TARIHI: YADDA JIHADIN FULANI YA KASANCE A KANO
Kashi na bakwai.
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
SOMA SARAUTAR FULANI A KANO DA SARKI SULAIMANU
Mallam Sulaimanu shine sarkin Kano na farko a jerin fulani. Tun bayan da Sarki Alwali ya fice daga kano, fulani suka shige mata, sai ya zamo sun karɓe iko da ita baki ɗaya.
Qadi Muhammadu Zangi bai faɗi yadda aka zaɓi mallam Sulaimanu a matsayin Sarki ba duba da akwai manyan malumma da suka jagoranci gwabza yakin jihadi a kano, misalin su Mallam Abdurrahman, da Mallam Jamo, da Mallam Jibrila da Mallam Bakatsine, da Mallam Danzabuwa da Mallam Usmanu Bahaushe da wasunsu.
Abinda ya ruwaito a Littafinsa Tayqidil Akbar shine: Masani Muhammadu Bello ya haɗu da tawagar malumman kano da suka jagoranci yakin jihadi a Birnin Gada. Sai ya basu takarda mai umartar su da cewar su zaɓi sarkinsu da kansu. Daga nan kuma sai suka zaɓi Mallam Sulaimanu, kuma babu wanda yayi jayayya bisa haka domin dukkansu sun shaida yadda Allah Ta'ala ya kaskantar da ɗaukakakkun masu mulki, ya kuma ɗaukakasu da sarautarsu.
To amma dai, wata ruwayar baka tazo akan cewa mallam sulaimanu ya kasance shine ke yiwa masu jihadi limancin Sallah, don haka bisa umarnin shehu Usmanu da yace "limamin ku a sallah shine shugabanku" sai aka naɗa shi ya zamo sarki, yayin da sauran malumma suka zamo 'yan kwamitin zartaswa wanda sarki bashi da ikon yanke wani abu sai da sahalewar su.
Saboda haka, an bayyana cewar anyi zaman lafiya a zamanin mulkin sarkin kano sulaimanu.
A zamanin, sarautar kano ta zamo ta daban, domin akwai mukamai da abubuwa da yawa na al'ada da fulanin suka ajiye tun bayan hawansu madafun ikon kano. Inda yaki ya fara shine shekara ta 1807 inda akace Sarki Alwali ya dawo daga zariya, ya shiga garin burum-burum, yana kulla yadda zasu kawowa kano hari domin ɗaukar fansa.
Ai kuwa sai Sarki Sulaimanu ya tura Mallam Bakatsine izuwa garin da runduna gagaruma. Ai kuwa suka je suka farwa garin da yaki. Akayi fafatawa gagaruma, amma dai cikin ikon Allah suka samu nasarar kone garin da halaka sarki Alwali.

No comments:
Post a Comment