Wednesday, 6 December 2017

TARIHIN KASUWANCI A KANO 4

TARIHIN KASUWANCI A KANO

  Tsakure daga littafin 'Kano cibiyar Kasuwanci ta Africa' wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo (Allah yajiqansa da Rahama ya wallafa).

  Daga Sadiq Tukur Gwarzo

 Kashi na huɗu
   Kasuwa dai wurin haɗuwa ce ta dukkanin mutanen gari ko alkarya, wacce take samar da kayayyakin amfanin jama'a na yau da kullum. A zamanin-da, kasuwa na zamowa a matsayin hanyar sadarwa ko cibiyar watsa labaran da suka shafi jama'ar gari.
  Anan kasar hausa, wurin kasuwa yakan zamo na wucin gadi, wanda za'0a iya zuwa lokaci zuwa lokaci, ko kuma na din-din-din.
  Kasancewar Kano a tsakiyar kasar Hausa tun asali, yasa har abada take alfahari da manyan kasuwanninta a tarihin harkar kasuwancin kasar hausa.
  Tsofaffin ksuwanni da suka fara kafuwa a cikin birnin kano sun haɗar da kasuwar kurmi, kasuwar sabon gari, kasuwar Rimi. Daga nan sai irinsu Kasuwar kwari da kasuwar 'Yan awaki, kasuwar kofar wambai da sauransu.
   A shekara ta 1445 miladiyya akace Sarkin Kano Abdullahi Burja, ya kafa sabuwar doka akan masu tallan bayi maza da mata, inda yace su daina yawo suna wahalar dasuƴ, su daina dukansu wajen talla acikin birni, sai dai su fita can wajen gari kudu da tsohuwar unguwar Mandawari domin akwai manyan bishiyoyi masu inuwa a ko ina a wurin, su rika zama suna saye da sayarwar bayin.
   Wannan wurin shine gabas da ofishin wakilin Yamma. Yann nan juma har yanzu a unguwar Magashi, sai dai yanzu gidaje ne a wurin. Shekaru 570 kenan.
   An kafa kasuwar kwari a zamanin sarkin kano Muhammadu Rumfa, shekara ta 1463 miladiyya, amma ance akwai kasuwar KARAFKA wadda ta wanzu tun shekara ta 1438.
   An sake gina kasuwar Kurmi a shekarar 1912 miladiyya da kayataccen ginin k'asa irin na wancan zamanin mai rufin k'yami. An ɗauko k'yamin ne daga Tudun wadar ɗan kadai ta gabashin kano, waɗanda suke ɗaukowar kuwa ɗaurarru ne 'yan kurkuku, kuma a kafa suke zuwa su ɗauko, yayin da masu gadinsu ke biye dasu bisa jakuna suna ko-rasu.
   Kamar yadda Tarihi ya nuna, ita wannan kasuwa ta samo sunanta ne daga Rafin Jakara inda mutane suka fara zama a kano suna yin farauta a wani kurmi kusa da rafin, don haka har yanzu sunan Jakara bai ɓata ba, yayin da kasuwar kurmi kuma ta zamo anan kusa da unguwar jakarar.
  A zamanin da wannan kasuwa ta kafu, an soma kakkafa rumfunan zana ne a cikinta domim aiwatar da harkar kasuwanci, kuma an tsara yadda kowanne mai siyar da kaya zai zauna a rumfarsa don gudanarwar kasuwancin.
   Daga baya ne Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya bada Umarni aka soma gine-ginen daɓe da siminti acikinta. Ance wasu turawa watau Moge, Borkon, da Dogon Lamba sune suka tsara gine-ginen domin sarrafa harkar kasuwanci a cinin kasuwar.
  A zamanin mulkin sarakunan kasar hausa kafin zuwan turawa, mutane basa fitowa da kaya barkatai a rumfar kasuwa, sai dai idan bako yazo yanason siyan kaya masu yawa a tafi dashi gida abashi iya abinda yakeso ya tafi dashi kasarsa.
  Amma dai an samu cewa kasuwar kurmi ta rinka karɓar fatake daga manyan garuruwan kasar hausa da makwabta, harma da larabawa. Kayan koli kuma shi akafi siyarwa acikinta.
  A wata faɗar kuma ance, tun zamanin sarkin kaɓo Muhammadu Rumfa akwai kasuwar kurmi. Ance yana da shekara 24 bisa gadon sarauta yayi hawa, ya tafi kurmin jakara tare da hakimansa da bayi da kuma ma'aikata ɗauke da kayan aiki, sannan ya nuna tun daga tsakiyar fadamar jakara, ɓangaren gabas, akayi ta saran itatuwa har sai da aka samar da sarari gagarumi. Daga nan da yake ance shi gwanin bin tarihi ne, kima ya samu cewa a lokacin Sarkin kano gijimasu, madakin kano ke kula da harkar kasuwanci, sai shima ya naɗa madakin sa domin yayiwa kasuwar gine-gine tare da haɓaka ta. Tun daga wancan lokacin kuwa kasuwar ke haɓaka, har zuwa yau..
  Wannan shine abinda ya samu dangane da tarihin kasuwanci a kano.
 
 


No comments:

Post a Comment