TARIHIN ANDALUS: TSOHUWAR MASARAUTAR
MUSULUNCI DATA KAFU A SPAIN
Kashi na uku
Daga SADIQ TUKUR GWARZO
Yarima Abdurrahman ya kara azama a kokarin sa
na shiga Yankin Andaluz, duk dadai bai san halin
da zai samu kansa ba saboda rikita-rikitar da ake
fama da ita a yankin. Sarkin Andaluz dai Yusuf al-
fihiri dan kabilar Berber ne, ance ya samu sabani
da wazirin sa kuma sirikinsa mai suna Al Sumayl
ibn Hatim Al-kilabi wanda ya fito daga wata
kabilar Larabawa dake sham(syria) mai suna
shamiyum. Har sun fara yaki a tsakanin su.
A Rundunar waziri sumayl akwai yawa-yawan
mutane masu kyakkawar alaqa da Umayyawa,
don haka yarima Abdurrahman yake tsammanin
zai samu mafaka a wannan runduna. Akan haka
ne Abdurrahman ya dakata a Afirka kusa da
garin Sebta, sannan ya tura yaronsa Badar domin
yaje ya nemo masa izinin shigowa wannan
runduna ta Sumayl dake Andulus. Badar yazo
Andaluz, ya samu kwamandojin yakin dakarun
kabilar shamiyum guda uku, Ubaidallah Ibn
Uthman da Abdullahi ibn khalid wadanda dukkan
su 'yan usulin garin damaskus ne kuma 'yan
kabilar Qaisu wadanda suke jinsi daya da
Umayyawa, sai kuma na ukunsu mai suna Yusuf
ibn Bukht wanda ya fito daga garin Qinnasrin.
Dukkan su sun amince da zuwan sa, amma sai
suka ce basu da ikon sahale masa yazo har sai
an jira izini daga babban kwamanda Waziri
Sumayl wanda alokacin yake zaune a Zaragoza.
A cikin rashin sa'a, da aka aikawa Sumayl, sai
yaji tsoron idan har Yarima Abdurrahman ya
shigo rundunar sa, nan gaba shugabanci zai
nema, kuma sai ya danne shi. Don haka sai yace
sam bai yadda ba. Sai dai kuma da kwamandojin
Qabilar Qaisu suka ji labari, sai suka sanar da
Bedar cewa ya sanarwa Abdurrahman cewa su a
shirye suke su taimakeshi kuma su goya masa
ba. Domin a cewar su, da su rinka yiwa
larabawan shamiyum biyayya karkashin
jagorancin sumayl, ko suyiwa laraban firhiyyun
biyayya karkashin Sarki Yusuf al fihri, zaifi kyau
subi dan Kabilar su Abdurrahman, domin farfado
da Sunan Umayyawa, in yaso kome zai faru ya
faru. Da wannan sakon Bedar ya samu Yarima
Abdurrahman kuma.
Akan haka sai Abdurrahman ya shirya bin wasu
mutane masu son shiga kasashen turai don tafiya
izuwa Andaluz. Ance daf da tafiyar sa ta cikin
jirgin ruwa wasu Kauyawa 'yan kabilar berber
suka tare shi a hanya, sannan suka ce sun kama
shi zasuyi garkuwa dashi, matsawar yana son fita
daga Afirka sai dai ya fanshi kansa. Ala tilas ya
fanshi kansa da zinare. Bayan ya dauka ya basu
sannan ya shiga jirgin ruwa don tafiya.
Wadancan kauyawa suna tafiya, sai kuma ga
wata zugar ta iso, itama taji labarin Abdurrahman
zai bar Afirka zuwa turai, don haka suka garzayo
karbar ganima a wurinsa, amma kuma akayi
rashin sa'a sun zo a makare, tunda har jirgin
nasu ya fara tafiya akan ruwa. Shine kuma har
wani daga cikin kauyawan yayi kokarin tsayar da
jirgin ta hanyar shiga cikin ruwa da rike igiyar
jirgin da hannun sa, yana kokarin tsayar dashi.
Amma kafin ya samu nasara, sai aka samu wani
daga cikin matukan jirgin ya sare hannun
mutumin. Jirgi ya mika da tafiya, suka barshi nan
yana ruri.
A karshe dai, Abdurrahman ya samu damar
sauka a wani waje da ake kira Almunekar, dake
gabashin Malaga, cikin Yankin na andalus, a
watan Saftamba na shekarar 755.
Da saukar sa sai kwamandojin nan biyu na
kabilar Qaisu dake cikin tawagar Sumayl wato
Abu Uthman da ibn khalid suka yo hawa tare da
mahaya guda dari uku 'yan kabilar Qaisu da wasu
na kabilar Shamiyum, suka tarbe shi. Sannan ne
akace labari ya rinka bazuwa cikin garin Malaga,
ana fadawa mutane su fito su tarbi Yarima,
wanda ake tsammanin ya rasu, ashe yana raye.
Nan da nan kuwa ya zamo mai farin jinin
mutane, aka rinqa zuwar masa da kyaututtuka,
anan ne ma akace wani yayi masa kyautar wata
kyakkyawar Baiwa, amma daga baya sai ya
maishe ta ga ubangijiyarta. Kuma ance a iya
zaman sa a Malaga, sai daya tara 'yar karamar
runduna ta sadaukai masu jiran umarnin sa.
Abu kamar wasa, sai gashi labarin zuwan Yarima
Abdurrahman ya bazu cikin Andulus kamar wutar
daji. Wannan yasa Sarki yusuf Alfiri da waziri
Sumayl suka hada kai, domin sunga kurar da
zata kaudasu ta taso, sai suka fara shirya
shawarar yadda zasuyiwa Yarima Abdurrahman
gadar zare su dusasar dashi ko su hallaka shi,
akarshe suka shawarta cewa suyi masa tayin
aurar 'yargidan Sarki Yusuf al fihiri, idan kuwa
yaki, kawai su kasheshi. Sai dai abinda basu sani
ba shine, yarima Abdurrahman yana da matukar
wayau da hangen nesa, don haka duk ya
tsammaci muguwar manufa daga garesu.
Ana cikin haka, sai fada ya barke a Zaragoza.
Wasu 'yan tawaye masu fafutikar neman mulki
suka hada runduna suna yakar dakarun Waziri
Sumayl. Wannan yasa Sarki yusuf din da waziri
sumayl suka hada karfi domin yakar 'yan
tawayen. Hakan kuma sai ya baiwa Abdurrahman
damar kara samun wurin zama da kuma karun
dakaru masuyi masa biyayya. shine ma aka ce a
watan maris na shekarar 756, Yarima
Abdurrahman ya kame garin Sevilla ba tare da
wani hargitsi ba.
Sarki Yusuf al fihiri yayi niyyar zuwa Sevilla don
korar Abdurrahman, amma sai wani fadan na 'yan
tawaye ya kara tasowa a garin Pamplona dake
karkashin masautar Andalus din dai, ga kuma
wancan na zaragoza ba'a kammala ba. Sai ya
zamana yana cikin tsaka mai wuya. Da fari, ya
fara maida Karfin sane don ganin yaci nasarar
murkushe 'yan tawaye, amma da abin ya gagara,
sai kawai ya yanke shawarar juyowa kan Yarima
Abdurrahman da yaki.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo

No comments:
Post a Comment