TARIHI: YADDA JIHADIN FULANI YA KASANCE A KANO (1803-4)
Kashi na biyar.
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
A baya, kafin muji yadda jihadi ya kasance a gabashin kano, mun dakata ne a inda masu jihadi suka tashi izuwa yankin Tofa da Bichi. To Daga nan sai suka wuce wani gari mai suna Magami inda yake karkashin gundumar Sumaila, sannan suka riski Hawwade, sai kuma suka koma yankin da suka baro suka sauka a garin Gora na Bebeji.
A garin Gora ne rashin fahimta da saɓani ya soma shigowa a cikin masu jihadi, har tawaga taso ta rabu biyu.
Dalilin hakan kuwa shine, Mallam Abdurrahman yace sai ayi gabashi a haɗu da Mallam Bakatsine a kara masa karfi a jihadin da yakeyi, shikuma Mallam Jamo yace sam ba za'ai haka ba, domin idan suka tattara karfi wuri ɗaya suka kyale sauran wurare, to akwai yiwuwar bisa tallafin sarkin katsina dana Damagaran, za'a iya haɗa gagarumar rundunar da zata murtsuke su.
A karshe, bisa taimakon Allah sai suka cimma matsaya, ska nufi arewa.
HADUWA DA FARIN TAFKI, BICHI DA AGUNBULO
Da masu jihadi suka bar garin Gora, sai suka riski garin Farin Tafki, daga nan sai suka wuce Tofa inda suka tarar da wata runduna tana saurarensu don a gwabza faɗa, aikuwa koda sukayi arba da juna sai yaki ya ɓarke. Sai dai cikin ikon Allah, masu jihadi sun samu nasarar fatattakar wannan runduna.
A wannan yakin, masu jihadi da dama suka samu ganimar dawakai da kayan faɗa, sannan da dawakan kuma sukai amfani wajen tsallaka tafkin watari suka nufi garin Tatarawa. Bayan sun ɗan jima anan sai suka tashi sukayi Damargu dake gundumar Bichi.
A garin Damargu ne mutanen garin Bichi, Tofa dana Farin Tafki suka kawowa masu jihadi ziyarar mika wuya da sallamawa. Don haka ba'a gwabza yakin jihadi da mutan garuruwan ba.
Bayan an kammala, sai masu jihadi suka nufi kauyen marke suka sauka, sai kuma suka tashi tare da sake komowa kauyen Tatarawa inda sukayi kichiɓus da sadaukan sarki Alwali karkashin ikon gawurtaccen sadaukin nan Agumbulo.
Shi Agumbulo buzu ne, sarkin kano Alwali ne ya gayyato shi wannan rikici tare da bashi dawakai dubu huɗu da nufin yazo ya fatattaki masu jihadi ya kone gidajensu.
Sa'ar da Agumbulo ya iso garin Tatarawa da rundunarsa, sai ya tarar masu jihadi sun bar garin amma akwai gidajen su da suka gina, sai kuwa ya hau gidajen da konewa. Daga nan yabi bayan rundunar masu jihadi.
Kwatsam, sai masu jihadi sukayi kichiɓus da wannan runduna ta Agumbulo. Kafin kace haka sun auka musu da yaki. Nan take kazamin faɗa ya sake rinchaɓewa.
Tabbas, ance a wannan lokaci Allah ne ya nuna ikonsa, ya tsallakar da masu jihadi, musamman bisa tallafin da suka samu daga wata rundunar fulani sulluɓawa da suka iso wurin faɗan daga baya, shine kuma har suka samu damar halaka sadauki Agumbulo tare da watsa rundunarsa, amma fa suma sun haɗu da rashin nasara gagaruma.
Kwana ɗaya da wannan faɗa masu jihadi suka bar wurin, inda suka nufi bakin tafkin Tomas na gundumar Dambatta. A wannan lokacin ne kuma rundunar sarki Alwali ta sake dawowa Tatarawa don a gwabza wani faɗan, amma sai suka tarar masu jihadi sun nufi Tomas, don haka sai suma suka bi bayansu.
Da rundunar jaruman sarki Alwali ta riski Tomas, sukayi gaba da gaba da rundunar masu jihadi, sai suka juya ba tare da an gwabza yaki ba, suka rabu biyu tare da yada zanguna a kauyukan Jalli dana Maɗachi bisa umarnin Sarki Alwali wanda a lokacin yana cikin birnun kano.
Anan suka zauna kullum suna kamen bayi da fursunoni daga mazauna yankunan.
KISAN MALLAM DAN GABUWA
A sa'arda rundunar da Sarki Alwali ya turo tayi nufin yaki, sai suka sare dukkanin bishiyoyin dake kewayensu, wuri ya zamo fili thabiyr .
Bayan sun gama, sai suka tura wasu tsiraru domin kaiwa masu jihadi farmaki. Da isar au kuwa sai aka soma fafatawa, amma jin kaɗan da haka sai suka juyo da gudu, inda masu jihadi kuwa suka biyosu abaya suma da gudu, ashe ramin mugunta aka kullawa masu jihadi basu sani ba.
Masu jihadi basu fahimci haka ba sai da suka gansu tsulundum cikin gagarumar runduna an hausu da sara da suka, ai kuwa a wannn rana an kashe da yawa daga masu jihadi.
Amma fa kashe gari, sai masu jihadi suka sake dawowa, suka hau sadaukan nan da kisa. Yaki sabo ya sake ɓallewa, kowacce runduna ta himmatu bisa samun nasara akan abokiyar bugawarta.
Daga karshe, bayan an shafe wuni ana gwabzawa, masu jihadi suka samu nasarar karya lagon wannan runduna, inda suka tarwatsa su tare da kone mazaunin su dake Jalli da Maɗachi.
Sarki Alwali yaji matsanancin haushi bisa wannan asarar yaki data auku. Don haka ya yanke shawarar fitowa da kansa domin a gwabza, inyaso duk mai yiwuwa ta yiwu.
A tare da sarki Alwali akwai sadaukai ɗari bakwai masu sanye da sulken bakin karfe. Haka suka baro kano izuwa inda masu jihadi suka yada zango anan Tomas, amma da sukai gaba-da-gaba, sai Sarki Alwali ya waske, ya shige garin Dawakin Tofa, inda ya kone garin tare da kashe dukkan mazajensu ciki harda alkalan garin bisa ƙlaifin chaffar da yaji sun kaiwa masu jihadi.
A lokacin kuma, sai masu jihadi suka bar inda suke izuwa wani gari mai suna 'Bak'in Ruwa', a cikinsu kuwa har da wasu shahararrun sadaukai hausawa da ake kira Dantunku da Maiduniya.
Da Sarki Alwali yaji sun tashi, sai shima ya tashi izuwa kusa dasu, ya sauka a wani gari mai suna 'Danyaya', ance harma masu jihadi na jiyo sautin tambura da gangi da ake kaɗawa sarki Alwali daga inda suke.
A tarihin yakin jihadin kano, ance saida rundunar masu jihadi suka gwabza yaki har sau 93 a tsawon watanni huɗu, amma a wannan karon ne kurum sarki Alwali ya fito cikin runduna za'a gwabza dashi a yaki.
Sarki Alwali ne ya jagoranci wannan yak'i da kansa wanda suka farwa masu jihadi a ranar wata litinin da yamma, suka kone gidaje da dawakan masu jihadi, anan nema Mal Dangabuwa ya rasa ransa, amma cikin ikon Allah kafin ɓullowar alfijir sai da masu jihadi sukayi galaba akan rundunar Sarki Alwali, tilas ya juya da baya da gudu.
Bayan wani lokaci sai suka sake dawowa wurin, a tsammaninsu zasu tarar masu jihadi sun bar wurin faɗan, amma sai suka tarar dasu cirko-cirko kamar masu jiran wani abu, ga gawarwaki nan a zube fululu..
Wasu daga rundunar sarki Alwali suka ɗaga murya suna tambayar masu jihadi cewa "ashe har yanzu kuna wannan wuri?" Sai kuwa masu jihadi suka amsa musu da cewa "eh munanan, kuma anan zamu kasance"
Sai kawai sarki Alwali ya umarci a juya da baya, yana mai cewa koda anyi faɗa babu nasara a wannan lokaci..

No comments:
Post a Comment