Wednesday, 6 December 2017

TARIHIN KASUWANCI A KANO 3

TARIHIN KASUWANCI A KANO

  Tsakure daga littafin 'Kano cibiyar Kasuwanci ta Africa' wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo (Allah yajiqansa da Rahama ya wallafa).

  Daga Sadiq Tukur Gwarzo

 Kashi na uku

A farkon shekara ta 1496 miladiyya, Sarkin kano Muhammad Rumfa yayi waɗansu bakin fataken Turawa da suka ɓullo daga Kumasi ta kasar Gwanja (Ghana) can yamma da Ilorin.
  A harshen hausa muna kiransu da suna PATOKI, amma ainihin sunansu Portuguese, ma'ana mutanen kasar Portugal. Babban cinikin waɗannan turawan shine fataucin bayi, sune turawan farko da suka kawo gyaɗa garin kano.
   Sukan sayi bayi maza da mata a kasuwa. Su kƴma sukan siyarwa da kanawa gyaɗa. Yayin da suka kammala sayar da gyaɗar tasu, sai suka shirya bayin da suka siya, suka tashi suka koma ta gwanja, sannan sukayi kudu suka riski birnin Ankara wanda yake a kasar Turkey ayau, sannan suka hau teku da bayinsu sukayi yamma sosai har zuwa wata kasa mai suna Brazil wadda ke jikin Amurka ta Kudu. Anan ne kasuwar da suke siyar da bayin nasu take.
   Haka kuma, a shekara ta 1497, waɗansu larabawa sunzo kano daga kasar Casabalanca ta Morocco. Sun sauka a wurin 'yan uwansu dake zaune anan dandalin Turawa cikin birnin kano.
  Daga cikin gaisuwar da Waɗannan larabawa suka kawowa Sarki Rumfa, akwai Saihanai babba da karami. Ance sarki ya tambayesu menene sunan wannan mazubin ruwan? Sai sukace masa sunansa Saihan. Daga nan sai ya kira wani bawansa mai suna Santali, yace masa ga waɗannan saihanai nan, ɗaya ka kaimin gida saboda alwala, ɗayan kuma ka rinka bina dashi da ruwa koda zan bukace shi. Tun daga nan ne sunan Santali ya zama sunan Sarauta.
  A dai cikin wannan shekara ne akace Fataken nan yan kasar Girka sun sake komowa kano, inda sarki ya sake zaunar dasu a unguwar da Rijiyar 'Yar Akwa take, watau masaukinsu na farko kenan.
  Ance sune suka kawo wani irin kuɗi na azurfa nano, a jikin kuɗin an zana suna kamar haka:-
    MARY
TREESA DOLLAR
Da irin waɗannan kuɗin ne kuma fataken suka rinka sayen bayi a kasuwa, da kiraza, albasa da sauran kayayyaki. Irin waɗancan kuɗin ne kuma mata suka rinka hudawa suna ratayawa yaransu a wuya. Wata macen takan haɗa kamar uku ta ɗaura, watakuma biyar, gwargwadon arzikinta. A wannan zamanin, sarkin Kano muhammadu Rumfa nada kimanin shekaru talatin bisa gadon mulkin kano.

No comments:

Post a Comment