TARIHI: MULKIN FULANI A KANO, DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.
Kashi na takwas (na karshe).
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN
08060869978
Masarautar Ningi
Ningi da Warji, sune manyan garuruwan da suke cikin masarautar Ningi.
Tun da jimawa ance akwai mutane a yankin, musamman kabilu marasa addini da suka haɗar da kabilun Fa,awa, Warjawa , Duwa, Ningawa da tsirarun Fulani.
Wani mai suna Mallam Hamza ne tare da wasu malumma kimanin arbain akace suka baro garinsu Tsakuwa ta gundumar Dawakin kudun kasar Kano saboda tsananin biyan kuɗin haraji daya damesu suka sauka a wannan yanki na masarautar Ningi, a wani wuri mai suna Mara.
Mallam Hamza ne jagorar waɗancan malamai, kuma a lokacin da suka isa yankin sun tarar akwai mutane da dama a yankin, harma shugabansu mai suna Dan-daura yana biyan haraji ga masarautar Bauchi wadda fulani ke mulka bayan sunci nasarar karɓe iko a yakin jihadi.
Wannan yasa Mallam Hamza ya shiga gamsar da Dan Daura cewar ya daina biyansu komi, domin a cewarsa ya kamata suma suci gashin kansu.
Da mallam Hamza yaga Dan Daura ba zai iya taɓuka komai ba, sai yashirya masa juyin mulki, ya halaka shi tare da zamowa jagora a yankin.
Kafin wani lokaci Mallam Hamza ya zamo shugaba, wanda ya haɗe kan kabilun Butawa, Fa'awa, Warjawa, Kudawa, da Sirawa, duk a karkashin ikonsa, kuma yana wa'azi tare da gamsar da wasu karɓar addinin musulunci, waɗanda kuma suka ki karɓa sai ya rabu dasu amma bisa yarjejeniyar suna cikin inuwar mulkinsa.
Wannan daula da Mallam Hamza ya kafa sai ta zamo barazana ga sarakunan Bauchi, zaria da Kano.
Daga nan sai suka soma haɗa dakaru suna kai masa yaki.
A lokacin Sarkin Kano Ibrahim Dabo ance yayi yaki da Mallam Hamza(watakila tura runduna yayi) amma bai samu nasara akan saba har ya rasu.
A wuraren shekara ta 1850 akace Mallam Hamza ya rasu, sai waɗannan kabilun suka haɗu tare da zaɓar wani malami mai suna Ahmadu ya zamo magajin shi, wanda yayi mulki na tsawon shekaru biyar. Ya rasu kenan a shekara ta 1855.
A wannan lokaci ne kuma sirikin Marigayi mallam Hamza mai suna Abubakar Dan maje ya hau karagar mulki. Daga nan fa ya shiga zagayen kamen bayi daga masarautun dake makwabtaka dashi, ance ya shiga kasashen Kano, Hadejia, Katagum, Jama'are, Gombe, Zaria, Birnin Gwari, Kontagora, Wukari, har dama Illorin duk yakai harin yaki tare da kamo bayi.
A wannan lokacin, Dan maje ya kafa wata gagarumar runduna mai suna "Mai Taɓaryar Mashi", wadda ke kan gaba wajen murkushe duk inda suka sanya a gaba.
Sarkin Bauchi Ibrahim yasha gwabza yaki dashi, amma baya samun nasara.
Ance ma ya tsorata dashi sosai, har yana ɗari-ɗari da cewar Dan maje zan iya baro Ningi a kowanne lokaci yazo ya kwace iko da garin Bauchi, akan haka sai ya kafa runduna a garin 'kafin Madaki' wadda zata rink'a kula da motsin sa tare da ankarar dashi da sauri koda yayi wani motsin shigowa Bauchi.
To, a dai-dai wannan lokacin ne kuma Sarkin kano ɗan Ibrahim dabo ya soma yaki da Abubakar ɗan maje kamar dai yadda labari ya gabata.
Sa'ar da Sarki Abdullahi ya tafi sokoto bisa amsa kiran sarkin musulmi, sai Dan maje ya kawo hari gagarumi da nufin kwace ikon kano.
Ance wani ɗan Sarki mai suna Yusufu shine ya jagoranci runduna suka tarbeshi, suka fafata da sadaukan Dan Maje, har daga bisani yayi nasarar dakile harin nasu duk kuwa da irin gagarumar ɓarnar da sukayiwa kanawa.
Ance sarki Abdullahi daya dawo, yaji matukar farin ciki bisa wannan nasara, shine ma har ya naɗa yusufu a matsayin galadiman kano, sannan ya tura shi neman Dan maje don ya yake shi da gagarumar runduna.
Galadima yusufu ya gwabza yaki sosai da Dan maje, wasu ma na ganin a hannunsa Dan maje ya rasu, amma tana iya yiwuwa ba a wajen yakin Dan maje ya rasu ba a shekarar 1870.
Shikuwa Sarkin Kano Abdullahi ɗan ibrahim dabo, ya rasu a shekarar 1882 yana kan hanyarsa ta zuwa sokoto ziyara a wani waje da ake kira 'karofi', daga nan ake masa lakabi da Abdullahi maje karofi.
Bayan ya rasu ne sai Sarkin kano Muhammadu Bello ɗan Ibrahim dabo ya hau karagar sarautar kano.
Shine wanda aka zarga da cewar tun daya hau mulki, ya soma sharewa ɗansa Muhammad Tukur fagen zamowa sarki. Wanda kuma rasuwarsa keda wuya yakin basasar kano ya ɓarke, tsakanin Sarkin kano Muhammad Tukur daya gaji mahaifinsa da yusufawa mabiya Galadima yusufu. Wanda shima daya rasu a Garko, sai Kaninsa Alu Babba zaki ya gajeshi, har kuma yazo yaci nasara akan Muhamad Tukur ya zamo sarki.
Daga baya kuma, sai turawa suka zo kano a lokacin sarki Alu, inda suka kwace kano gami da naɗa kaninsa wambai Abbas ya zamo sarki.
Karshen wannan rubutu kenan da yardar Allah.
Assalamu Alaikum.

No comments:
Post a Comment