Wednesday, 6 December 2017

FAHIMTA FUSKA, INJI MALLAM IBRAHIM KHALIL

FAHIMTA FUSKA inji Mallam Ibrahim Khalil.


Mallam ibrahim khalil, shine wanda akafi sani da bayar da fatawowi masu sauki acikin lamuran addini. Har ake masa lakabi da suna 'fahimta fuska', an taba tambayar sa cewa " Me ake nufi da fahimta fuska?" Sai yace
 "Ma'anar fahimta fuska abubuwa ne guda biyar.
 Na daya; kowanne mahaluki idan ka kalleshi, zakaga fuskarsa tasha bam-bam data saura koda kuwa tagwaye ne. Wannan na nufin dukkan dan Adam nada tunani da fahimta daban data waninsa.
Na biyu yace Ma'anar fahimta fuska shine Ka gamsu cewa duk yadda kakai gajin cewa an saba maka a fahimta, to an saba maka ne saboda hakan aka fahimta. Sannan kuma kaima duk yadda kakai ga fahimtar lamurori, to ka sab'awa wani a tunani ko a fahimta.
  Na uku Mallam yace "ka sani cewa kowanne mahaluki zai iya saba maka a fahimta ko a tunani kamar yadda yake sabawa kansa-da-kansa. Domin yau zakaga mutum ya siyi sabon abu na alfahari, amma a gobe zakaga yana neman canjinsa saboda sauyawar tunani". Don haka mallam yace" idan har mutum yana sabawa kansa-da-kansa a fahimta, me zaisa ya rinka fada da waninsa akan sabanin su ga fahimta?"
Na hudu Mallam yace " yadda kowanne mutum yake kallon lamurori yasha bam-bam da yadda sauran mutane ke kallo. ( Kamar misalin daki ne, idan akace mutane su leka ta taga, abinda wannan zai hango sai yasha bam-bam da abinda wancan zai hango, kuma duk a daki guda). Har mallam yake bada misali da cewa ' Wata Rana Annabi Isah (AS) ya shige wani mushe. Sai yake cewa da mutanen sa' me kuka gani game da mushennan?' Sai mutanen suka ce 'me kuwa zamu gani sama da dabba wadda ta kumbura kuma ta bushe?' Sai Annabi Isa ya kara cewa 'Yanzu ku bakuga wani abu da zakuce madalla ko na yabo a jikin mushen ba?' Sai suka kara amsawa da cewa 'babu wani abu da muka gani' Sai yace 'ku dubi hakorin wannan dabba fa kyakkyawa ne fari tas har da wushirya'. Sai mallam yace 'to kaga shi, ya hango musu cewa duk munin abu akwai wani abu mai kyau a taredashi. Kuma duk inda kakai ga kallon abu, sai wani ya fika gano kyau da sharrin wannan abu.
Sai abu na biyar, Mallam yace " Babu yadda za'ayi ra'ayin al'umma yazo daya har abada. Duk kuwa wanda tunanin sa ya bashi haka, hakika yazo da kuskure, domin fadar Allah Ta'ala da yake cewa "mutane ba zasu gushe suna samun sabani ba sai wanda Allah ya yiwa Rahama". Rahamar nan kuwa inji Mallam itace idan kun saba kada kuyi fada, kada kuyi rigima, domin mai yiwuwa kuzo ku hadu a wani wuri.
Bayan kammala wannan jawabi, sai wani yake tambayar mallam da cewa "Mallam me zaka ce game da masu ganin cewa kamata yayi adaina kallon yanayi wajen bayar da fatawa, arika farke komai ba tare da la'akari da yanayi ko sassauci ba? Sai Mallam ibrahim khalil ya amsa da cewa "To kaga wannan ma fahimta fuska din kenan.." (Amma dai mallam yana da fahimtar duban yanayi da kuma sassauci wajen bada fatawa, ba kuma ya zargin malaman da basa bin irin fahimtarsa, saboda yasan iya abinda suka fahimta sukeyi).
A wajen Mallam Ibrahim khalil, addini mai sauki ne. Fahimtar addini kuwa babbar baiwa ce wadda ba kowa ke samu ba, kamar abinda hadisin manzon Allah (saw) ke cewa ce "wanda Allah ya nufeshi da alheri, sai ya fahimtar dashi addini". Kuma Mallam baya tsaurarawa mutane a fatawowinsa na addini, "Wannan fa shine falsafar; hanyar tunani da fahimta ta mallam Ibrahim Khalil. Kowanne dan adam kuma yana da irin tasa. Don haka Fahimta fuska.
 Da fatan Allah ya kara masa lafiya. Allah ya fahimtar damu addini da ilimai da fahimtarwa mafi dacewa. Amin

No comments:

Post a Comment