Monday, 23 January 2023

Matsalar kuɗi

 Matsalar kuɗi


 (Money Problem)

Sadiq Tukur Gwarzo

Zuwa yanzu, abinda zantukan ilimi suka tabbatar shine, kowanne mahaluki a wannan duniyar yana da matsalar kuɗi, walau Attajiri ko Faƙiri, babban abinda ke rarrabewa a tsakani shine hanyar da kowanne mutum ke bi wajen warware matsalar kuɗin da ta fuskance shi, don haka wannan ɗan rubutu zai kalli waɗannan matsaloli da hanyar fita daga garesu.

Kuɗi wasu kawwamammun abubuwa ne masu ƙayyadajjiyar daraja wadda kowa ya yarda dasu, walau su kasance na takarda ko sulalla, ko na ma'adinai, ko su kasance taskantattu a wani muhimmin wuri wanda kuma ake amfani dasu wajen mallakar darajoji.

   Da yawan mutane sun ƙwallafa a ransu cewa basu da wata matsala sama da matsalar ƙarancin kuɗi, saboda sun lura da cewa wanda ya tara kuɗi yana da ikon warware yawa-yawan matsaloli, don haka babban burinsu shine su tara mamakon kuɗaɗe.

Akwai zantuka biyu masu cin karo da juna dake tattare da kuɗi gami da alaƙar kuɗin wajen tunzura aikata ayyuka musamman munana a wannan duniyar. 

Zance na ɗaya yana cewa "Son kuɗi shine tushen aikata duk wani laifi", yayin da zance na biyu ke cewa "Rashin kuɗi ne silar dukkan wasu munanan ɗabiu".

Sau tari da zarar an ambaci matsalar kuɗi, abinda ke zuwa a zukatan mutane shine 'ƙarancin kuɗi'. Yawa-yawan mutane ita suka sani, saboda ita tafi yawa, kuma ita akafi sani a matsayin matsalar kuɗi, amma a zahiri, abin ya haura haka.

 Ga abinda nazari ya nuna game da kuɗi da masu kuɗi:-

-Daga cikin mutanen duniya balagaggu sama da biliyan biyar, mutane miliyan sittin da biyu da rabi ne suka mallaki kashi 47.8 na arzikin duniya (1%). 

-Rahoton Oxfam na 2021 ya nuna cewar mutane goman da suka fi kowa kuɗi sun mallaki arziƙin da ya haura abinda mutane biliyan uku da miliyan ɗari ɗaya suka mallaka.

-Kashi 27 na attajirai sun faro ne daga tsatson talauci (Bank of America)

-Kashi 46 na attajirai sun samu arziƙi daga kyakkyawar tarbiyar sarrafa dukiya gami da gadon jari ko na kasuwanci  (Bank of America).

Saboda haka a taƙaice, matsaloli biyu ne ke tattare da kuɗi

1. Matsalar Ƙarancin kuɗi

2. Matsalar Yawaitar kuɗi

Kowacce babbar matsala ce wadda idan baka san yadda zaka yi da ita ba haƙiƙa zaka kasance cikin gagarumar matsala.

Attajiri na ɗaya a Afirka, Aliko Ɗangote, ya haɗu da matsalar ƙarancin kuɗi a shekarun baya, lokacin da yake ƙoƙarin gina gagarumar matatar man fetur ta afirka, amma saboda shi gwani ne a wajen warware matsalar ƙarancin kuɗi, ya jima da warware matsalarsa ba tare da kowa ya sani ba.

  Ɗangote yana sahun kaso 46 na daga ƙididdigar bankin Amurka, watau sahun attajiran da suka samu arziƙi daga kyakkyawar tarbiyar kasuwanci gami da jalin soma kasuwancin. Don haka tun da jimawa, ya gina ɗabi'unsa akan tarbiyar sarrafa dukiya, maimakon burga da burgewa. Wannan ya sa kuɗi da kansa yana son zama a tare dashi.

Matsalar ƙarancin kuɗi ita yawa-yawan mutane ke fama da ita, tunda ga abinda rahoton Bankin Amurka ya nuna can a sama, don haka da yawan mutane ke ɗaukar kuɗi shine jindaɗin rayuwa.

A zahiri, matsalar ƙarancin kuɗi abu ne mai muhimmanci ga duk wanda ya fahimce ta, domin ita ke tunkuɗaka yin tunani da ayyuka waɗanda zasu sauya rayuwarka daga talauci zuwa arziƙi, waɗanda kuma zasu hana ka wawanci idan ka shiga sahu na gaba, watau kashi ɗaya bisa ɗari na Attajirai a duniya.

Wannan yasa koda attajiri ya tsiyace, ake kiran yanayin da ya shiga da suna 'Broke', saboda yanayi ne wanda ba tabbatacce ba, yanayine tamkar makaranta wadda zata ta ƙara masa haske da karsashin sake ginawa kansa arziƙin da zai fi abinda ya mallaka a baya. Amma shi talaka, saboda ɗabi'unsa na rashin tafiyar da dukiya yadda ya kamata, ko nawa ya samu na ɗan lokaci ne, sai aga kuɗaɗen sun gudu sun barshi, don haka ake yiwa nasa laƙabin da suna 'poverty'.

Matsalar yawaitar kuɗi tana sanya mutum ya zama rago, shashasha kuma wawa musamman a harkar rayuwa ko ta kasuwanci matsawar bai ɗauki darussan dake cikin yanayin ƙarancin kuɗi ba. Sannan wannan matsala, ta kanyi silar mutum ya mutu cikin ɓacin zuciya.

   Mun  ga haka a rayuwar Mashahurin mai Kuɗin nan Pablo Escobar ɗan ƙasar Columbia, wanda ake zargin ya tara dukiya daga dillancin miyagun ƙwayoyi.

 Pablo ne wanda ya taɓa zuba zunzurutun kuɗi kusan dalar amurka miliyan biyu a wuta domin ta ruru, ta samar da ɗumi wanda zai sa ƴarsa ta daina kyarmar sanyi.. a lokacin da ya tserewa kamun jami'an tsaro.

Pablo ya bi miyagun hanyoyi wajen tara kuɗi, ya kuma yi amfani da kuɗin wajen cimma muradunsa, ya sa an kashe mutane da yawa waɗanda suka ɗaga masa yatsa, ya gina gagarumar daula. D

A lokacin da gwamnati ta kama shi ta tsare a kurkuku sai da ya siye kafatanin jami'an jarun ɗin ya tsere, daga bisani aka sake kamo shi, inda aka bashi dama ya gina Fursuna tashi ta kansa, wadda ya cikata da kayan alatu, da ɗumbin kayayyakin more rayuwa, amma dai a ƙarshe, ana zargin ya kashe kansa da kansa saboda gudun kamun jami'an tsaro.. kuɗin ba suyi masa rana ba.

Wani rahoto na kafar Business Insider ta Amurka ya nuna cewa ko ɗa gareka idan yana samun duk abinda yake nema a wurinka, karsashinsa na yiwa kansa abinda ya kamata yayi raguwa yake yi matuƙa.

Wannan yasa daga rahoton sama, kashi 27 kaɗai na talakawa ke iya jure fafutikar gina dukiya daga ƙuncin ƙarancin kuɗi.. saboda kiran dukiya yana buƙatar waɗansu ɗabi'u waɗanda dole sai mutum ya soma aikatasu na tsawon lokuta kamar yadda marubuci Tom Corley ya kawo a littafinsa 'Rich Habits'  bayan ya shafe shekaru yana nazartar rayuwar attajirai.

Haka kuma dalili kenan da yawa-yawan attajirai (kashi 46 daga rahoton Bank of America) suka samu tarbiyar kafa kasuwanci da kuma jarin soma kasuwanci, saboda sun samu abinda yawa-yawan mutane basu dashi, don haka sunfi zarafin zamowa attajirai.

  Talakawa da yawa basu gane haka ba. Akwai ɗabi'u da ayyuka na mutane waɗanda ke ƙara cusa su cikin talauci, a tsammanin wasu, gwamnati zata rage musu raɗaɗi, amma akasari duk abubuwan da gwamnatoci ke yi suna ƙara dankwafar da talaka cikin talauci ne da ƙara arziƙa mai arziƙi, saboda a duk sa'ar da kace zaka yiwa mutum abinda ya kamata ya yiwa kansa, a zahiri cutar dashi kayi ba taimakonsa ba.

A taƙaice, Wajibi ne mutum ya koyi rayuwa da ƙarancin kuɗi matsawar yana so kada kuɗin su tunzura shi aikata shiririta a yayin da ya tsallaka fagen attajirai masu matsalar yawan kuɗi.

 Ga duk inda matsala ra samu, akwai wani darasi dake rattare da ita. Fahimtar wannan darasin da aiki dashi sune abubuwanda zasu ƙara maka daraja a ayyukanka na gaba.

 Sannan yana da kyau a sani cewa ba kuɗi ne mafi muhimmanci a kasuwanci ko a rayuwa ba, duk abinda zaka mallaka, matsawar ka rasa farin ciki, ai kuwa sam ba suyi maka rana ba. Haka nan, duk abinda ka rasa na dukiya, matsawar ka samu farin ciki, ai kuwa ka mallaki abinda ya fisu.

Saboda haka, idan kana da matsalar ƙarancin kuɗi, ya kamata ka soma koyon ilimin nema da sarrafa dukiya.

 Sannan idan har ka iya kafa kafar warwarewa mutane matsalolin dake damunsu, tabbas da sannu zasu kawo kuɗin da suka mallaka zuwa gareka.

Haka kuma, yana da kyau ka koyi dabarar farantawa na kusa da kai domin samun dacewa da farin ciki daga mahalicci..

Thursday, 6 October 2022

YADDA AKA YI BAUTAR KURMIN JAKARA A KANO

 BAUTAR JAKARA


Ga abinda ya zo a littafin Tarihin Kano game da Bautar Kurmin Baƙin ruwa ko ace kurmin Jakara.

'Ma'abutan wannan ƙasa (Kano) waɗanda Bagauda ya same su a cikinta suna muljin garinsu, ba su bin kowa sai Tsumburbura da duhuwa tasa JAKARA. Ana ambatonta (duhuwar) da KURMIN BAƘIN RUWA, domin shi ruwa ne baƙi, duhuwa ta kewaye shi, ana kiyaye dukan musiba da ita da gunkinsu, mafarinta kuwa daga Gurgumasa har zuwa Dausara. Kiraranta da zartakenta ba su motsi sai idan musiba ta gabato wannan gari ta yi kuruwa sau uju, hayaƙi ya riƙa fitowa daga cikin Tsumburbura, wanda ke cikin tsakiyar ruwa. Sai su nemi baƙin kare su yanka a ƙarƴashin Tsumburbura, kuma su yanka baƙin bunsuru a cikin duhuwar.

   Idan hayaƙi da kururuwan sun daɗu, to babu makawa sai musibar dɗta sadu dasu. Idan kuwa ba su daɗu ba, babu masiba. Sunan duhuwan nan kuwa MADAMA. Kuma sunan Tsumburbura RANDAYA'.

Ƙarin Bayani game da KURMIN JAKARA

Ita Jakara ana kiranta da suna KURMIN-BAƘIN-RUWA saboda ruwan tafkin baƙi ne, kuma kewaye take da bishiyoyi masu yawa. A cikin bishiyoyin ne akwai guda ɗaya da aljani yake kanta, wadda suke yin tsafinsu a kanta, kuma wadda take yin hayaƙi idan musiba ta tunkaro Kano. Ita wannan bishiyar a tsakiyar ruwan take. Wannan daji mai yawan bishiyu sunansa MATSAMA, Bishiyar Tsafin kuma itace RANDAYA. Ɗaukacin wajen shine Jakara har zuwa inda Kasuwar Kurmi take a yanzu.

Daga Littafin KANO TA DABO TUMBIN GIWA na Alhaji Ahmad Bahago

Sunday, 31 July 2022

HANYAR KANO: TARIHIN DA KE GURIN GAWA

 HANYAR KANO: TARIHIN DA KE GURIN GAWA


SADIQ TUKUR GWARZO

Kamar yadda marubutan littafin 'Urban Society ' Gist da Halbert suka faɗa, kuma kamar yadda yake game da asalin ita kanta Wayewar, tushen kowanne birni kusan ya samo asali ne daga hijirar mutanen ƙauyuka.

Birane sune cibiyar hadar-hadar kasuwanci, tsaro, al'adu, ilimi da bincike. Don haka ya sanya mutanen karkara na kusa da na nesa, da ma wasu mutanen da ke wasu biranen da dama kan ziyarci birane domin samun mafakar tsaro, ko kasuwanci, ko samun ilimi ko cimma wani dalili na al'ada da ma sauran muradai walau ziyarar ta kasance ta wucin gadi ko kuma ta-din-din-din. 

  Akwai ilimin tarihi mai yawa da mukan rasa yayin kawar da kawunan mu ga tafarkan da suke sadar da mutane zuwa waɗancan birane. Wannan kuwa ya haɗar da tarihin wasu muhimman abubuwa da aka taɓa yi ko kuma muhimman wurare masu dangantaka da biranen kansu.

Sau tari a ƙasar Hausa mutane kan niƙi gari domin ziyartar wani birni amma sai su shantake a wasu wurare na kusa ko na nesa da biranen bisa wasu dalilai. Haka kuma a wasu lokutan, sauyawar yanayai kan tursasa mutanen cikin birane komawa makusanta ko manesantan garuruwa ko birane da zama.

 Garin Gurin Gawa na ɗaya daga cikin ƙauyukan da suka kafu a turbar kano. Hasashe ya nuna cewar mabanbantan mutane da akasarin su ƴan tafarki ne suka kafa garin tsawon lokaci da ya shuɗe. Garin yana kudu da garin kano, akan turbar da zata shigar da mutum birnin kano ta ƙofar Ɗan Agundi (wadda aka sara a wajajen shekarar 1499AD). Don haka duk mutanen da suke son shiga kano daga yankunan Rano, Jos, sassan ƙasar Bauchi da makamantan su sai sun bi ta wannan turba.

ASALIN SUNAN GURIN GAWA

Akwai mabanbantan zantuka game da asalin sunan Gurin Gawa.

1. Na ɗaya: Gurin Gawa daga Gurin Gawarwaki. Ance an samo sunan ne daga kasancewar wurin filin daga. Watau a zamanin yaƙi, da zarar kano ta samu labarin an tunkaro ta da yaƙi ta wannan shiyya, sai ta turo dakarunta ta jibge su a wannan wuri. Don haka anan za a fafata yaƙi, anan kuma za a samu tulin gawarwaki bayan ƙarewar yaƙi. 

2. Na biyu: Gurin Gawa daga 'Gurin-Ge'

Wannan ra'ayin yana cewa an samu sunan ne daga wani Bafillatani mai suna Gurin-ge, wanda kiwo ya biyo dashi ta wajen har kuma dabbobin sa suka gano masa wani kwarmin ruwa, don haka ya mayar da wajen mazaunin sa, daga bisani ƴanuwansa fulani suka riƙa riskar sa da zama.

3. Na uku: Gurin gawa daga Gurin da aka samu  gawar Kuyangar Sarkin Rano

Ance akwai wani rafi tsakanin Medile da Gurin Gawa wanda ake kira 'Ci-kuyangi', saboda yadda yayi silar mutuwar kuyangi da dama a ciki har da wata amintacciyar kuyangar Sarkin Rano wadda ta rasu a wurin akan hanyarta ta shiga Kano, ance daga nan aka samo sunan na Gurin Gawa.

  Zuwa yanzu, garin ya kasu kashi biyu, akwai Ruga inda fulani masu sarautar garin suke, da kuma ɓangaren Hausawa inda ake kira Dausayi. Anan ne mahaifiyar shahararren masani marigayi Sheikh Nasir Kabara ta ke.

TASIRIN SHAHARAR KANO GA SAURAN MAKUSANTAN GARURUWA

 Kasancewar birnin Kano birnin kasuwanci ne ba birnin Siyasa ba, ya samu ɗaukaka tsawon lokaci saboda yadda fatake ke tururuwar zuwa gare shi bisa dalilan kasuwanci. Wannan ya taimakawa birnin wajen zamowa shahararre, shahararsa kuwa ta yi tasiri ga makusantan ƙauyuka wajen karɓar baƙi a ko-da-yaushe, da kuma hada-hadar kasuwanci.

Kamar yadda aka sani, a baya babu tsarikan otal ko masaukai a ƙasar Hausa, sannan akan rufe ƙofofin shiga birane  idan dare yayi. Saboda haka, matafiya a zamanin baya sukan samu waje da suka aminta da amincin sa su yada zango idan dare yayi kafin su ƙarasa cikin birni. Don haka kafuwar ƙauyuka a kusa da birane kan zamo masaukai ga baƙin da suke haramar shiga kano yayin da dare yayi musu.

 A irin haka ne aka samu wani mutumi daga ƙasar Bade ta cikin jihar Yobe a yanzu haka ya yada zango a Gurin Gawa tare da soma sana'ar Kwarami (awo), inda ya samu shahara a wannan sana'ar, ya rinƙa sauƙaƙawa fatake masu zuwa kano da jakuna siyan hatsi da kuma masu fitowa daga kano neman haja ba tare da sunyi dogon zango ba. (Har yanzu ana yiwa mazaunin wancan babarbare laƙabi da suna 'Marken Bade').

  A ƙarshe, ina da ra'ayin cewar muhimmancin buƙatar bibiyar tarihin manyan tafarkan da suke sadarwa zuwa biranen mu tamkar na sanin tarihin biranen ne.

HANYAR KANO: TARIHIN RIMIN GADO

 HANYAR KANO: TARIHIN RIMIN GADO


SADIQ TUKUR GWARZO


Akan yiwa garin Rimin Gado kirari da cewa "Rimin Gado garin ƴan lalle", silar hakan kuwa shine, Allah ya baiwa garin yalwa ta bishiyoyin lalle, wanda a zamanin baya ya kasance itace mai daraja wanda mutane ke rububin neman sa domin yin amfani da shi a matsayin sinadarin tsaftace jiki da magani da sauran su.

 Wannan gari, a zamanin baya, ya zamo kasuwa matattarar fatake inda mutane ke niƙo gari daga mabanbantan sassa domin siyen lalle da sauran hajoji.

A binciken da Mallam Muhuyi Magaji Rimin Gado yayi, ya sanya kafuwar garin Rimin Gado da kimanin shekaru 300 da suka gabata. Kafin zamowar Rimin Gado gari, inda Rimin Gado yake a yanzu ya kasance (zango ne) wurin saukar matafiya ne masu kara-kaina tsakan-kanin birnin Kano da biranen da ke yamma da ita misalin Sokoto.

  KAFUWAR RIMIN GADO

Ance akwai wani mutum mai suna Magili, mabaraci ne, wanda ya taso daga Degel; wani ɗan ƙaramin gari dake jamhuriyar Nijar ayau zuwa inda garin Rimin Gado ya ke, don haka ana iya cewa shine asalin kafuwar wannan gari.

Bisa al'ada ta mabarata, sukan samu gefen turbar da mutane ke shigewa su fake suna addua ko zikirai ko waƙoƙin nasiha ga matafiya da makamantansu da nufin neman sadaka daga masu shigewa. Magili ya gina gadon ƙasa a inda garin Rimin Gado ya ke a yanzu, a gefen turbar da matafiya ke wucewa zuwa birnin Kano, akan wannan gado yake zama yana bara a ko-da yaushe.

ASALIN SUNAN RIMIN GADO

Ance Magili,  wanda yake zama akan gadon da ya gina na turɓaya yana bara da rana sai kuma ya kwanta bacci idan dare yayi, ya samo ƙwanson Rimi da ya tattara a matsayin matashin kai wanda yake ɗora kansa yayin bacci. A kwana a tashi sai ƴaƴan rimin da ke cikin ƙwanson ya rinƙa zuba daga gadon nasa zuwa ƙasa, har kuma aka yi sa a tsiron bishiyar rimi ya fito a wajen wanda daga bisani ya girma ya zama bishiya gagaruma wadda ake zama don hutawa ko don gudanar da cinikayya a ƙarƙashin ta. Daga nan ne fa aka samo sunan 'Rimin Gado' wajen nuni da bishiyar Rimin da ya girma a ƙarƙashin ko a kusa da gado. 

  Sannu a hankali wannan wuri ya haɓaka ainun tare da zamowa dandalin yada zangon fatake masu son shiga kano waɗanda akasarin su suke tafiya a ƙafa, ko a jakuna da sauran ababen hawan lokacin daga birane irin Alƙalawa, Sokoto da sauran su.

  TURBAR KANO TA SASHEN RIMIN GADO

  Wannan turba ta soma ne daga ƙofar Kabuga wadda take a yammacin kano, ta keta ta shacin Janguza, ta wuce ta Yalwan Ɗan ziyal har zuwa wannan gari na Rimin Gado. Daga nan kuma sai ta cigaba da nausawa sashen yamma har ta keta Gwarzo zuwa wasu sassan ƙasar Katsina. Kuma kamar yadda tarihi ya nuna, ta wannan turbar ne aka rinƙa samun sadarwa a tsakanin biranin Kano da biranen da suka kafu a zamanin baya waɗanda a yanzu suke cikin jihar kanon kanta, da Katsona da Zamfara daa Sokoto da Kebbi har zuwa sassan ƙashen Mali da  Nijar. Kuma haƙiƙa, ba iya Rimin Gado ba, akwai garuruwa da dama da kafuwar su ya samu ne daga albarkar wannan turba.

Wednesday, 16 February 2022

WAƘE: RABBI KARE MIN MIJINA

 Rabbi kare min mijinaaa

Abin kirana farin ciki naaa


1. Ni ina sonsa sahibina

Shi nake so nake wa ƙauna

Shi yake sanya murmushi na

Shi yake yaa yen fushi na

      Shi nake yiwa kwalliya ta

      Ina adon gyara fussskata

      Na sanya kwallin idaniyata

      Na fesa ƙamshi ga suttura ta....

     Rabbi kare min mijina!!!


Rabbi amsa min kira na!!!

Rabbi kare min mijina!!!


2. Ni a guna sam bai da tamka

Duk sirrikana shi zasu riska

Da nay fushi, in yazo na sauka

Hidimtakarsa ke sani kuka

      Ya abin so farin cikina

       Na mallaka maka dukka kaina

       Ina ƙaunar ka dare da Rana

      Ina yawan sonka sahibiyna...

Abin kirana farin ciki naaaa!!!


Rabbi kare min mijinaaa

Abin kirana farin ciki naaa


3.  Yau da kullum na ayyukansa

Hawa da sauka a lamurransa

Yana cikin sauke haƙƙunan sa

Yana yawan bani lokacin sa

      Shi ya sanya nake ta son sa

      Ina ta Rama don ambaton sa

       Ina shirin kare lafiyar sa

       Ina nufin na zama garkuwar sa...

Haba masoyi ka ceci raina!!!

Rabbi amsa min kira na!!!

Rabbi kare min mijina!!!


4.   Son ka ya keta zuciya ta

   Yayi cafkar idaniya ta

   Yana ta yawo a jijiya ta

   Son ka shineee Rayuwa ta

       Zan biyayya a lamuranka

       Zan yi tamkar Sa ɗakar ka

       Zan duƙursawa zantukan ka

       Zani girmama ƴanuwan ka...

Ni ina sonka ya miji na..


Rabbi kare min mijina

Abin kira na Farin cikina 


5.     Shine mijina farin ciki na

Shine yake gyara laifuka na

 Shine yake saita lammura na

 Shine yake ɓoye kuskure na

      Bautar sa Bautar Ubangiji ne

      Fushin sa wannan abin gudu ne

       Ka ɓata rai ko nayo kure ne

        Haba masoyi, rashin sani ne..

 Ka ceci raina, ya kai mijina!!!


Ni ina son masoyiyata

Son ki ke mulka zuciya ta.

haƙƙin mallaka @Sadiq Tukur Gwarzo

Sunday, 30 January 2022

MUYI KOKARIN KARE KAWUNAN MU DAGA RIBA

 MUYI ƘOƘARIN NESANTA KANMU DAGA RIYA, ƘARAMAR SHIRKA. 

   Allah Ta'ala ya umarci masu imani a cikin littafin sa Alqur'ani da cewa su bauta masa, kada kuma su haɗa wannan bauta da ta waninsa. Harma ya kira aikata haɗa bautar Sa maɗaukakin Sarki da ta wanin sa a matsayin zalunci wanda yake abu maigirma. 

  Annabi Muhammad (s.a.w) ya bayyana Riya a matsayin shirka wadda take ƙarama, wadda kuma Allah ba ya amsar aiki komai kyawunsa matsawar akwai ta a ciki.

 Malamai sun fassara riya a matsayin 'yin abu don neman yardar mutane, ba don neman yardar Allah ba'. 

   Shin yardar Allah muke nema ko ta murane a ayyukan da muke aikatawa? 

   Mallam Umar Sani fagge yayi tsokaci akan haka, inda yace "Idan kana so ka auna cewa akwai Riya acikin aiyukanka, to kayi duba acikin waɗannan abubuwan guda biyu;

   1. Na farko, Ibadar Ka.

Mallam yace, ka auna Sallar ka da sauran ibadun da kake yi duka, idan har ka samu cewa kana yin su da kyau acikin/gaban jama'a sama da yadda  kake yinsu kai kaɗai, haƙiƙa kana aikata Riya; ƙaramar shirka. 

Mallam Ya ce "Ba ibada kadai ba, hatta sadaka, kyauta da sauran ayyukan alheri, indai kana fifita yinsu akan idon jama'a don jama'ar suyi maka shaidar kai mai aikata aiyukan alheri ne, a bayan idonsu kuma ba ka yi, haƙiƙa kana aikata Riya. "

A ranar alqiyama kuma Allah zai tozartar da duk mai aikata Riya, Allah Ta'ala zaice masa 'kayi abu kaza da abu kaza don mutane suce kayi, kuma sun faɗa, don haka baka da lada a wurina'. Daga nan sai mala'iku su kifa fuskar mai aikata Riya da qasa, su jashi izuwa wutar jahannama. (Allah yayi mana tsari da ita).

  2. Abu Na biyu: Rayuwar ka

Mallam Umar Sani Fagge ya labarta mana wata ƙissa, inda  yace "watarana wani mutum yana yawo, yana sanye da riga mai tsada, wadda farashinta zai tasarwa dirhami arba'in, sai Sayyadina Umar(R.A.) ya kirashi yake tambayar sa nawa ne jalin kasuwancin sa da har yake sanya irin wannan tufafi? Sai wannan mutumi yace Jalinsa yakai misalin dirhami dubu daya. Sai kuwa Sayyadina Umar (R.A) ya dakeshi da sanda, sannan yace "Amma kake sanya irin wannan tufafi saboda Riya?" Akace ana cikin haka kuma sai ga Sayyadina Abdurrahman bn auf (R.A) yazo wajen yana sanye da tufafi wadanda darajarsu takai ta durhami dubu hudu (Mallam yace sama da miliyan dari kenan a yanzu), amma Sayyidina Umar bai ce masa komai ba."

 Sai Mallam ya cigaba da cewa "dalilin haka shine, wannan mutumi mai jarin durhami dubu, idan aka ƙyaleshi yana sanya tufa kurum na durhami arba'in, watarana sai ya karya jalinsa da kansa, domin yana yin abinda matsayinsa bai kai ba, yin hakan kuma nau'I ne na Riya. Shikuwa sahabi Abdurrahman bn auf, Allah ya bashi mamakon dukiya, yana da ikon sanya tufafi masu tsada ba tare da ya girgiza ba".

 Don haka Mallam yace, "duk wanda yake ƙuƙutawa ya sayi wani abu, ko yayi wani abu sama da matsayin da Allah ya ajiye shi don gama da nuna isa, wannan Riya ne, Allah ba yaso, idan mai aikata haka kuma bai tuba ba, zai gamu da fushin Allah a ranar alqiyama". 

  Lallai Riya babban lamari ne da ya kamata mu yi ƙoƙarin kare ayyukan mu da shi. Lallai Allah Ta'ala ne mafi kyautatuwar miƙa lamura da kuma neman yarda daga gareshi ba sauran mutane ba. 

  A sani cewa duk wanda Allah Ta'ala ya so, kuma ya ƙaunata, to Mala'ikun sa masu tsarki zasu ƙaunace shi, hakanan  al'umma zata ƙaunace shi kamar yadda yazo a cikin Hadisi.

  Dafatan Allah ya kiyaye mu daga dukkan wani nau'I na Shirka. Amin. 

#Sadiq Tukur Gwarzo