Wednesday, 6 December 2017

TARIHIN GWAGWARMAYAR MULKIN FULANI A KANO 2

TARIHI: MULKIN FULANI A KANO, DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na biyu

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN
     08060869978

Mulkin Sarki Ibrahim Dabo ɗan Mamuda.
   Bayan Allah ya karɓi ran sarkin kano Sulaimanu ɗan Hama bafillatani na farko a jerin sarakunan kano, sai Sarkin Muminai na lokacin Muhammadu Bello ya aiko da takardar naɗin Ibrahim Dabo a matsayin Sarki, tare da umarnin sauran malumman nan da suka jagoranci yakin jihadi su cigaba da kasancewarsu a matsayin rukunin masu zartaswa wanda sarki bazai aiwatar da wani lamari ba sai da sahalewarsu.
   Koda yake, izuwa wannan lokaci ance akwai waɗanda Allah yayiwa rasuwa misalin Mallam Abdurrahman wanda aka naɗa ɗan ɗanuwansa Mallam Jibrila mai suna Ummaru a muk'aminsa, sai kuma Mallam Jamo wanda shima Mallam Ibrahim Dabo ya soma zamowa magajinsa bayan rasuwarsa kafin kuma Sarki Sulaimanu ya rasu har a zaɓeshi a matsayin sarki.
  Baya da haka, sai kuma waɗanda aka tura shugabanci suka bar kano izuwa wasu sassan, misalin mall mam Amadu da aka naɗa Sarkin Gaya, da kuma Mallam Muhammadu Bahr Ajami ɗan Alhaji da aka tura ya zama sarkin Dawaki.
  Mallam Sulaiman Ango shi aka naɗa Wambai a masarautar kano, yayin da Mallam Muhammadu Sani yake a matsayin Waziri, amma bayan rasuwarsa sai aka ɗaga likkafar wambai ya dawo waziri.
    ƁBayan Sarki Ibrahim Dabo ya hau karagar mulkin kano, sai ya turawa 'yanuwansa sarakunan garuruwa da takardu yana mai sanar musu sarautar daya samu. A bisa haka ma ya turawa Dantunku takarda yana mai sanar dashi cewar yanzu fa shine sarkin kano, amma sai Dantunku ya maido da ba'asi na lafuzza masu ɓata zuciya. Badon komai ba sai saboda Sarki Ibrahim Dabo ya nemi Dantunku ya cire hannunsa daga sha'anin kabilar wadaɓe, sai kuwa yace da sarki Ibrahim Dabo sam ba zan cire hannusa daga mutanen da yake da alaka dasu ba.
  Shi Dantunku shine sarkin Kazaure, kuma tare akayi yak'in jihadi dashi har aka samu nasarar karɓe iko da Kano, inda aka tabbatar dashi a matsayin sarkin Kazaure. Amma daga baya sai wasu dalilai suka sanya ya soma yunkurin yin bore
  Bayan anyi wannan, sai Sarki Ibrahim Dabo ya tafi Sokoto domin kai ziyarar ban girma ga sarkin musulmi. A lokacin sai kuwa Dantunku ya soma aikewa ga yankunan maguzawa cewar yana neman taimakonsu domin suyiwa fulani masu sarautar kano bore.
   Abu fa kamar wasa, kafin wani lokaci Dantunku ya tara gagarumar zuga har ya zamo yana yunkurin kwace iko da gabashi da kuma yammacin kano.
  Wannan yasa dole sarki Ibrahim Dabo ya shirya zama da kwamitin malamai inda suka yanke shawarar cewa a tura runduna domin takawa Dantunku burki tun da wurwuri.
  Rundunar farko ta tashi ta nufi yankin garin bichi Bisa jagorancin Madaki, sai da suka isa garin Danzabuwa, sannan suka haɗu da dakarun Dantunku. Anan aka gwabza wani kwarya-kwaryan yaki wanda kowanne cikin rundunonin biyu sai da yaji jiki, sannan aka rabu.
   Madaki yaja zuga sukayi yamma, daga bisani suka haɗe da Mallam Ali da Mallam Bakatsine dukkaninsu da tawagar mayaka, sannan suka komo garin mazan gudu suka yada zango.
  Da dare sai ga rundunar Dantunku itama ta sauka a wannan guri, mai cike da tururuwar mayaka.
  Gari na wayewa rundunonin biyu suka fuskanci juna, kafin daga bisani suka rinchaɓe da faɗa.
  A wannan yakin ne Gwani Hafizu Muhammad masanin alkurani maigirma ya rasu, sannan an kashe musulmai masu yawa ciki harda Mallam Ali, aka kame wasu a matsayin fursononin yaki tare da kone gidajen dukkan musulman dake yankin.
 Hakika rundunar sarki Ibrahim Dabo tayi gagarumar asara a wannan yaki.
   Daga nan fa sai yanayi ya soma tsamari ga fulani. Runduna ta koma baya babu nasara, gashi kuma Dantunku sai yayibar mayaka yakeyi, mutanen da suka koma musulunci bisa tsoron karfin fulani suka soma samun sakewa da damar komawa ainihin al'adarsu ta baya. Zaman kano ya soma zama abu mai wahala saboda tsoron mahara masu kamen fursunonin yaki da kuma fargabar yaki.
   Ance ana haka sai Sarki Mallam Ibrahim Dabo ya shiga Halwa a gidansa.
  Qadi Muhammad zangi ya ruwaito a Littafinsa 'Tayqidil Akbar' cewar sai da Sarkin ya shafe shekaru biyu a wannan halwa a gidansa wanda babu mai shiga wurinsa sai bayi masu yi masa hidima kurum. Babu abinda yakeyi sai neman nasara daga Allah ta'ala. Daga nan ne ya fito.
  Da fitowarsa sai ya yanke shawarar kafa sansanoni biyu domin samar da tsaro ga kano. Ya aike da runduna dawakin Tofa, ɗaya kuma ya aike da ita Ungogo.
Babu jimawa ne sai ga Dantunku yayo hawa, ya nufo kano da yaki, amma da isarsa Ungogo sai sadaukan Sarki Dabo suka tareshi da yaki. Allah cikin ikonsa ya basu nasara inda suka koreshi tare da watsa tawagarsa.
  Daga nan sai Sarki Dabo ya sake kafa wasu sansanonin a Dan madafo, da Mariri da Tanqarqar. Sannan yasa aka shiga atisayen horas da dakaru dabarun yaki.
Baya da haka yasa aka tara masa dakarunsa wuri ɗaya, yazo garesu tare dayi musu jawabi. Yayi zantuka masu sanya dakiya a zukata garesu, ya janyo ayoyin alkurani da hadisai masu karfafa zuciya ga dukkan mai shirin yin jihadi, sannan ya nemi suyi shirin yaki gagarumi..

No comments:

Post a Comment