HIKAYAR HAUSA: WATARANA A KASAR HAUSA!
Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
Shekaru daruruwa da suka gabata, tarihi ya nuna cewa qasar hausa na karbar baquncin fararen fata wadanda akasarin su Larabawa ne, da kuma mutanen hadaddiyar daular Ottoman, wadanda ake kira da Turkawa, masu zuwa siye da siyarwa.
A wani lokaci irin haka, anyi wani shahararren Falke wanda yake tasowa daga Birnin Ankara izuwa kasashen hausa, sunan sa Mehmet. Sana'ar sa itace fatauci, don haka a wannan lokacin Mehmet yana zuwa kasashen hausa ya siyarwa da sarakuna kayan sawa na alfarma, kayan fada da kayyakin Alatu. Shi kuma yana siyen bayi daga wurin su ya tafi dasu kasashen larabawa ya siyar.
Mehmet yana da wani da matashi mai suna Abdulkarem, wanda yake matukar kauna. Har ma shi yake dorawa akan duk wani abu na dukiyar sa. Rannan qaddara Abdulkarem ya kamu da wata cuta, ashe cutar ajali ce, babu jimawa rai yayi halinsa.
Hakika, mutuwar Abdulkarem tayi matukar dugunzuma Mahmet, amma kasancewar sa musulmi, sai ya dangana ga Sarki Allah. Daga nan kuma sai ya jawo wani bawa mai suna Ishaqa wanda yake amini ne na qut da qut ga marigayi Abdulkarem ya maishe shi tamkar da. Duk wani abu da Abdulkarem yake yi masa, sai Ishaqa ya zamo yana kamantawa.
A Wata shekara, Mehmet kamar yadda ya saba, ya keto ta Libiya daga Ankara, ya sauka a Damagaran, sai dai jikin sa na masa nauyi, wannan yasa yaji tsoron qarasawa cikin qasar hausa, ya yanke shawarar zai tura Ishaqa ya wakilce shi a kasuwancin da suka saba, shi kuma zai huta anan damagaran, in yaso idan yaji dama-dama sai ya gangara Kukawa dake Masarautar borno ya taba kasuwanci ya dawo damagaran ya jira su.
Haka kuwa akayi, Ishaqa ya zamo jagora, ya taso da tawaga suka biyo ta qasar sakkwato, yana tare da turkawa abokanan mehmet, da dakaru masu yi musu rakiya da kariya, wadanda suke dauke da bindigu, takubba da sauran kayan fada don gudun Mahara da 'yan fashi. Duk da dai suna da kyakkyawar alaqa da sarakunan qasar hausa, amma 'yan ta'adda na iya yi musu kwanta-kwanta su karbe dukiyoyin su.
A kwana a tashi, Ishaqa da tawagar sa ta Iso birnin Kano. Daman bisa al'adar su sukan tsaya a babban gari suci kasuwa su kuma baiwa sarkin garin kyauta. Amma da yake Mehmet yana da babbar alaqa da Sarkin kano na lokacin, kyautar sa tana zamowa ta musamman, kuma sau tari, daga kano kukawa suke qarasawa, amma da yake sun raba tafiyar da mai gidansa, wannan na nuna cewa a bana iya kacin tafiyar su Kano.
Da isar su birnin kano, suka aika wani baran su domin yayi musu iso. Babu jimawa kuwa akace Sarki na maraba dasu, don haka suka dunguma izuwa cikin gari.
Tun daga kofar gari Ishaqa da mutanen sa suka lura da sauyi a garin. Gashi dai an qawata gari kamar ana wani qwarya-qwaryan biki, amma kuma gidaje da rumfunan kasuwa duk a rufe, ba kuma a ganin mutane a garin. A haka har suka isa fada.
Fadar ce suka gani cike da mutane. Ashe sarkin garin ne ya tara al'ummar sa duka yana musu jawabi.
Isar su keda wuya aka basu wuri a fadar, aka kuma shaida musu cewar su dan jira sarki ya kammala wani uzuri sannan ya saurare su.
Akan idon su Ishaqa Sarki keta zazzagawa al'ummar garin fada. Yana ta cika da batsewa. Su kuma al'ummar gari kowa yayi tsit, babu mai cewa kanzil. Koda gyaran murya baka ji. Wanda hakan ke fayyace irin tsoron da jama'ar garin kewa sarkin nasu. Daga bisani bayan ya gama fadan, aka gabato da wani mutumi. Sarki ya umarci hauni ya sare kansa. Ai kuwa kafin kace kwabo sai ga jini yana tsartuwa, hauni ya raba kan mutumin da gangar jikinsa.
Wannan abu yayi matukar kidima turkawan dake tawagar ishaqa. Kasancewar basa jin hausa sosai, sai suke tambayar ishaqa abin dake faruwa. Sai shima ya kusanci wani bafade da wannan tambayar.
Bafaden cikin tsoro murya qasa-qasa ya baiwa Ishaqa amsa da cewa "Ranka ya dade, akwai sarkin yaqi gashi can Azaune, shine yayiwa sarki bajinta ta cinye wani Gari da yaqi. Wannan yasa Sarki ya yaba masa kuma yace ya zabi duk abinda yakeso sarki zaiyi masa. Sai sarkin yaqi yace babu abinda yakeso sama da a aura masa diyar wannan mutumi da aka sare kansa. Ita kuwa wannan yarinya duk garinnan babu kyakkyawa irinta. Sarki kuwa yace tilas haka ta yiwu, don haka yaune ranar da akasa za'a daura aure, amma kuma sai aka nemi amarya qasa ko bisa aka rasa. Wannan yasa sarki yayi fushi yace ubanta ne ya boyeta, don haka ya yanke masa hukuncin kisa. Ita kuma gobe zai tura da rundunoni, yasha alwashin indai tana doron qasar nan sai an kamo ta"
Ishaqa ya girgiza kai alamar baiji dadin abinba. Ya kalli mutumin da ake cewa shine sarkin yaqi, ya ganshi wani bijimi ne maras kyan gani. Gashi baki wuluk, da jajayen idanuwa sai muzurai yakeyi. Tabbas shima ya hango dalilan da zasu hana kyakkyawar budurwa ta auri wannan basumuden mummunan qato, ya tabbatar babu soyayya a lamarin, amma kasancewar tarbiyar da Mehmet ya basu itace kada su yarda su sanya baki cikin sha'anin mulkin wani sarki, sai kawai ya labartawa turkawan abinda ke faruwa sannan ya gargade su da kada wanin su yace uffan.
Bayan sarki ya kammala ne, sai ya fuskanto su. Yayi musu lale marhabin yana mai tambayar ina abokin sa Mehmet ya shiga?
Ishaqa ya labarta masa halin daya baro Mehmet da kuma shawarar daya yanke. Daga nan kuma ya gabatarwa da sarki kayayyakin da mehmet din ya aiko su dashi wadanda suka hadar da manyan riguna da shimfidu na alfarma, da wasu dogayen bindigu tare da alburusan su, da tasoshi nacin abinci wadanda akayisu da azurfa, da dai makamantansu. Sarki ya dube su cikin farin ciki yayi murna sosai. Sannan shima ya bada umarnin a hada musu bayi wadanda zasu tafi dasu.
A wannan Rana dai 'yan tawagar ishaqa hutawa kurum sukayi. Kashe gari kuma suka shiga kasuwa. Anan ne kowa yake siyar da kayan dayake tafe dashi, tare da siyo abinda yake ganin yana da daraja a kasashen larabawa.
Bayan kwana biyu suka yi bankwana da Sarki, sannan suka hau dawakan su tare da yin haramar komawa Damagaran.
Basu jima suna tafiya ba sai wani baturke wanda yake aboki ne ga Mehmet mai suna Ottoman, ya matso kusa da Ishaqa yana cewa "Ishaqa Mujde, mujde ishaqa". Ma'ana "Inada wani kyakkyawan labari ishaqa" sai kuma ya gabatar wa da Ishaqa wata mace wadda ta lullube fuskarta da baqin mayafi.
Ishaqa ya tambayi Ottoman menene labarin? Kuma wacece haka? Shine ottoman din yake sanar dashi cewa ai wannan macen itace wadda ake nema a kano, kuma kawai ganinta sukayi acikin tawaga ba tare da sun san yadda akayi ta shigo ba. Don haka kasuwa tayi riba kenan, domin ya tabbatar da cewa ba qaramar daraja matar zatayi ba.
Nan take Ishaqa ya tsaida dokinsa, abinda ke nuni da kowa ma ya tsaya. Ransa a bace, ya kalli macen gami da daka mata tsawa, yace "yi maza ki fita daga ayari na, ba zaki janyo min masifa ba".
Matar nan ta rugo da gudu ta duqursa a gabansa tana magiya, ya taimaka ya kyale ta, yayi mata rai, saboda komawarta kano azaba ce. Har tana cewa "ya kai wannan shugaba mai adalci kaji tausayi na, kayi mini rai, bani da kowa a duniyar nan, sun kashe mini mahaifina, sun karbe duk abinda muka mallaka, idan na koma hannun su mutuwa zanyi.."
Ishaqa yace ai sam bazai yiwuba. Saboda matsawar Sarkin kano yaji labarin sun tafi da ita zai iya biyo sawu, ko kuma zai iya yanke duk wata alaqar kasuwanci dake tsakanin sa da maigidansa Mehmet, shikuma ba zai taba son ya batawa ubangijin saba. Don haka sai ya umarci wasu dakarunsa da suyi gaggawar ciccibarta su mayar kano.
Tana kuka da birgima haka suka fincike ta, suka dora bisa wani ingarman doki, suka fita aguje zasu kaita kano.
Ana haka kuma sai Ishaqa ya fahimci hukuncin daya dauka baiyiwa 'yan tawaga dadi ba, saboda duk tausayinta ya kamasu. Yayi jim yana tunanin mafita, shima kansa tausayin nata ya kamashi, sai kuma ya yanke shawarar canza tunani.
Saboda haka da kansa yabi bayan dakarun yana kwalla musu kira har saida ya tsayar dasu, sannan ya umarci a kyaleta a tawagar, amma da sharadin zata rinqa boye kanta don gudun kada a ganta akaiwa Sarki labari ya biyo bayansu. Daga nan sai suka ci gaba da tafiya.
Tun daga wannan lokacin, wannan matar take ta yunkurin zantawa da ishaqa. Shi kuwa sam bata gabansa, har kar sa kawai yakeyi. Daman mutum ne wanda bai cika son surutu ba.
Rannan kuwa sai akayi sa'a, tawaga ta yada zango, Ishaqa da Ottoman sun kebe suna fira, sai yaji ottoman yana magana da harshen turkanci, yana cewa "Guzellik Guzellik, ya subhanallah" Ma'ana, 'Kyakkyawa kyakkyawa, tsarki ya tabbata ga Allah'.
Ashe matar nan ce ta yaye fuskarta ta tunkaro inda suke domin tayi magana da Ishaqa. Da isowar ta tagaishe da ottoman, sannan na roqeshi izinin ganawa da Ishaqa. Don haka sai ya tashi ya basu wuri.
Ta dubi ishaqa, suka hada ido, ta sakar masa wani murmushi lallausa, sannan ta duqar dakai ta fara magana cikin ladabi, tana mai cewa "Ya shugaba, ina maka godiya bisa tausayi na da kaji har ka kyaleni acikin tawagar ka, kuma idan ka amince, inason labarta maka halin da nake ciki ne"
Ishaqa ya kura mata ido, saboda ya tsinci kansa ne a wani yanayi wanda har yanzu bai san sunan saba. Ya gyada kai, alamar ya amince. Ita kuma sai ta cigaba da cewa "Da fari dai sunana Randiyya, mahaifina attajiri ne babba a birnin kano, wanda babu attajiri irinsa. Ni kuma nice kadai 'yarsa, mahaifiyata ta rasu tun ina qarama.

No comments:
Post a Comment