Wednesday, 6 December 2017

TARIHIN GWAGWARMAYAR MULKIN FULANI A KANO 7

TARIHI: MULKIN FULANI A KANO, DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na bakwai.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN
     08060869978

Da Sarkin kano Abdullahi ɗan marigayi sarki Ibrahim dabo yaji arna mazauna saman duwatsu sun cigaba da tayar da fitina ga makwabtansu, sai yace "tunda waɗancan mutane sun karya alkawari, tilas mu koma garesu da yaki."
  Nan take ya shiga shirin haɗa gagarumar rundunar yaki.
  Ance duk wani babban barde, ko wani kwararre a fagen fama dake kasar kano karkashin ikonsa sai da sarki Abdullahi ya gayyato shi, sannan ya tattarasu ya jagoranci runduna izuwa garin Daraja.
  Isar su garin keda wuya suka tarar babu kowa a ciki, an rushe gidajen garin ma, sai wasu gidaje kaɗan ne sukayi saura.
  Don haka sai basu ɓata lokaci ba, suka cigaba da tafiya izuwa wani gari mai suna Tufi.
   Shi Tufi ance babban gari ne mai cike da manyan tsaunika.
  Ance kuma tafiyar kwana biyu ce akeyi don zagaye waɗannan tsaunika.
  Kuma akan tsaunikan aka tabbatar da cewa tawagar arnan dajin nan sukayi ganganko.
 Rundunar sarki Abdullahi ta tunkari rundunar arnan saman duwatsu. Ana cewa da sarkinsu Dan maje, kuma a lokacin yana nan tare dasu. Nan fa aka soma yaki, ana fafatawa tun daga wajen garu har sai da aka shiga cikin birni ana gumurzu, ana bin arnan sukuwa suka ja da baya suna hawan tsaunika kamar dai yadda suka taɓa yi a baya, to amma a wannan karon, koda suka gama hawa saman duwatsun, sai suka sake karfi tare da kara azamar yakar rundunar kano, ala tilas tawagar Sarki Abdullahi ta juyo da baya a sukwane.
  A wannan rana dai kam batayi nasara ba.
  Amma fa kashegari, sai Sarki da kansa yayi hawa, suka sake koma musu da yaki.
   A wannan rana an buga yaki kasaitacce. Domin kuwa tun daga wajen ganuwa ake tura sadaukan Tufi baya har saida aka tunkuɗasu cikin birnin nasu.
  Sarki Abdullahi ya shiga birnin da kansa, sannan ya umarci dakarunsa dasu rusa garin baki ɗaya.
  Barade suka wanzu nuna sadaunantaka da bajintardu, aka wanzu anata ɗauki ba daɗi a wannan gari.
  Da gumu-yayi-gumu, tilas sadaukan Tufi da sarkinsu suka sauko daga kan duwatsu suka fice daga garin da gudu.
  Wannan fa nasara ce kurum daga Allah izuwa ga rundunar dake aiki dominsa.
   Bayan an huta, sai kuma runduna taci gaba izjmuwa garin Banga. Acan ne kuma aka haɗu da Sarkin Bauchi Ibrahim wanda shima yazo da rundunarsa domin ayita ta kare. Sai kuwa aka karawa runduna k'arfi sannan aka ja tunga ana sauraron mutanen garin Bunga.
  Ance ba'a tarar da mutane acikin Bunga ba, sai dai wasu da aka rinka hangowa a saman duwatsu.
   Daga nan sai rundunar ta cigaba izuwa wani gari mai suna Gamawa, to amma cikin nasara tun kafi a karasa garin, sai sarkinsu ya bada umarnin cewar kowa yabaro gidansa yazo ya tarbi sarkin musulunci Abdullahi domin nuna goyon baya gareshi
   Ai kuwa hakan sukayi, don haka koda sarki Abdullahi ya haɗu dasu, sai ya sauya akalarsa inda dukkansu suka ɗunguma izuwa garin kano.
   A kano suka suka suka huta.
Ance kwanaki tara sukayi a kano sai labari ya sake riske sarki Abdullahi cewar ga sarkin Arnan nan mai suna Dan maje nata yawatawa da runduna gagaruma a kan iyakokin kano yana kame mutane da zaluntarsu.
   Ai kuwa da gaggawa sarki Abdullahi ya sake shiri ya baro kano, sannu a hankali ya riski garin Garun Ali da yammaci amma sarkin yace sam ba za'a dakata ba, aci gaba da tafiya.
  Ance haka runduna taci gaba da tafiya, abinda ke tsayar da ita kurum sai ko idan lokacin sallah yayi shine ake a tsayawa a sauke farali sannan aci gaba.
  A haka har suka isa wani gari Abladu inda suka haɗu da wata karamar runduna da sarki Abdullahi ya ajiye a yankin domin samar da tsaro kafin abu yafi karfinsu.
   A wurin rundunar suke jin cewa Dan Maje ya gudu yabar yankin saboda jin sarki Abdullahi na zuwa, don haka sai sarki ya kwaso runduna suka koma wani gari mai suna Fadi. Acan suka zauna na wani lokaci, (wasu sunce kimanin shekaru uku) amma batare da anyi gaba-da-gaba da rundunar arnan ba saboda sunki juyowa yankin ma baki ɗaya ballantana a haɗu a gwabza.
   A wannan lokacin, dakarun Dan Maje duk sun fara tarwatsewa saboda gajiya da kuma tsoro, wasunsu ma har sukan zo ga Sarki Abdullahi neman afuwa tare da shiga cikin tashi rundunar.
   To amma dai da sarki yaga jinkirin na kara yawa, sai ya nemi shawarar cewa 'a tashi abisu da yaki ne ko kuma aje a tattake amfanin gonarsu dake garuruwansu?' Anan Sai shawara ta yanke akan cewa gara a fara lalata musu amfanin gona, idan sunji zafi kafin a gama aikin zasu iya kawo kansu a gwabza faɗa dasu.
  Shikenan, sai sarkin ya tashi haikan izuwa gonakinsu don saukar da yak'insa akansu.
  Suka isa Fagam, mutanensa suka bazama cikin gonaki suna fatattaka amfanin gona.
  Wani abin a tattake shi, wani kuma wuta zakaga an cinna masa yana konewa.
  Da mutanen fagam sukaga ba dama, sai suka zo suka nemi sulhu da tsaro daga Sarki Abdullahi, sai kuwa akace an basu abinda suke bukata bisa alkawarin sun bar sake tada fitina, sukace sunji sun amince.
  Baya da wannan, sai suka k'arasa garin warji, suka rufarwa garin da yaki.
  Arnan garin suka haye saman duwatsu tsammaninsu sun kuɓuta, amma ga mamakinsu sai suka ga dawakan kano na hawa garesu, sun mance cewar tuni sukayi atisayen hawa tsaunika.
   Aka buga yaki gagarumi, wanda takai tilas arnan suka gudu suka bar dukiyoyinsu da muhallinsu. Babu ko ɗaya daga cikinsu da yayi saura a saman dutsen nan. Sai kawai aka tattara dukiya mai tarin yawa a matsayin ganima aka mikata gaban Sarki Abdullahi.
  Da yake a lokacin ma sarkin Bauchi Ibrahim na tare dashi, sai yasa aka raba dukiyar biyar ɗaya aka bayar sadaka ga musakai, ragowar kuma suka raba tsakaninsu.
  An kammala wannan kenan sai sarki Abdullahi ya komo kano da rundunarsa cikin murna da kwarin guiwa, da niyyar zai sake komawa don ganin ya yaki shugaban Arna ɗan maje., sarkin bauchi ma ya koma gida abinsa.
  To amma kafin sarki Abdullahi ya sake komowa, sai wasika ta iske shi daga sarkin musulmi cewar ana bukatarsa da gaggawa domin halartar yakin Harifa.
   Tafiyar sarki Abdullahi sokoto ita ta baiwa Dan maje karfin guiwar sake haɗa runduna, sai kuwa fitinarsa ta sake komowa sabuwa.
  Kanawa kuwa me sukeyi idan ba addu'a ba..

No comments:

Post a Comment