HIKAYAR KARSHEN MAI KWADAYI
Watarana, wani Dila na tafiya cikin dokar daji, sai yayi arba da wasu Raguna suna fada a tsakanin su kuma duk sunyiwa junansu jina-jina, sai jinni keta kwarara daga kahunhunansu.
Koda wannan mayunwacin dila yaga haka, sai ya matsa kusa dasu yana mai lasar jinin dake kwarorowa daga kawunan wadannan raguna ba tare day a kula da fadan nasu ba.
Raguna nata fada, dila na kara himmatuwa wajen yin koto da jininsu, har yakai ga yana kai harshensa kan kahunhunansu yana lashe jinin dake fitowa tun kafin ya gangaro kasa.
Duk abin nan da akeyi, akan idon wani kare akeyi. Sai wannan kare yake tunanin don me dila yake haka? Shin baya tsoron kwalamarsa zata iya sanyawa ya tsinci kansa a halaka idan wadannan ragunan sukayi masa karo?
Ai kuwa bai gama wannan tunani ba, sai akayi rashin sa’a dila yakai harshensa dai-dai kahon daya daga cikin ragunan yana lashe jinni, sai kuma daya ragon ya kawo wawan gware.. kafin kace haka ya hada da kan wannan dila. Ya zamo sun gwarashi a tsakiya kenan. Nan take kan ya lotse, ya fadi kasa matacce.
Darussa
*Kada kwalama da kwadayi ya gusar da tunanin ka har kasa kanka a wani abu wanda zai iya kaika ga halaka ba tare da yin tunanin hatsarin da zai iya biyowa ba.
*Duk inda kaga ana rashin jituwa, kokarin sulhu ya kamata kayi. Idan kuwa kakiyin haka saboda kana amfanuwa da wannan rigima, to da sannu rigimar zata shefeka kachokan.

No comments:
Post a Comment