano suna da alaƙa da juna. Alaƙar kuwa na iya zamowa ta jinsi, ko ta addini ko kuma ta duka gaba ɗaya, tunda har ma an samu cewa acan baya alakar kasuwanci na shiga tsakanin mazauna waɗannan duwatsu biyu. Wasu kuma na ganin Santolo tayi shaharar da har daga Borno ake zuwa yin fatauci a koma, to amma daga baya sai Allah ya fifita yankin Dala sama da ita Santolon.
Babban abin tunawa dangane da Santolo shine 'Yakin Santolo' wanda aka gwabza tsakanin Sarkin Kano Ali Yaji ɗan Tsamiya da kuma shugaban Santolo mai laƙabin 'Magajin Santolo' wanda ya karɓi bakuncin takwaransa 'Magajin Dala' bayan sarkin Kano ma goma sha ɗaya Ali Yaji ɗan Tsamiya ya karya tsumburbura da ke saman dutsen Dala, sannan ya kori Magajin Dala da mutanen sa.
Tarihi ya nuna cewa asalin garin Kano ya faro ne daga dutsen dala, inda ake bautar gunkin wata aljanna mai suna 'tsumburbura' dake saman dutsen, amma daga baya maɗatai ta kafu, har Bagauda yazo ya soma sarautar ɗaukacin yankunan maɗatai da na yankin Dala, waɗanda suka haɗe da sunan kano.
Haka kuma, tsawon zamani a kano babu addinin musulunci, daga masu bautar tsunburbura karkashin ikon magajin dala (wanda yayi gadon Barbushe) sai kuma maguzawa waɗanda basa bautar komai irin su Bagauda da salsalarsa da ke sarautar kano.
A haka kano ta taho har aka zo kan mulkin Sarki Ali yaji ɗan Tsamiya a wuraren shekara ta 1349-1385 miladiyya, wanda ya karɓi bakuncin kabilar fulani Wangarawa daga Kasar Mali, waɗanda suka kawo musulunci zuwa garin kamar yadda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya faɗa a littafinsa da yayi magana akan tarihin kano da tarihin zuwan wangarawa birnin.
To, bayan sarki Ali Yaji ya karɓi addinin musulunci, sai kuma ya jagoranci karya gunkin tsunburbura tare da umartar masu bauta masa su dawo musulunci, amma sai wasun su suka ce sam-sam ba zasu bar addinin kaka-da-kakan-nin su ba suyi addinin dungure, don haka sai suka gudu izuwa Santolo domin cigaba da bautar da suka saba.
Ga abinda yazo a littafin Kano Chronicle game da wannan yaƙi:-
Sarki ya umurci dukkan garururuwan Kanawa su yi salla, sai suka yi. Ya gina masallaci mai-kusurwa hudu a karkashin itaciyar da muka ambata a baya, suna salla a cikinsa wakati biyar, suna komawa gidajansu. shi ko, Sarkin Gazarzawa ya kan zo da jama'arsa, suna yin najasa suna shafe dukan masallaci da ita. Saboda wannan aka sa Dan-buje ya rika gewaya masallaci da dukan makamai iri iri tun daga lisha har hudowar alfijr, yana kururuwa.
Kai duk da haka suka yaudare shi da mutanensa, wadansu suka bi maganar arna, shi da sauran jama'a suka ki. Ba su daina najasa cikin masallaci ba, har Sheshe da Famore suka ce, "Babu maganin wadannan kafirai sai rokon Allah." Sauran suka ce, "Hakanan ne." Sa'an nan suka taru cikin masallaci daran Talata, tun daga magariba har hudowar rana suna addu'a a kan kafiran. Sa'an nan suka fito suka koma gidajansu suna masu rauni.
A cikin wannan rana Allah ya karbi rokonsu,
ya makantad da idanun babbansu, da kuma dukan wanda yake yin wannan aiki ya makance, duk da matansu. Daga nan sai sauran kafirai sukaji tsoro.
Sa'an nan Yaji ya tuɓe babbansu daga sarautarsa, ya ce masa, "Kai ne Sarkin Makafi."
An ce a cikin zamanin Yaji ne Sarkin Dabi da Sarkin Daf da Sarkin Gano suka zo da dawaki cikin wannan gari, amma wannan zance ba shi da karfi.
Bayan haka sai Sarkin Kano Yaji ya ce da Wangarawa,"Ina so ku taimake ni da addu'a domin in rinjayi Santolo, idan na rinjaye ta
dukan garuruwa za su bi ni, domin ita ce ƙusar Kasashen Kudu. Suka ce, "To, ma taimake ka da addu'a amma ba za mu yi addu'ar ba sai a
bakin ramin ganuwarta. Sa'an nan Sarki ya fita tare da Wangarawa zuwa Santolo, mayakan da ke tare da shi mutum ɗari da goma sha
ɗaya, hamsin na fuskar Wangarawa, sittin na fuskar Sarki.
Na farko daga cikin jarumawansa: Jarmai Gobara-daga-sama, da Jakada Kwalo, da Ragamar-giwa, da Makama Butaci, da Madawaki Kuamna, da Barde Shege, da Sarkin Zaura Gamaji, da Dan-buram Gantaroro, da Ɗan-makoyo Dagazau, da Galadima Tuntu, da Sarkin Sirdi Maguri, da Gauji, da Garuji da Tankarau, da Kargage, da Karfashi, da Kutunku, da Toro da Kamfashe, da Gwauron-giwa shine
Galadima, da Zaki, da Bambauri, da wadansu na Cikwan sittin.
Yayin da Suka kai Santolo, sarKI ya zauna a Duji (Sunan mutum ne.) Da duhun dare ya tashi ya tafi tare da Wangarawa zuwa Santolo, suna kewaye ta suna yi mata addua har hudowar alfijir, sa'an nan suka komo sansani. Sa ad da rana ta hudo suka taso zuwa gare ta da niyyar yaki Mutanen Santolo suka fita suka tare su a sarari, suka soma yaƙi tun daga hudowar rana har faduwa ta ba wanda ya rinjayi wani.
Kanawa suka koma Duji, mutanen Santolo suka koma gida. Sarkin Kano kuwa ya yi bakin ciki. Famore ya ce, "kada ka yi bakin ciki, ma rinjaye Su in Allah ya so." Sarkin Kano ya yi farin ciki saboda wannan magana. Daga nan Ƙosa bawan Sarkl, yace "Ya Ubangijina, ni na san asirinta. Akwai waɗansu mutum takwas
cikinta, in ba a kashe su ba ba wanda zai iya shiga ramin ganuwarta".
Famore ya ce, Ka san sunan mutanen nan?" Ƙosa Ya ce, "I na san sunan su". Sai Famore yace, "Kaka sunayansu?" sai ya ce, "Sunan babbansu Hambari, da kuma Goshin-Ɓauna da Ka-fi-wuta, da Gugan-karfe, da Gandar-giwa, da Hamburkin-toka da Zangada-kere, da Gumbar wake" Goje yace, "Idan na ga Hambare na kashe shi in Allah ya so".
Sa'ad da alfijir ya hudo Sarkin Kano ya fita tare da rundunarsa, zuwa dutsen Santolo da mashi a hannunsa, yana mai daurariyyar fuska, GoJe yana gaban sa, Zaite yana damar sa, Famore yana hagun sa, Sheshe yana bayansa, sauran Wangarawa da Kanawa suna binsa.
Sa'ad da suka iso Santolo dukan kafirai suka fito. Da Goje ya ga Hambare sai ya zage dantsan sa ya zabura zuwa gareshi, dukan kafirai Suka zaburo wa Goje, sai ya yi musu tsawa suka watse. Sa ad da ya kai wurin Hambare ya soke shi da mashi, Hambare kuma ya ribce wuyansa ya fizgo shi daga kan doki, sai Goje ya fid da ƴar wuka ya soke shi da ita a ciki, ya mutu. Daga nan ya hau dokinsa
ya shiga cikin ganuwar Santolo, Kanawa suka bi shi suka ci birnin dukansa. Sarki ya yi umurni a yanka dukan wanda aka samu a cikinta, Sai mata da kananan yara. Goje kuma ya shiga cikin gunkinsu tare da Kosa da Gurgu, suka sami kuge da ƙaho biyu da barandami da mari.
Goje ya dauki kugen da kahon nan biyu, Kosa ya dauki barandamı da mari, Gurgu ya dauki mari.
Yaji ya zauna a cikinta kwana bakwal, ya rushe ta sarai, ta zama babu gini ko itace. Bayan wannan ya komo garinsa, ya ce da Goje, "Fadi dukan abin da kake so, na ba ka. Goje yace "ba ni son kome sai ka naɗa mini sarautar Madawakin Kano".
Sarkin Kano ya ce. "Kai ne Madawakin Kano. Ya tube Madawaki Gasatoro, ya fita ya gina gida a gawo; saboda haka aka Kira shi da suna Madawakin Gawo, domin a rarrabe tsakaninsu.
Dutsen Santolo gagarumi ne, faffaɗa da doro, tsayinsa ya tafi kamar hawan bene daga baya, daga gabansa kuwa goshi yayi mai faɗi da santsi, tsakiyarsa yana da faɗi harma akwai koguna da akace dabbobin daji misalin su kyarkeci, dila da macizai na rayuwa a ciki.
Ko da yake, bamu ji sunan gunki da aljanar da aka ce akwai a saman dutsen santolo ba, amma har yanzu mutanen dake zagaye da wurin sun kiyaye cewar kakanninsu sun basu labarin cewar a zamanin da, ana taruwa ahau kan wannan dutse don neman wata biyan bukata.
Sannan kuma akwai wata rijiya zuzzurfa dake saman dutsen mai suna 'Rijiyar Giɗaɗo', wadda akan hana mutane zuwa kusa da ita saboda kuɓuta daga k'wank'waman dake wurin masu halaka mutane.
Zuwa yanzu garin santolo ya kasu biyu, akwai sabon garin santolo wanda kanawa (kabilar hausawa) ke ciki, sai kuma santolon fulani, amma dukkan su suna karkashin ikon dagaci mai suna Santolo Da'u.
Haka kuma dutsen yana nan a tsakiyar kauyukan sabon garin santolo, santolon fulani, Madawa, Koɗe, kyarmawa, da Tsakuwa waɗanda dukkanin su suke cikin gundumar Dawakin Kudu ta Jihar Kano.
8 Casino - New York State - MapyRO
ReplyDelete8 Casino is a 안산 출장샵 place where locals and visitors alike alike 동해 출장안마 can feel at home in New York State's top casino with over 서산 출장샵 1,100 slots, table 김천 출장샵 games 진주 출장샵 and live