Saturday, 9 December 2017

HIKAYA: WATA RANA A KASAR HAUSA 2

Ishaqa ya kura mata ido, saboda ya tsinci kansa ne a wani yanayi wanda har yanzu bai san sunan saba. Ya gyada kai, alamar ya amince. Ita kuma sai ta cigaba da cewa "Da fari dai sunana Randiyya, mahaifina attajiri ne babba a birnin kano, wanda babu attajiri irinsa. Ni kuma nice kadai 'yarsa, mahaifiyata ta rasu tun ina qarama.
Rannan sai gaba ta hadosu da Sarki a dalilin haraji. Sarkin yaqi ke zuwa karbar haraji wajen mahaifina. Shi kuma kamar yadda ya saba, bayan ya biya harajin, yana yiwa Sarkin yaki alheri mai yawa. To lokacin da yazo sai akayi rashin sa'a ya hangoni, ai kuwa sai ya kamu daso na. Yace idan har mahaifina zai yarda ya aura masa ni, to ya bar qara biyan haraji, kuma sai yaga bayan makiyansa duka. Shi kuma mahaifina yace gaskiya lokacin dazai aurad dani bai karasa ba, kuma zumunci yakeso ya hada ni da dan- dan uwansa.
Daga nan fa Ran sarkin yaqi ya baci, yayi rantsuwa da cewa sai ya bakantawa mahaifina, kuma ko bayaso sai ya aureni. Daga nan sai ya tafi ga sarki, ya shirya qarairayi wadda ta sanya Sarki yaji ya tsani mahaifina.
Sarki ya aiko gidan mu da cewa baya son zaman mu a garinsa. Don haka ya bamu kwana daya, mu hanzarta bar masa gari.
Cikin tashin hankali mahaifina ya nufi fada, yayi juyin duniyar nan, sarki yace sam bazai saurareshi ba, dole ne ya bar gari. Tilas mahaifina ya shiga hada kayan sa don fita daga garin.
Abin bakin cikin ma shine, sarki ya hana kowa daga mutanen garin amsar ajiya ko tsaron wani abu na daga dukiyar mahaifina. Ya kuma bada shelar cewa idan kwana daya ta cika, kowa na iya zuwa gidanmu duk abinda ya samu ya zama ganima.
Mahaifina ya hada abinda zai iya dauka bisa dawakai, ba shiri ya sa ni a gaba da wasu amintattun bayinsa muka bar garin muna kuka. Fitar mu keda wuya sai muka mufi wani gari Marke inda Sarkin garin aboki ne ga mahaifina.
Bayan kwana biyu, sarkin yaqi ya qara zuga sarki akan cewa dole abi bayan mahaifina a kamo shi a daure, idan ba haka ba zai tara sadaukai yazo daukar fansa ga sarki. Don haka sarki ya baiwa Sarkin yaqi izinin aiwatar da wannan aiki, da nudin idan har sarkin Marke yayi turjiya, ya qone garin duka da abinda ke cikinsa.
Hakan kuwa akayi, Sarkin Marke yace bazai sallama muba sai dai ayi duk wanda za'ayi. Sadaukan sarkin yaqi suka rufarwa garin da fada, suka shiga kisa ba babba ba yaro, suna kone gidaje. A karshe sarkin Marke ya gudu mu kuma suka samu nasarar kama mu gami da komar damu kano.
Ala dole mahaifina yace ya gamsu ayi aurena da sarkin yaqi domin a zauna lafiya. Sarki yace to zai yafe masa laifin sa idan har akayi auren lafiya, amma idan wani abu mummuna ya auku, to tilas sai ya halaka shi a gaban dumbin jama'a.
Daga baya mahaifina ya yanke shawarar daya hada jinin sa da azzalumi irin sarkin yaqi, gara ya mutu. Don haka ya nemi wani bafade wanda ya shirya sace ni tare da shigar dani tawagar ku. Da ranar daurin auren kuma tazo sarki bai ganni ba, shine yasa aka sare kan mahaifina.
Ta qare da cewa " a yanzu haka na miqa wuya a gareka, ina rokon taimakon ka. Bani da wani gata idan ba kai ba. Ka taimake ni na isa Damagaran, akwai dan uwan mahaifina da yake fatauci acan, wajensa nake son komawa.
Ishaqa yayi ajiyar zuciya yana mai tausawa Kyakkywa Randiyya. Ya kalle ta cike da jimami, yace "Hakika na tausaya halin da kika shiga. Kuma ina sanar miki da cewa a shirye nake na taimake ki dom ki tsira daga sharrin wadannan azzalumai. Amma fa ki sani, wannan lamri yana da matuqar hatsari. Kinga dai ni yaron gida ne, wakilci nakeyi, don haka nake kaffa-kaffa da rayukan wadanda nake jagoranta gami da dukiyoyin su. A yanzu kuma muna cikin wani lokaci, sarakunan mu basu da tausayi. Akan ki yaki zai iya barkewa tsakanin damagaran da kano, duk da daman nasan sukan fafata jefi-jefi.. Gashi kuma labari baya buya, ina tsoron kada aje a sanar da Sarkin kano cewa kina cikin tawagar mu, nasan tabbas sai ya biyo bayan mu.."
"Ni dai ka zama gatana" Randiya ta fada. "Allah shine gatan mu Randiyya.." inji Ishaqa. Sai ya qara da cewa " Amma ki kwantar da hankalinki, da yardar mai duka zaki kubuta" itama Randiyya ta nemi sanin tarihinsa amma yace kada ta damu, zai sanar da ita.
Sannu a hankali tawaga na cigaba da tafiya tana kusantar Birnin damagaran,
Shaquwa ta fara aukuwa tsakanin Ishaqa da Randiyya, har ya kasance kusan koda wanne lokaci suna tare da juna. Ayi raha ayi firar duniya. Wannan ne ya fara daukewa Randiyya bacin ran da take ciki, hankalinta ya fara kwanciya.
Wata rana suna tare, sai Randiyya take cewa "Ya shugaba na, naga kamar kai ba bahaushe bane, wataqila baka san rike zumunta ta hausawa ba.. Idan ka shirya, zan baka wani labari"
Ishaqa yayi murmushi, yace "na gane wayon ki ay, so kikeyi ki bugi ciki na na baki tarihi na, nikuma nace miki lokaci baiyi ba, kawai dai idan kina da labari mai dadi kibani"
Randiyya ta kyalkyale da dariya tana mai rufe fuskarta don kunya, sannan ta soma bashi labarin da cewa " A wani gari, anyi wasu abokan juna su biyu, wadanda suka amince da juna. Sai suka yanke shawar tafiya wani gari neman kudi. Akayi sa'a kuwa, garin da sukaje suka sami 'yan kudinsu, har ma kowannen su yayi aure.
Rannan sai suka ce ai kuwa ya kamata muje qarinmu da matayen mu domin suga iyayen mu. Ai kuwa sai suka yi shiri suka kama hanya. Tinkis tinkis suna tafiya, sai dare yayi musu cikin wani daji. Sai daya abokin yace ai kuwa ya kamata su tsaya ana shikuma ya nemo musu karyo musu itacen da zasu kunna wuta, in yaso idan ya samu 'ya'yan itatuwa ma zai hado musu dashi.
Tafiyar sa keda wuya sai ga Zaki ya qaraso wurin, yana gurnani, matan nan duk suka rude, shikuwa namijin yayi ta maza ya zare wuqa ya durfafi zaki. Kaca-kaca har ya samu nasarar halaka zaki.
Yana cikin hutawa sai yajiwo tafiyar abokin nasa yana dawowa, sai kuwa yace da matan su kwanta kamar sun mutushikuma ya tsayar da zakin kamar mai rai, domin ganin yadda abokin zaiyi.
Isar abokin keda wuya yayi kuwa, yace aikuwa rayuwa ta bata da amfani, tilas na rufarwa zakin nan inyaso ya kashe ni kamar yadda ya kashe min 'yanuwa. Da fadar haka sai ya rarumi zaki, sai dai ga mamakinsa sai ya tarar da zaki a mace, anan ne abokin da matan suka tashi suna masa dariya gami da jinjina masa. Kaji kadan daga amincin hausawa"
Ishaqa yayi murmushi. Yace "wataqila ma na rigaki sanin wannan labarin. Kinsan mu matafiya ne, muna bada kyauta don a bamu labari, wannan labarin kuwa ya shahara a qasar hausa" Daga nan dai suka ci gaba da firar su ta arziki.
A wani lokaci suna cikin tafiya, sai suka jiwo ihu da hargowa. Daga can kuma suka ga hayaqi na tashi, ashe mahara ne masu dibar bayi suka tasamma wani dan qauye.
Akan idon su ishaqa maharan nan suka rinqa rashin mutumci, su kashe na kashewa, su kama na kamawa a matsayin bayi. Mata da yara kuwa me sukeyi idan ba kuka ba. Gashi kuma duk sun cinnawa qauyen wuta.
Ishaqa ya matsa da dokinsa kusa da dokin Randiyya,ya saitu da ita sannan ba ya fara magana da cewa "Tarihina ya soma ne da misalin wannan abinda kike gani. An bani labarin cewa tun ina yaro akayiwa qauyen mu irin wannan zaluncin, a haka aka daukeni daga wurin mahaifana tare da siyar dani bawa ga Mehmet. Don haka a hannun sa na girma, a yanzu haka na mance siffar garin mu data mahaifa na, ban san komi ba kuma sai bauta..
Daga Sadiq Tukur Gwarzo 08060869978


No comments:

Post a Comment