TARIHIN ANDALUS: TSOHUWAR MASARAUTAR
MUSULUNCI DATA KAFU A SPAIN
Kashi na hudu
Daga SADIQ TUKUR GWARZO
Dakarun Sarki Yusul al-Fihiri dana Yarima
Abdurrahman sun hadu daf-da-daf a bakin tekun
Gwadalqibir dake nesa da birnin Qordoba.
Kowacce runduna tana fuskantar kowacce.
Tun Asali, wannan teku na Gwadalqibir, ambaliya
yayi saboda kwararar da yakeyi mai yawa. To
amma a wannan karon sai ya Kafe, wannan yasa
akayi rashin abinci a yankin domin ba'ayi noma
ba. Don haka dakarun Yarima Abdurrahman sun
gamu da karancin abinci a lokacin da suka isa
wannan yanki. Shikuwa Sarki Yusuf alfihiri, ganin
haka, sai yasa aka rinka yin odar abinci ga
dakarun sa, ana basu shi ci-bari.
Da fari an fara shirya sulhu ne maimakon zubda
jini. Tunda har an shirya cewa Sarki Yusuf al-fihiri
zai aurawa Yarima Abdurrahman 'yarsa ta cikinsa
zai bashi dukiya mai yawa. Zai kuma bashi
mulkin wani gari a cikin Masarautar sa. Amma
daga bisani yarjejeniyar ta watse, aka tabbatar
da cewa yaki shine kadai mafita.
Sannan kuma wata rarrabuwar kai ta kara
tasowa acikin dakarun Yarima Abdurrahman,
kasancewar wani ingarman doki daya hau irin na
turawan Spain din, sai larabawan Shamiyum dake
cikin tawagarsa suka fusata har suke kunji-kunjin
cewa dalilin dayasa ya nemi wannan dokin shine
saboda idan yaki yayi tsamari sai ya arce ya tsira
da ransa, tunda babu wanda ya taba ganin yakin
sa, balle a bada shaidar yarima Abdurrahman
Sadauki ne.
Abinka da jinin Sarauta kuma gwanin siyasa da
hikimar shugabanci. Daya fuskanci matsalar dake
faruwa, sai yayi hawa nan-da-nan ya isa ga wani
sarki dan kabilar shamiyum dake zaune a wani
dan tsibiri kusa da inda suke. Ana kiran tsibirin
da suna 'Noorayn', ya gaishe shi, sannan ya nemi
sarkin daya musanya masa dokin da yake hawa
da wani, saboda acewar Abdurrahman, yasha
wahala wajen hayowa kan tsibirin da dokin sa. A
karshe sai sarkin yayi farin ciki da haka, shine
kuma ya baiwa Yarima Abdurrahman kalar dokin
da Larabawan Shamiyum ke hawa shikuma ya
karbi nasa. Wannan abin shine ya kashe rigimar,
bacin ran larabawan ya gushe, suka ji cewar a
shirye suke suyi yaki domin yarima Abdurrahman.

No comments:
Post a Comment