TARIHI: MULKIN FULANI A KANO, DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.
Kashi na shidda.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN
08060869978
FITINAR WASU KABILU MAZAUNA TSAUNIKA
A wannan lokacin dai na Mulkin sarkin Kano Marigayi Abdullahi ɗan Ibrahim Dabo fitinar wasu kabilu mazauna tsaunika ta bijiro.
Ance sarkin Bauchi Ibrahim ya gwabza yaki dasu, amma sai ya haɗu da raunin dakarunsa a kansu, tilas ya koma gida don sake shiri.
To ganin haka kuma, sai kabilun ya zama kamar sun samu karfin guiwar cigaba da takurawa jama'a ne, inda suka rink'a tura mayakansu garuruwa suna kamo mutane a matsayin bayi gami da kwace dukiyoyin su.
Abu kamar wasa, sai ya zama wannan ta'asa ta kwararo izuwa yankunan kano, har ma an kaiwa wasu rundunoni da Sarkin kano Abdullahi ya ajiye a yankunan hari.
Don haka, koda Sarki Abdullahi yaji haka, sai yace sam bazai kyale ba.
Wannan yasa ya tara 'yan majalisarsa domin neman mafita akan cewa 'shin zasu fara zuwa don kaiwa waɗannan kabilu harin yaki ne, ko kuwa gari ya kamata su soma kafawa inda za'a jibge rundunar yaki?'
Anan ne shawara ta tashi akan cewa a soma kafa gari kafin akai yaki.
Hakan kuwa akayi.
Sarkin kano Abdullahi ɗan Ibrahim Dabo ya aike aka gina gari, sannan ya tashi da runduna mai yawa izuwa garin.
Bayan ya ɗan huta ne sai yayi haramar yaki, ya fito daga garin da aka gina masa tare da tunkarar waɗannan arna mazauna saman duwatsu.
Ance kafin ya karasa ɗin ne sukaci karo da sarkin Bauchi Ibrahim, sannan dukkansu suka ɗunguma izuwa wani gari mai suna Duwa, suka yaki dakarun garin tare da tarwatsa su. Suka kuma k'one garin gaba ɗayansa, sannan kowanne sarki ya koma birninsa.
Bayan sarkin Kano Abdullahi ya komo kano daga wancan yak'i na Duwa, bai jima ba sai ya sake haɗa runduna ta musamman sannan ya jagoranceta suka nufi yankunan arnan kan duwatsun nan, suka isarwa wani gari nasu mai suna Daraja, nan ma suka faɗa masa da yaki.
Aka yini ana gwabza yaki, dakaru na kai suka da sara da takubbansu ga abokan hamayyarsu, sai dai kaga wasu sun faɗi k'asa matattu, wasu kuwa sun zube magashiyan da munanan raunika. Daga bisani dai, Sarki Abdullahi yayi nasara akansu.
Sannan dai bai gaji ba ya k'arasa wani garin nasu mai suna Tufai nan ma da niyyar ya yak'esu, amma sai ya tarar mutanen garin sun k'one gidajensu da kansu kuma sun gudu sun bar garin.
Ganin haka, sai kuma ya k'arasa wani garin mai suna Banga, inda ananma ya tarar babu kowa a garin. Mutanen garin sun bar gidajensu da dukiyoyinsu sun fice daga gareshi.
Don haka sai sarki ya umarci a sauka a garin don a huta.
Ashe wai mutan garin sunji labarin yaki ne shine suka gudu baki ɗaya suka bar dukiyarsu.
Aikuwa ance Sarki Abdullahi ya tara gagarumar ganima daga wannan gari.
A wannan dare da sarki Abdullahi da jama'arsa suka saukadon su huta a garin banga, sai basu samu hutun ba, ashe wai tarko aka ɗana musu don su faɗa a mamaye su, tunda kuwa arnan sun tara dakaru masu yawa sun laɓe, sai da dare yayi sannan suka kawo sumame.
Haka kuwa aka kwan ana buga kazamkn faɗa, amma dai cikin ikon Allah duk da haka arnan basu samu galabar yaki ba. Sarki Abdullahi da rundunarsa ne suka ci nasarar tarwatsa su.
A wani waje mai suna Sirfa aka haɗu da mutanen dutsen warji tare soma gwabza yaki.
Mutanen sun samu gagarumar taimako daga wani sarkinsu, amma cikin ikon Allah anan ma saida aka sake tarwatsa su.
Da sukaga an soma cin galaba akansu, sai suka soma ja da baya suna hawa saman dutsen inda gidajensu yake, ita kuwa rundunar sarki Abdullahi tana binsu sannu a hankali tana kashe su.
A haka har sai da suka kai kansu wani kogon dutse inda babu wurin ficewa, sai kuma suka nemi a dakata da yaki, suka kuma nemi a basu tsaro, ko kuma ace alkawarin ba za'a kai musu hari ba.
Suma kuma suna masu alkawarin ba zasu sake tayar da fitina ba ko zaluntar musulmai.
Abinka da jarumin Shugaba, Sarki Abdullahi mai koyi da halin ma'aiki Annabi Muhammad (s.a.w) Sai sarkin yace anyi musu duk abinda suke so.
Qadi Muhammad Zangi ya ruwaito a littafinsa "Taqyidil Akbar" cewa yana cikin wannan runduna tare da sarki Abdullahi, "haka muka sauko daga saman wannan dutse sannan muka shige izuwa wani wuri kusa da garin Gwaram mai suna Aru, arnan nan suna ta lekenmu daga saman datse suna mamaki".
Akace mutane kaɗan ne suna rage a garin Aru a lokacin da rundunar sarki Abdullahi suka riski gsrin, sauran duk sun tsere.
Waɗanda suka rage ɗin suma zuwa sukayi ga sarki Abdullahi suna masu tuba da eman kuɓuta daga gareshi.
ƁNan take suma aka shimfiɗa musu dokokin dake k'unshe cikin yarjejeniyar zama lafiya, suka ce "munji kuma mun karɓa".
Sarki kuwa yace "to kun kuɓuta".
Daga nan sai sarki ya tashi da jama'arsa suka komo kano.
Sai dai bai gama huce wannan gajiya ba ya samu labarin cewa waɗancan arna dukkansu sun karya yarjejeniyar da aka kulla dasu..

No comments:
Post a Comment