HIKAYAR ATTAJIRIN SARKI MANSA MUSA
Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978
An taba yin wani Sarki a Masarautar Manden Niani dake cikin Kasar Mali a yanzu, mai suna MANSA MUSA (Musa Keita). Wannan sarki ya faro mulkin sane a garin Niani, a qarni na goma sha uku. Kafar sadarwar yanar gizo ta http:http://www.celebritynetworth.com, ta bayyana Mansa Musa a matsayin attajiri na daya a fadin duniya, wanda ba'a taba samun kamar saba, domin ta kimanta cewa arzikin sa ya tasamma darajar dala biliyan dari hudu (Attajiri na daya a duniya Bill Gate yana da arzikin dala biliyan 79 ne kachal).
HAWAN MULKIN MANSA MUSA
Mansa Musa ya sami damar hayewa kan karagar Mulkin garin niani ba tare da zubar da jini ba. Domin kuwa a lokacin da sarki Abubakar keita II yayi niyyar zuwa kasar saudiyya aikin Hajji, sai ya danqa Amanar gari a hannun wazirin sa Mansa Musa. Ance bayan Sarki Abubakar ya kammala aikin Hajjin sa sai kuma ya shagaltu da son ganin Qarshen Tekun maliya, don haka sai ya bige da binta, a haka har aka daina jin duriyar sa. Daga nan ne kuma sai mansa musa ya zamo cikakken sarki mai iko na garin Niani.
Har ma wani masanin tarihi dan qasar misra mai suna Al-Umari ya ruwaito Mansa Musa yana cewa "Sarkin dana gada bai amince da cewa Sanin qarshen tekun Maliya ba abune mai yiwuwa ba, don haka bashi da wani buri sama da Wanna. Shine ma yasa aka shirya masa jiragen ruwa guda dari biyu, wasu jiragen aka cika su da sadaukai, wasu kuma aka cikasu da ruwa da abincin dazai ishesu na tsawon shekaru da kuma gwala-gwalai. Sannan ya umarci Jagoran jiragen da cewa suyi ta tafiya babu juyowa har sai sun taradda karshen tekun Maliya, ko kuma har lokacin da ruwan su da abin bukatarsu zai qare. A haka aka daina jin duriyar su har tsawon lokaci, a qarshe jirgi daya ne kurum ne ya dawo. Da Sarki ya tambayi jagoran jirgin inda ragowar tawaga take, sai yake cewa ya shugaba na, ka sani cewa jirginmu ne a baya, kuma munyi tafiya doguwa a cikin teku, har sai da muka tarar da wani doro na ruwa, wanda duk jirage suka shige cikinsa suka nutse, namu ne kadai mukayi nasarar juyowa da baya ba tare da mun nitse ba. Amman duk da haka sai Sarki abubakar yaqi amincewa, a inda ya sake shirya jiragen ruwa guda dubu biyu, ya shiga ciki da mutanen sa, jirage dubu kuma aka tamfaye su da abinci da ruwa da tulin dukiya, sannan ya aiko min da wasiyyar rikon gari, shikuma ya umarci tafiya akan tekun maliya don ganin qarshenta. Abinda har yanzu bamu sake jin duriyar su ba"
Bayan mulki ya tabbatu a hannun Mansa musa, sai ya dukufa wajen fadada kafofin samun arziki na gwamnatin sa. A wancan lokaci, Gishiri da zinare sune manyan abubuwan da suke taqama dashi, sune kuma abubuwan daya nema haiqan.
Mansa musa Mutum ne mai son addini da Ilimomi, don haka da hawan mulkin sa ya fara yiwa musulunci hidima, ya fara kokarin tara Masana kuma a gwamnatinsa. Ance shine sarkin da duk Jumu'a yake sanyawa a gina masallaci, don haka kafin mutuwar sa sai daya gina masallatai masu dumbin yawa.
A shekarar 1324 ne sarkin Niani, mai martaba Mansa Musa yayi haramar tafiya aikin Hajji, lamarin daya ajjiye tarihi a daukacin duniya. A wannan lokacin, sai daya shirya runduna gagaruma mai dauke da sadaukai dubu sittin aciki har da bayi dubu goma sha biyu kowannen su yana bisa doki, yana riqe kuma da sunduqai na zinare guda hudu, sannan aka shirya rakuma guda dari biyu, aka dora mangaloli masu cike da sunduqan gwal daga guda talatin zuwa dari biyar.
Akan hanyar sa kuma, duk garin da yaje bashi da abin kyauta sai gwala-gwalai. Sai daya raba gwala-gwalai kamar yayi babu adadi. Wannan ne yasa sai da gwal ya zamo abin banza mara kadari a lokacin saboda yawaitar sa a wannan yanki.
Ance da sarki Mansa Musa ya fahimci yadda lamarin ya baci, akan hanyar sa ta dawowa Niani bayan ya kammala aikin Hajji ya biya ta birnin Cairo na Misra, ya hadu da sarkin garin sultan Al-Nasir Muhammad a watan yulin shekarar 1324, sannan ya nemi rance Gwal daga attajiran garin akan farashi mafi daraja, wannan yasa duk wani mai gwal ya rinqa rige-rigen miqa nashi ga Mansa Musa, kafin wani lokaci sai gashi Gwal yayi qaranci, farashin sa kuma ya hau. Ance har abada ba za'a mance dashi ba akan haka, domin shine mutum daya tilo da yadauki matakin gyara tattalin arzikin wani yanki na duniya kuma yaci nasara cikin lokaci qanqane. #SadiqTukurGwarzo
Mansa Musa na kusa da isa garin sane aka labarta masa cewa jagoran sojojin sa mai suna Sagmandir, ya samu nasarar cinye garin Gao na daular songhai da yaqi, don haka saboda murna sai ya biya ta garin, anan ne kuma ya samu tarba gagaruma, mutan garin sukayi ganganko cikin annushuwa da murnar zuwansa, shine ma aka kawo masa 'ya'yan Sarkin garin guda biyu a matsayin fursunan yaqi, daga baya ya tafi niani dasu yasa aka koyar dasu Ilimi.
A shekarar 1330 ne kuma akace sarki Mansa Musa ya cinye garin Tumbuktu da yaki, shine fa ya hade garin Gao da Tumbuktu da masarautarsa. Yasa aka gina ganuwa gagaruma ta dutse aka zagaye garin Tumbuktu, aka kuma jibge tulin dakaru domin samar da tsaro.
Tarihi ya tabbatar da cewa alokacin mulkin Mansa Musa ne Tumbuktu takai matsayin da takai. Domin sai da Tumbuktu ta zamo cibiyar kasuwanci da al'adu ta afirka inda ake zuwa daga sassan duniya domin yin kasuwanci. Sai da kuma garin ya zamo daya daga cikin Kasaitattun birane na duniya a wancan lokacin, domin Sarki Mansa aikawa yayi Cairo da Andaluz aka zo masa da magina, ya basu kwangilar yin hamshaqan gine-gine na zamani a garin. A ciki har da ginin wani Masallaci mai tarihi wanda akewa laqabi da Masallacin djinguerber'. Sannan shine ya qarfafa jami'ar sankore, ya gina wasu jami'o'in a Djenne da Segou, ya kuma wadata su da manyan malamai masu karantar da iliman Falsafa, kimiyya, lissafi, likitanci, sararin samaniya da dai sauran su. #SadiqTukurGwarzo
Ance Mansa Musa ya shafe shekaru ashirin da biyar akan gadon sarauta. Wasu sunce ya mutu ne a shekara ta 1332, Ibn khaldun kuwa yayi musu akan haka, inda yace Mansa musa yana raye har zuwa shekarar 1337 lokacin da wani Sarki ya kame garin Tlemcen dake qasar Algeria a halin yanzu, domin sai da Mansa Musa ya tura jakadan sa ga sarkin don taya shi murnar nasarar daya samu.
Masanin tarihi kuwa Ibn Batuta wanda ya rayu shekaru kusan saba'in bayan mutuwar Mansa, ya bada labarin girman masarautar Mansan, inda yace masarautar nada tsananin fadi, ta yadda sai mutum ya shafe tafiyar watanni hudu daga farkonta ta yamma sannan zai iya isa qarshenta a kudu.
Bayan Rasuwar Mansa Musa, dansa Magham Musa ne ya gajeshi.
Wannan shine taqaitaccen tarihin babban attajiri, wanda duniya zata dade tana tunawa dashi, watau Mansa Musa.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo.

No comments:
Post a Comment