Wednesday, 6 December 2017

TARIHIN JHADIN DANFODIO A KANO 2

TARIHI: YADDA JIHADIN FULANI YA KASANCE A KANO (1803-4)

Kashi na biyu.

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
      08060869978
 
  Sarkin Kano Alwali ya aike da Mallam Dan Zulni'ima, jakadan kardawa da Mallam Hayu, da Zayyan Al'arabi ga musulmai masu hijira a Kwazzabon 'yarkwando domin ayi dulhu dasu, a tare dasu akwai wasikar Sarki garesu.
   Koda Masu hijira suka karɓi waɗannan baki, sai sukayi shawara a tsakaninsu, daga bisa suka yanke hukuncin cewa matsawar Sarki Alwali nadon sulhu, sai dai shima yayiwo hijira izuwa garesu, yazo su bautawa Allah shi kaɗai babu shirka, in yaso lokacin da Allah ya basu ikon soma jihadi izuwa sauran sassa, to zasu kara tabbatar masa da mulkin Kano.
   Abinda akayi kenan, basu bada wata takarda a rubuce ba sai wannan sakon na baki.
  Akan hanyar dawowar jakadun sarki Alwali nema har Jakadan Kardawa Mallam ɗan zulni'ima ya rasu sakamakon ciwon ciki daya turnukeshi saboda tsananin tsoron abinda wannan lamari zai haifar.
   Sa'ar da jakadu suka komo Kano, sai Sarki Alwali ya nemi su bashi amsar takarda daga masu hijira, amma sai suka sanar masa sakon baki kaɗai aka basu. Sannan suka labarta masa sakon.
  Anan ma sai Sarki Alwali ya tattara manyan fadawa da malumma, ya nemi shawararsu. Ance anan ne wani babban masani mai suna Abdulkadir yace waɗancan mutane jahilai ne, don haka kada abiye musu.
    Ai kuwa sai duk sauran malumman Musulunci na wurin suka amsa da cewar sam basu taɓa jin wani Annabi mai suna futi, ja'o'je ko Dabo ba. Don haka kada a amsa kiransu.
  A karshe sai shawara ta tashi akan cewa za'a nemi tallafin manyan mayaka, mafarauta da makiyaya, da sauran kabilu makusanta misalin buzaye, da kanuri domin yakar waɗancan mutane.
   Amma fa sai da Sarki Alwali ya kara tambayarsu da cewa "kun amince da wannan shawarar?" Dukkansu sukace sun amince. Sannan kowa ya watse..
 Kunji yadda aka dulmiyar da Sarki Alwali.
    YAKIN DAUKAKA MUSULUNCI, DA SOMA YAKIN JIHADI
Sarki Alwali yayi ganganko kwarrai da gaske. Aka tara dukkan mayaka daga dukkan sassa, gabas da yamma, kudu da arewa.
  Sai da aka tattara dakarun da kai kace k'asa ba zata iya ɗaukar suba.
  Gashi kuma a kullum mutane sai sulalewa suke izuwa kwazazzabo suna kai chaffa gami da karɓar musulunci. To amma da labarin yaki ya gama gari, sai mutane suka dakata suna masu cewar bari muga yadda yak'in zai kaya.
   Sarkin Dawaki Ali sarki Alwali ya naɗa jagoran wannan runduna. A wannan rana hakika an tara mayaka mashahurai, masu ɗauke da muggan makamai, bindigogi da harsasai, takubba da kibau, da kayayyakin rushe gini. Saboda tsammaninsu zasuyi fata-fata da kwazazzabon 'yarkwando ne da duk abinda ke cikinsa.
   Sarki Alwali ya bada umarnin a halaka duk namijin da aka tarar  a wurin koda kuwa jariri ne, matayensu kuwa a maishesu bayi, sannan a kamo shugabansu.
    Daga nan sai runduna ta mika, ana tafe ana kiɗe-kiɗen ganguna da tambura, mayaka na kirari da kuranta kawunansu .
   Tun kafin isowarsu ne labari ya riske masu hijira a bisa wannan gagarumar tawagar mayaka dake zuwa garesu. Don haka sunyi iya iyawarsu domin katange kansu daga wannan sharri dake tunkaro su, amma abin ya faskara.
   Wani da ake kira murnaji ya hau saman bishiya yana hange, abinda kurum yake iya ganowa itace k'ura data tokare sama, sai kuma sadaukai da baya iya ganin karshensu. Ai kuwa da sauri ya sauko dayana mai sanar da 'yanuwansa.
  Koda jin haka sai hankalin kowa ya tashi, mata suka shiga koke-koke suna faɗin shikenan karshensu yazo, mazaje kuwa da yawansu duk guiwowinsu sunyi sanyi, har sun fara tsammanin mutuwa.
   Shugabansu kaɗai akan iya cewa bai karaya ba, domin yana da dakakkiyar zuciya, da kuma zurfi wurin imani da Allah. Ya gamsu cewar Allah zai taimakesu a wannan yaki, don haka sai ya mika lamura ga Allah.
   Tun daga nesa rundunonin biyu suka shiga harbin junansu, da kibbau da bindigogi.
   Da yake gidajen masu hijira acikin kwari suke na wannan kwazazzabo, haka Barde Bakure ya jagoranci rundunar wasu mayaka suna kone gidajen su tun daga farko har saida suka riski tsakiyarsu. Wani jarumi ya sanar da Barde cewar ai nanne tsakiyar gidajen masu hijira. Barde yayi kuwwa da kururuwa, yace da dakarunsa "ku k'one komai dake nan kurmus".
   Hakika sadaukai da dama sun mutu a wannan rana. Yaki yayi tsamari. Kuma da fari an soma yiwa masu hijira gagarumar ɓarna. Amma da Allah ya kawo taimakonsa, sai masu hijira suka tarfa dakarun Sarki Alwali a tsakiyar kwari, suka hausu  da kisa.
   Daga bisani da dakarun Alwali sukaji babu dama, tilas suka nemi guduwa, suka bar dukiya da kayan faɗa masu ɗumbin yawa anan.
 A wannan yak'i ne Dantunku daga rundunar da Sarki Alwali ya turo ya karɓi musulunci sa'ar daya hangi nasarar da ake samu akansu. Ya tabbata wannan karfi bana masu hijira bane.
  Daga nan kuma sai ya juye yana kisan abokan tafiyarsu, kai kace daman can acikin masuƴ hijira yake.  
  Wannan shine gagarumar nasarar da Allah ya baiwa masu hijira. Inda sunansu ya ɗaukaka, martabarsu ta girmama.
 ( Watau dai abin na kama da nasarar da Allah ya baiwa Manzonsa S.A.W a yakin Badar)
  Tun daga nan kuwa sai mutane suka rinka yin ɗururuwar zuwa kwazazzabon 'yar kwando domin karɓar musulunci.
 Daga nan kuma sai aka soma yakin jihadi gadan-gadan, inda masu hijira suka soma far-wa garuruwan dake kusa suna kwace iko dasu...

No comments:

Post a Comment