Saturday, 9 December 2017

HIKAYAR SARKIN BIRNIN HUNAN DA ALJANNU

HIKAYAR SARKIN BIRNIN HUNAN DA ALJANNU
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Daga cikin tsoffin hikayoyin da suka shahara a birnin
Sin daruruwan shekaru da suka gabata, wannan hikaya
na sahun gaba.
Akace a wani zamani daya shude anyi wani babban
birni mai suna Hunan. A wani lokaci kuma, sai ya
kasance anyi wani attajirin sarki a garin wanda ya tara
mamakon dukiya a baitul malinsa. Har ya kasance ya
taskance sunduk'ai na zinariya kimanin dubu d'ari
shidda acikin wannan taska. Wannan ne yasa yaga
buk'atuwar samo mutum mai amana don dank'a masa
gadin wannan taska.
Akan haka, sai ya baiwa wani amintaccen Bafadensa
mukullin taskar. Ya shaida masa cewa ya dank'a tsaron
dukiyar duk dake ciki a hannunsa. Baya son ko allura ta
b'ata.
A kullum, wannan ma'aji yana baro gida da dare, yazo
ya kwana da safe ya koma gida. Kullum haka kullum
haka. Rannaan ya baro gida kenan sai hadari ya hadu a
gari, kafin kace haka ruwa ya kece mai mamakon
yawa. Tilas ma'ajin taskar sarki ya nemi mafaka a wata
rumfa tsohuwa, da niyyar da zarar ruwa ya d'auke sai
ya k'arasa wajen aikinsa.
Abu dai kamar wasa, a wannan dare sai da aka kwana
ana ruwa. Hakan na nufin ma'aji a rumfar daya fake ya
kwana sab'anin a taskar sarki. Aikuwa bayan d'aukewar
ruwa ya runtuma izuwa taska. Sai dai ga mamakinsa,
yana zuwa sai ya tarar da ita a washe. Babu ko allura.
Wannan abu yayi matuk'ar sanya shi jimami. Ya rasa
inda zaiyi da kansa. Yayi dube-duben duk da zaiyi tare
da tambayar makwabta, amma sam bai samu wani abu
mai dadi ba. A k'arshe dai ya yanke shawarar tafiya
don sanar da sarki wannan mummunan labari.
Da zuwan sa fada, ya fadi gaban sarki yayi gaisuwa.
Sannan ya kwashe labari ya fad'awa sarki. Sarki yace
sam bai gamsu ba, k'arewa ma sai yasa fadawa su
tuhume shi, yace awurin sa wannan ai barkwanci ne.
Abu dai kamar wasa, fadawa suka rink'a nakad'awa
ma'aji azaba, amma bai canza maganar saba. Sarki
yasa aka je taska aka gano yadda ma'aji ya fada
hakanan take.
Da sarki yaga ana neman hallaka ma'aji ba tare da
samun wata magana mai k'wari ba, sai yace a dakata.
Yacewa ma'aji ya bashi lokaci, da zimmar yaje duk inda
wannan dukiya take ya maido da ita, ko kuma a
maimakon ransa.
Ma'aji ya taso daga wurin sarki a gajiye, tinkis-tinkis.
Yana tafiya kamar wani mashayi sabida azabar da aka
gana masa. Azuciyarsa kuwa yana ta sak'a yadda zaiyi
da rayuwarsa. Kwatsam sai ga wani makoho ya
bangaje shi. Ma'aji cikin fushi ya dubi makaho zai daka
masa tsawa saboda bangajin da yayi masa, amma
dubawar dazaiyi sai ya fahimci ai makaho ne, don haka
baice uffan ba, ya cije baki kurum yayi gaba.
Makaho ya juyo yana doddogarawa da sandarsa, yana
kai hannu dazimmar kamo tufafin wanda ya bangaza,
yana cewa yi hakuri mallam, kune ke ganin mu ba
mune ke ganin kuba.
Ma'aji yace to babu laifi, amma dai zaifi kyau ka rink'a
yawo da d'an jagora, kasan halin mutanen yau da zafin
zuciya, idan wani ka bangaza haka yana iya kwabd'eka
da mari.
Makaho yace kwarrai kam. Mutanen yau sai hakuri. Sai
dai na karanci wani abu a tattare dakai, don haka idan
kanaso matso kusa na taimakeka.
Ma'aji yace me ka karanta? Kuma wanne irin taimako
zakayi mini? Yana mai matsawa kusa da makaho.
Makaho ya dafa kafad'ar ma'aji a dai-dai sa'ar dayazo
daf dashi sannan yace "ni daka ganni nan, makaho ne
mai karantar abinda ke zukatan mutane. Kuma a yanzu
na fahimci cewa matsalar kud'i ce ta dugunzuma ka.."
Ma'aji yace tabbas haka nan ne. Daga nan ya zayyana
masa labarin sa duka.
Makaho yace to biyo ni idan kana Iyawa, da sannu zaka
gani da idonka.
Daganan suka fara tafiya. Ma'aji na gaba makaho na
biye, amma makaho ke fadin inda za'abi. Shine ke
cewa ayi gabas, yamma, kudu ko arewa. A haka har
suka bar gari, suka shiga kungurmin daji cikin manya-
manyan duwatsu. Suka hau kan wata hanya da take a
tsakankanin duwarwatsu, basu jima ba sai ga wani
katafaren birni a gabansu.
Nan ma dai suka shiga cikin garin, ga mutane nata
harkokinsu babu mai tankawa wani, gidajen garin kuwa
na alfarma ne dogaye gwanin ban sha'awa.
Suna cikin tafiya, sai makaho yace wa ma'aji ya tsaya.
Sannan makaho yayi nuni da sandarsa izuwa kofar wani
babban gida na alfarma, yace "ka kwankwasa wannan
kofa, ka nemi taimakon mutanen gidan akan matsalar
ka, da yardar Mai sama zaka dace da buk'atar ka."
Daga nan bai k'ara cewa uffan ga ma'aji ba, ya wuce
gaba yabar shi anan.
Ba tare da bata lokaci ba, ma'aji ya matsa kusa da
kofar gidan ya fara kwankwasa ta sannu a hankali.
Ba'ajima ba kuwa sai yaji ana kici-kicin bude kofa.
Wani mutumi fari dogo ne yafito daga gidan, yana
sanye da tufafi kalar tufafin da fadawan sarkin Hunan
ke Sanyawa. Ma'aji ya kwashe duk abinda ke tafe
dashi ya fadawa wannan mutumi. Mutumi kuwa yace
kwarrai kazo inda za'a taimakeka, amma sai idan zaka
iya jira na wasu yan kwanaki a cikin wannan gida.
Ma'aji yace to babu matsala. Shikenan kuwa sai suka
dunguma izuwa cikin gidan....
Ma'aji ya cigaba da zama a wannan katafaren gida ba
tare daya nemi wani abu ya rasa ba. Ana bashi abinci
da ruwa akai-akai, amma dai ank'i bashi fuskar yin fira
tayadda zai samu jin wani labari daga wurin mutanen
gidan.
Wata rana ya samu damar zagayawa cikin gidan, sai ya
samu wani lambu daga bayan gidan mai cike da
itatuwa na alatu. Ya shagaltu yana zagaya wannan
lambu tare da tsinkar 'ya'yan itatuwn cikinsa yana Ci
cikin nishadi.
Yana cijin wannan zagaye ne sai gashi a wurin wani
katon keji na k'arfe. Dubawar da zaiyi a ciki sai ga
sassan jikkunan dan Adam yashe a ciki. Kawuna,
hannaye, 'yan hanji, da dai sauransu.
Ma'aji yayi saurin d'auke kansa, yaji gaban sa na
fad'uwa sabida kad'uwarsa ga abinda ya gani. Bai yi
wata-wata ba ya fara waige-waigen hanyar fita domin
ya gudu daga gidan.
Abinda tunanin sa ya wassafa masa shine, wannan gida
ne da ake cin naman bil'adama. Don haka zaifi kyau
yayi nasa wuri tun gabannin irin haka ta auku gareshi.
Ya fara azamar fita kenan, sai wani tunani ya cika
zuciyar sa akan cewa idan har ya fita daga gidan nan
yanzu bashi da makoma sai mutuwa, kuma back ribar
bin makaho ba. Don haka wata zuciyar ta gargade shi
da cewa gara ya mutu a wannan gida akan ya komawa
sarkin hunan da labarin bai san inda dukiyar sa take ba.
Hakan kuwa akayi, sai yayi ta maza ya dake kamar
baiga komi ba, yacigaba da zamansa a gidan.
Kashe gari wannan mutumi daya bude masa k'ofa tun
da farko ya fito gareshi, sannan yace masa lokaci yayi,
don haka idan ya shirya yana iya binsa izuwa inda za'a
warfare masa matsalar sa. Ma'aji yace a shirye yake,
don haka ko ina za'aje aje.
Mutumi yayi kwalliyarsa da tufafin sa na fadawa,
Sannan ya d'are bisa ingarman doki yacewa ma'aji ya
bishi a baya. A haka suka shiga cikin gari tinkis-tinkis,
babu mai kulasu suma kuma ko uhm basu cewa kowa
ba, har izuwa wani Katafaren gini.
Mutumin ya sauko daga doki ya shiga ta tsakankanin
wasu fadawa masu tufafi irin nasa su shidda, ya umarci
ma'aji ya biyo shi. Aka bude musu kofar gidan suka
shiga, sannan suka yi tafiya kadan har izuwa wata
babbar haraba. Daga nan sai mutumin ya tsaya chik,
batare daya ce uffan ba yayiwa ma'aji nuni da wata
kofa da nufin yaje ya bud'e kofar ya shiga.
Ma'aji yayi kamar yadda aka umarce shi. Budewar
kofar da zaiyi sai kuwa ya ganshi a wata sabuwar
alk'arya. Wata k'asaitacciyar fada ce mai dauke da
kujeru na alfarma, da kayayyakin alatu wadanda bai
taba ganin irin suba, ga mutane da dabbobi kala-kala
barbaje a kasa, wasu kuma suna can bisa kujeru anci
ado na alfarma.
Daga can nesa kuma sai ma'aji ya hango wani mutum
mai kwarjini, da ado mafi na sauran, yana zaune bisa
kujerar mulki, kai da gani kasan shine sarkin wannan
masarauta. Kai tsaye ma'aji ya nufi inda yake, sannan
ya zube k'asa yana kwasar gaisuwa.
Anan ane sarkin ya tambaye shi ko shine mai kula da
taskar birnin Hunan! Ma'aji yace kwarrai shine.
Sai sarkin yace " dukiyar nan gaba dayanta tana nan
tare damu. A hakika bani da wata bukata agame da ita,
amma babu yadda na iya wajen karbarta daga hannun
wani gwamna na. Shine ya kwaso ta kuma ya aikota
gareni"
Dajin haka sai ma'aji ya fashe da kuka, jikinsa yana
kyarma, yahau Afi ga sarki.. Har ya sanar dashi irin
azabtarwar da sarkin yayi masa akan bacewar dukiyar
da kuma abinda ke jiran sa idan ba'a samu dukiyar ba.
"Wannan abu mai sauki ne" inji sarkin.
"Kayi sani cewa wannan rigima ba taka bace, amma
zamu wanke ka daga cikinta".
Daga nan sarkin ya umarci a baiwa ma'aji wata
zungureriyar takarda, sannan yacewa wasu sadaukai
suyi masa rakiya don su bada shedar inda dukiyar take.
A wannan karon, hanyar da aka biyo don kawo ma'aji
gida tasha bambam da wadda makaho ya bi dashi.
Ma'aji ya rink'a ganin abubuwan mamaki, kamar
lambuna na alfarma wadanda ko a labari bai taba
misalin suba, dabbobi masu magana, ga Macizai akan
dokuna, da dai sauran su.
Sai dai kuma suna wuce wasu manyan tsaunika sai
sadaukan nan suka ce masa to fa iyakacin su nan, tilas
shi kadai zai karasa garin Hunan. Daga nan suka juya
da baya suka barshi anan.
Ai kuwa babu yadda ya iya. Ya kamo hanya, sannu a
hankali sai gashi a Hunan. Da zuwan sa kuma Bai
zaame ko ina ba sai fadar sarki. Ya zube ya kwashi
gaisuwa sannan ya labartawa sarki abin duk daya faru.
Sarki yayi fushi matsananci, sannan yace wannan ai
zancen wofi ne, raini kurum ma'aji ke kawo masa. Daga
nan yace wa fadawa a tambaye shi. Sai kuwa suka yi
caa kansa, suka fara dakumar sa zasu yi sama dashi
su buga, sai yace a tsaya-a tsaya, akwai takardar
shaida da sarkin garin ya bayar a baiwa sarki.
Sarki yace musu su dakata, ya karbi takarda ya
karanta. Bayan ya gama ne aka kara ganin bacin rai
sosai a fuskar sarki. Sannan yace a sallami ma'aji ya
tafi, amma kuma yana so duk yadda za'ayi fadawan sa
su tattaro masa dukiyar datafi wadda aka kwashe yawa
daga hannun mutanen sa nan da kwana uku harma ya
basu damar halaka duk wanda yayi musu tsaurin kai.
Anyi wannan da kwana biyu, aka wayi gari sarkin ya
mutu, matarsa kuma da yafi so ta tashi da safe taga
kanta da kwalkwal, kai kace ma'aski ne ya aske gashin
ta.
Wannan abu ya baiwa mutanen garin matukar mamaki.
Amma kuma da aka binciko takardar da ma'aji ya kawo,
sai aka fahimci inda lamarin ya dosa. Ga abinda aka
rubuta a wasikar:-
Tun sa'ar da kahau karagar mulki muke gargadin ka
akan halin ka na bushasha da tara dukiyar haram, gami
da kuntatawa mabiya. Sundukan zinariya guda dubu
dari shidda na wurin mu, mun dauke sune don yi maka
gargadi bisa daina mulkin zalunci tare da shinfida
adalci, don haka tilas ne kada ka azabtar da ma'ajinka
akan laifin da bai aikata ba. A karshe muna sanar maka
da cewa matsawar baka Saduda ba, da sannu zamu
halaka ka, zakuma mu tozarta matar ka dakafi so a
duniya".
Mutanen garin nan sunyi matukar bincike don gano
hanyar da makahobyabi da ma'aji wajen zuwa wannan
gari da ma'aji yaje, amma ba'a samu ba. Daga bisani
dai labari yazo cewa akwai masarautar sarkin aljannu a
gefen wannan gari, kuma ya hana zalunci da tara
dukiyar haram ga sarakuna. Don haka tilas sauran
sarakunan dake yankin suka saduda, suka dena
addabar mabiyansu saboda tsoron kada abinda ya
samu sarkin Hunan ya auku garesu.
Ana koyar da dalibai halayyar dan adam ne wajen
labarta musu wannan hikaya. Mutun na iya aikata duk
abinda yakeso matsawar baya tsoron aukuwar wani
mummunan abu akansa.
Karshen wannan hikaya kenan.

1 comment: