TARIHI: YADDA JIHADIN FULANI YA KASANCE A KANO (1803-4)
Kashi na Uku.
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
KANANUN YAK'UNA
Akwai maganar yak'in cinye garin Kabo, inda Musulmai masu jihadi suka gwabza yaki tare da kwace iko da garin, suka kama fursunonin yaki.
Sannan an gwabza yaki na kwace garin Masanawa, a nan ma masu jihadi sun samu damar kwace garin tare da kama fursunonin yaki masu yawa, amma daga baya sai aka 'yantar dasu.
Sai kuma yakin kama garin Goɗiya (goɗiya ta ɗan tama mai gezar alharini, garin da ba'a iya cinsu da yak'i) wanda shugabanta Dan Tama ya kori masu jihadi da fari, ya rarake su tare da kwace wasu garuruwan da suka fara kamawa. Amma kwana ɗaya da haka, sai masu jihadi suka sake koma masa da yaki, suka kuwa samu nasara akansa tare da kone garin. Ya gudu dashi da sadaukansa.
Nan da nan kuwa labari ya karaɗe kasar Kano cewar an cinye goɗiya da yaki, saboda sanin karfin ta da girman kafin da garin ke dashi game da yaki.
Shikuwa garin Garun Mallam, mika wuya sukayi ga masu jihadi, don haka ba'a gwabza yaki dasu ba.
Ance shugabansu mai suna Turmi ya karɓi musulunci, sannan ya shiga cikin masu jihadi an rink'a zuwa yak'i dashi, daga bisani kuma aka naɗa shi shugabancin garin Bebeji yayinda Gyanako ya gudu daga garin izuwa garin Kura don neman mafaka.
Yak'in kama garin Karaye ya auku ne a wata ranar Jummu'a. Malam Danzabuwa ne kwamandan masu jihadi a ranar, kuma hakika sun gamu da turjiya da asara gagaruma daga hannun dakarun masarautar Karaye. Sadaukan masu jihadi da dama sunyi shahada a wannan rana. Sai kuwa suka ɗauki lamarin a matsayin jarabta daga ubangiji.
Bayan an fatattako masu jihadi daga Karaye, kashe gari ne kuma aka gwabza yakin Arɗo Sabti.
Shi Arɗo Sabti, bafullatani ne gwarzo dake cikin masu jihadi. Kuma yadda yakin ya samo sunansa shine, sa'ar da masu jihadi suka baro Karaye a sukwane, ashe akwai wasu dakaru da sukai musu kwanton ɓauna, ai kuwa sai mahara kurum suka gani sun hau su da kisa.
ƁNan fa abin ya haɗar musu, ga waccan rashin nasara, ga kuma yakin bazata daya sake faɗo musu.l.
Anan ne aka sake gwabza kazamin yaki, Arɗo sabti ya nuna matukar Jarumta a wannan yakin, daga bisani kuma ya rasa ransa a yak'in (Allah yajikansa amin).
Anyi wannan babu jimawa sai watan Ramadan ya shiga, don haka sai masu jihadi suka yi shawarar tsagaitawa da yaki har sai bayan karamar Sallah.
YADDA FULANI MASU JIHADI SUKACI GARIN KARAYE DA YAKI, DA MUSULUNTAR MALLAM JATAU NA ZAZZAU.
Da yake masu jihadi sun san cewa matsawar suna kasar kano, baza'a taɓa kyalesu ba, batare da sun gwabza yaki a watan Ramadan ba, don haka sai suka barta izuwa yamma .
A watan shawwal masu jihadi suka riski garin Bunga, suka yada zango acan. Daga baya suka karasa Kumasi (ta kasar Ghana).
Bayan sun huta, sai sukayi shiri, suka taso izuwa kano.
Ance sun biyo ta Karaye, suka sauka da niyyar shan ruwa a wani tafki, amma sai dakarun karaye suka far musu da hari.
Ai kuwa a bakin tafkin nan aka gwabza yaki tun safe har yamma sakaliyan, inda aka samu nasara akan dakarun karaye.
Masu jihadi na wannan wuri da dare bayan sun kori dakarun karaye, sai kuma Barde Bakure da Dan Tama sarkin Goɗiya suka sake zuwa da dakaru da niyyar yiwa masu jihadi kisan gilla, amma sai akai rashin sa'a wani cikinsu ya harba bindiga, nan-da-nan kuwa masu jihadi suka farga, tare da soma shirin yaki. Kafin kace haka sabon yaki ya sake rinchaɓewa a wurin.
Allah cikin ikonsa ya baiwa masu jihadi nasara, har suka samu damar halaka Barde Bakure a wurin, sauran runduna kuma ta warwatse kowa ya ranta ana kare,suka bar dukiya da kayan faɗansu anan.
Kwana uku da faruwar haka sai masu jihadi sukaci karo da Mallam Musa yana tafiya shi kaɗai, (Wanda ya zama sarkin zazzau a shekarar 1808) a wurinsa kuma suke samun labarin cewar sarkin Zazzau Jatau da mutanensa sun karɓi musulunci, har kuma suna bukatar a tura musu masani wanda zai koyar dasu addini.
Aikuwa sai akai shawara, akace a tura Mallam Danzabuwa da wasu mutane su tafi zazzau don koyar da Sarki jatau da mutanensa musulunci.
Haka kuwa akayi, tunda ance sa'ar da Mallam Danzabuwa ya riski zazzau, ya tararda sarki Jatau zaune bisa kan karagar mulki a fadarsa, yana sanye da rawani irin na mabiya sunnah (ba irin rawanin da sarakunan hausa sukeyi ba a baya). Ya karɓesu hannu bibbiyu, yana mai cewa "ayau, ni mabiyin sunnah ne".
Ragowar mutane kuwa sai sukaci gaba da yakin su na jihadi izuwa can arewacin kano (daga kasar karaye, suka keta kabo, gwarzo da shanono izuwa yankunan tofa, ɓagwai da bichi).
Sai dai duk waɗannan yakuna an gwabzasu ne a yammacin kano, a lokacin da gabashinta kuma ke gwabza nata yakin kwatankwacin irin wannan, tunda acan ne Mallam Bakatsine ya kafa runduna tare da fafata yaki a gabashin kano dama wasu kasashen makwabta irinsu Bauchi.
Saboda haka, bari muji yadda yaki ya kaya a gabas da kudancin kano, inyaso sai mu komo arewaci da yammacin kano, tayadda zamu haɗu a lokacin da fulani suka karɓe iko ga ɗaukacin kasar kano.
MALLAM BAKATSINE DA JIHADI A GABASHIN KANO.

No comments:
Post a Comment