TARIHI: MULKIN FULANI A KANO, DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.
Kashi na ɗaya
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN
08060869978
Gabatarwa
Sarki Sulaimanu ɗan Aba Hama shine sarki na farko a jerin sarakunan fulani na kano tun bayan da fulanin suka jagoranci yakin jihadi tare da karɓe iko da kasar kano baki ɗaya.
Sai dai kamar yadda aka sani, kowanne mulki ya kanzo da kalubale mabanbanta. Don haka rubutun zai kalli yak'unan da sarakunan fulani suka gwabza da abokan hamayya masu son ɗaukar fansa daga garesu, ko kuma ace masu son kwace kasarsu ta haihuwa daga hannun fulani baki.
Haka kuma, zamufi maida hankali ne akan rikice-rikicen da suka auku daga zamanin Sarkin Kano Sulaimanu izuwa yakin basasar Kano, da kuma zuwan turawa birnin na kano.
Sarkin Kano Sulaimanu
A zamaninsa ne aka halaka tsohon sarkin kano Alwali bayan ya dawo garin burum-burum da zama daga zariya inda ya fara yin hijira.
Wasu sunce Mallam Bakatsine Sarkin kano Sulaimanu ya tura domin yaje ya halaka Sarki Alwali, amma wasu na ganin Mallam Jamo ne jagoran rundunar ba Mallam Bakatsine ɗin ba.
Amma dai abu mafi inganci shine, wannan runduna ta isa garin burum-burum, tayi gagarumin faɗa da rundunar Sarki Alwali, a karshe ta samu nasarar halaka sarkin acikin garin burum-burum inda ya fake, tare da komowa kano da ganimar yaki mai yawa.
Sheikh Abdullahi Ibn Fodio (Kani ga limamin yakin jihadi shehu Usmanu ɗan fodio) ya ziyarci kano a zamanin mulkin sarkin kano Sulaimanu, a watan azumin Ramadana, har ma ance shine wanda ya nuna alkiblar masallacin kano na jumu'a dake kofar fadar Sarki, sannan shine yayi jagorancin sallar nafila bisa rashin lafiyar Rana (khusufin Rana) daya faru a wannan watan na Ramadan.
Tarihi ya nuna cewar Sheikh Abdullahi ɗan fodio ya zauna a Kano na wani lokaci, ya kuma karantar da mutane ilimin addinin Islama, tare da rubuta wani littafi garesu mai suna 'Diya'ul Hukamah' domin taimakonsu wajen sauke nauyin mulkin daya hau kan jagorori bisa bukatarsu da suka nuna gareshi. Sannan yayiwa kano addu'a matuka dangane da yalwatar arziki da nema mata tsari daga dukkan sharri.
Ance shekaru goma sha uku Sarki Sulaimanu yayi yana mulkar kanawa, amma ba'a samu fitintinu sosai ba a lokacin mulkinsa.
K'ari akan yakin kashe sarki Alwali da akayi a zamaninsa sai yakin da akayi da maguzawan wani gari mai suna Fagam. Inda sarkin yahau da kansa akaje akaci garin da yaki tare da kamo fursunoni da ganimar yaki.
Baya da wannan kuwa sai boren da sojojin tumbi suka tayar, inda suka rinka tare mutane suna musu fashi. Suma sai da aka je kansu da yaki sannan aka samu lafiya.
Sai dai, akwai wani mai suna Dantunku a zamanin, wanda ya rinka tara sojoji da shirin yak'i a ɓoye ba tare da masarautar kano ta sani ba har sai da sarki sulaimanu ya rasu sannan ya soma ɗaga kara..
Sarki sulaimanu ya rasu ranar wata lahadi da dare, a karshen watan shawwal.
Da fatan Allah ya gafarta masa amin.

No comments:
Post a Comment