TARIHI: YADDA JIHADIN FULANI YA KASANCE A KANO (1803-4)
Kashi na shidda.
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
SAMUN TAIMAKON SARKI ALWALI DAGA DAURA, DA KUMA CINYE GARIN DANYAYA.
Sarkin Daura na lokacin (Sarkin Gwari Abdu) ya kawowa dakarun Alwali ɗauki. Kashe gari aka sake gwabza faɗa da rundunar masu jihadi.
A wanna rana masu jihadi sunyi matukar jigata saboda wahalar yaki, ga yunwa dake damunsu. Don haka basu samu nasara a yakin ba.
Amma bayan yaki ya k'are da dare, sai malumma shugabanni ga masu jihadi suka taru domin tattauna mafita garesu.
A wannan lokaci, dukkansu sun gamsu da cewar kamata yayi su bar wannan wuri izuwa ga Mallam Bakatsine wanda ya aiko musu da sakon albishir na cewa ya kame iko da garin Gaya.
To sai kuma aka shiga shawarar tayaya za'a tafi can ɗin?
Wasu suka ce a tafi da dare, Mallam Abdurrahman yace ai idan aka tafi da dare za'ace guduwa sukayi. Sai Mallam Jibrila yace a bari da safe su sake yakar wannan runduna, in yaso sai Allah yayi hukunci a tsakanin k'arya da gaskiya.
Shikenan kuwa sai kowa ya gamsu da hakan.
Da gari ya waye sai aka sake shiga yaki. Aka buga yaki mai tsanani, har sai da masu jihadi suka soma cin galaba akan rundunar Sarki Alwali.
Koda Sarkin yaga haka, sai yayi saurin janye rundunarsa ya shige cikin garin Danyaya yasa aka ɓame kofar gari.
Masu jihadi suka bisu a baya har bayan gari. Daga nan sai suka zauna suna jira.
Ba tare da wata jimawa ba sai mutan garin Danyaya da dakarun Alwali suka soma fitowa waje, da alamar za'a sake yin faɗa kenan.
Da suka fito sai suka jeru suna fuskantar rundunar masu jihadi, wasu cikinsu suka ɗaga murya suna cewa kun kawo kanku ga mahalaka.
Nan take kuwa matan dake cikin masu jihadi suka ɓarke da kabbara, suka amsa musu da cewa "Kwarin guiwarku abune mai kyau". Daga nan fa sai faɗa ya ɓarke.
Aka shafe dare dukkansa ana fafatawa, daga bisani dai masu jihadi sukayi galaba, inda suka kashe mazaje da yawa daga rundunar sarki Alwali, suka kone ganuwa da rushe wani yanki, suka shige garin tare dayi masa kawanya, gashi kuma Sarki Alwali yana cikinsa.
Daga baya dai sai Malumma Shugabannin masu jihadi sukayi shawara, sukace a kyale sarki Alwali ya fita daga garin ba tare da wani abu ya same shiba tunda yaga ikon Allah da idonsa.
Sai kuwa aka buɗe masa kofar gari, ya fice da wata tawaga 'yar kaɗan tunda sauran duk sun tsere, wasu kuma an karkashe su.
A tare dashi a wannan lokaci akwai 'ya'yansa biyu, chiroma wanda daga baya ya tuba har sarki bafullani na farko a kano watau sulaimanu ya naɗashi mai unguwar kutumbawa, sai kuma ɗanuwansa Madawaki. Ragowar kuma bayin sarki ne irinsu Sarkin yara, sarkin shanu da wasunsu.
SAKON SULHU DAGA ALWALI DA GUDUNSA IZUWA ZARIA
A farkon sha'aban sai masu jihadi suka tafi ɓagwai, sannan sukayi Damargu.
A ɓagwai sun tarar mutan garin sun karya alkawari, sun sauka daga kan abinda suka ɗorasu akai, don haka sai suka farma garin, suka koresu. Daga nan suka tafi Tofa, sai suka wuce Gogori, suka isa Farin Ruwa, sai suka karasa Tambari, sannan suka tsallaka yankin katsina inda suka sauka a Kurkujan.
Acan ne suka haɗu da Mallam Ummaru Dallaje (wanda ya zamo sarkin katsina a shekarar 1816) da Mallam Ishaqa (wanda ya zamo sarkin Daura a shekarar 1805). Suka shafe watanni huɗu suna gwabza yaki da sadaukan daular katsina, amma daga bisani yunwa da gajiya yayi musu yawa, sai suka yanke shawarar komowa kano.
Suka shigo kano ta Taɓanni dake tsohuwar gundumar Gwarzo, sannan suka wuce farin ruwa, suka shiga Gogori, suka biya ta ɓagwai sannan suka nufi bichi.
Daga Bichi sai sukayi Damargu, sannan suka karasa Tomas suka sauka. Daganan kuma sai suka tura wata runduna bisa jagorancin Mallam Jibrila izuwa garin Fagay, suka yaki garin tare da kone shi, sannan suka kamo bayi.
Sai dai ya kamata. Sani, a wannan lokaci, sarki Alwali a takure yake matuka, domin birnin kano ne kaɗai a hannunsa, babu kuma inda yake iya zuwa.
Sarki Alwali ya aiko wasu malumma mazauna Kano da takardar neman sulhu ga rundunar masu jihadi. Malumman sune :Mallam Kabara, Mallam Gabto, Dan gwauranduma Sumailu, Mallam Jabbo Alfulati, da Mallam Goja.
A cikin takardar, ya bayyana cewar a shirye yake ya riski masu jihadi kuma yayi jihadi tare dasu koda kuwa zaiyi tafiya da kafa ne. yace kuma zai bi dukkan umarninsu.
Amma sai masu jihadi suka yi watsi da bukatarsa, suka ce ai tun da fari suka umarceshi yayi haka, amma maimakon yaji maganarsu sai ya shiga haɗa rundunar mayaka wadda zata halaka su, sai yanzu da Allah ya kunyatar dashi zaice yana son ya shigo cikinsu.
A karshe suka shaida masa cewar zasu kawo farmakin kwace kano ranar sha biyu ga watan Rabiul Awwal.
Ranar wata lahadi da dare sarki Alwali ya sulale izuwa Rano bayan yaji sakon masu jihadi, inda ya ɗan kwana biyu sannan ya haura Zaria.
Ranar wata litinin kuwa da dare masu jihadi suka shiga kano fare da kame iko da ita.
A bisa wata ruwayar ance kwanaki arba'in da ficewar sarki Alwali daga kano sukuma suka shiga, amma wasu sunce kwanakin arbain da ɗaya ne ba arbain ba.
Tun daga nan ne kuma suka kasance a cikin kano tare da mallake sassanta duka.
Wannan kuma shine tarihin yadda aka kwace kano da yaki a jihadin fulani.
Abu nagaba bai wuce yadda Mallam Bakatsine ya halaka Sarki Alwali ba a garin burum-burum, da kuma yadda mulkin sarakunan fulani ya kasance, haɗe da kalubalen yakin da suka fuskanta kuma.

No comments:
Post a Comment