Thursday, 26 August 2021

ASALIN HARSHE

 RANAR HAUSA TA 2021: Asalin Harshe

SADIQ TUKUR GWARZO

  Harshe na nufin adabin yare da ake amfani dashi wajen sadarwa tsakanin al'umma, wanda ya ƙunshi fitar da sautin kalmomi a bayyane ko a rubuce.

  Farfesa Greg Downey, da sauran masana irin sa na fannin ilimin tarihin wanzuwar ɗan adam a duniya da yadda ya kasance yana rayuwa tun fil-azal, 'Anthropology', sun gamsu da cewa har yanzu ba a san takamaimen dalilin soma maganar ɗan adam ba musamman dube da ƴan uwansa na kusa a ƙwayoyin halittu irin su birrai da gwaggwonin sa waɗanda suke ɗauke da kusan duk abinda ɗan adam yake dashi na halitta, amma su basa iya magana. 

   Don haka bincike ya yanke cewar wasu ɓangarori da aka gani a ƙwaƙwalwar ɗan adam waɗanda duk da cewa akwai shigen su a ƙwaƙwalwar gwaggon biri, amma sun fi haɓaka a na ɗan adam, ke da alhakin baiwa ɗan adam wayewar furta magana da amfani da harshe, waɗannan ɓangarorin sune 'Brocas area, da 'wernick area'.

SOMA YARE A DUNIYA

Hasashe dai na ilimi ta nuna cewa an soma amfani da harshe kimanin sama da shekaru 150,000 da suka gabata. Haka kuma binciken adadin harsuna da masana suka yi yana nuni da cewa yarukan da ake amfani dasu a duniya sun kai kimanin 6000, sai dai binciken wasun su na nuni da samuwar su a wasu shekaru ƙasa da lokacin da aka ƙiyasta soma yare a duniya.

Zantukan da aka rinƙa samu a jikin kogunan duwatsu ya ƙara zama hujjar cewar harsuna da yawa sun samo asali ne daga tsatso ɗaya, watau harshe ɗaya.

Daga ina Harshe ya samo asali?

  Harshe ya soma ne a wannan duniyar kaɓar yadda aka faɗa tun da farko kimanin shekaru 150,000 da suka gabata yayin da halittun zamanin suka haɓaka wata wayewa ta soma amfani da shi (harshe) wajen sadarwa a tsakanin su. Amma sanin asalin harshen da aka soma amfani da shi a wancan zamanin abu ne da har yanzu masana ke bincike akai, wasu ma na ganin ba abu ne mai yiwuwa da za a iya samu ba.


MENENE ASALIN DUKKAN HARSUNA?

Masana da yawa na cewar asalin dukkan harsuna sun samo ne daga guda ɗaya tilo, sannu a hankali suka rinƙa rarrabuwa. To amma da yake da akwai ra'ayin masana daban daban akan haka, zai fi kyau mu ji wasu daga ciki kamar yadda yazo a littafin 'Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa' wanda Rabiu Zarruk, Abubakar Kafin Hausa da Bello S Alhassan suka wallafa a shekarar 1990:-

1. Ra'in Bow-Wow

Dangane da labarin da ake kira ra'in bow-bow, kalmomin da muke amfani da su a harsunanmu na yau, sun faro daga sauti ne irin na halitta. Wai lokacin da dan Adam ya fara magana, yana ƙókarin misalta sauti ne na dabbobi da tsuntsaye da sauran halittu. Saboda haka, in mutum ya ga wani abu yakan yi magana ne, bayan ya riya wani sauti a zuciyarsa. Sautin da yakan riya kuwa, shine kamar kukan wani tsuntsu, ko motsin wata dabba in tana tafiya, ko tana gudu,ko motsin ganye yayin da ake guguwar iska, ko wanin wadannan. Wai haka ne abubuwa suka sami sunayensu a kowane harshe.

2. Ra'in Poob-Pooh

Ra'in pooh-pooh shigen na bow-wow ne. Shi yana cewa, duk kalmomi mafarinsu razana ce ko mamaki. Larurar magana ce take kama dan Adam yayin da wani abu ya razana shi ko ya ba shi mamaki. A lokacin nan, duk abin da ya fito daga bakinsa ya zama sunan wani abu. Saboda haka, a wannan ra'in kalmomin motsin rai, kamar a'aha! assha! haba! kash! tir! wai! wayyo! yawwa! da sauransu, su suka fi kowanne tsufa a harshe.

3. Ra'in Ding-Dong

A wannan ra'in, kwatancen kamannin abubuwa ko motsinsu shi ne asalin kalmomi a harshe. Watau da farko dan Adam ya yi kokarin samun lakabin abubuwa ne dangane da kamanninsu ko motsinsu. Saboda haka a nan, amsa-kama su ne kalmomin farko a harshe.


4. Hasumayar Babila

A wannan labarin cewa aka yi, can asali, duk 'yan Adam harshensu daya ne.

Jikokin Annabi Nuhu sun gaji duniya bayan Ruwan Dufana. Sun yadu ƙabila-ƙabila, amma a sannan harshensu daya ne. Daga baya, wasu 'masu taurin kai a cikinsu suka yi tunanin gina babban gari mai suna Babila. Bayan sun gina garin sai kuma suka ga cewa za su iya gina hasumayar da za ta kai su sama. Da hasumayar ta yi nisa sai ta rushe. Shi ke nan, duk wanda ya faddo daga hasumayar dą wanda ke cikin garin sai bakinsa ya juye. Daga nan- ne mutane suka rarrabu kowa harshensa daban.

5. Ajiyar Allah

Ga abin da wannan labarin ke cewa: Kamar yadda Allah ya halicci zanzaro da ilimin gini, ya ba ƙudan zuma baiwar tattara zuma dága furanni, to hakanan ya ajiye wa dan Adam harshe. Dalilin wannan baiwa, duk inda mutum ya girma Sai ya tashi da harshen wurin. Saboda haka, Allah ya ajiye harsuna ne a wurare daban-daban na duniya. Saboda haka tun can farko idan al'ummá ta zauna a wani wuri shi ke nan, sai ka ji tana kiran abubuwa da sunayen da aka ajiye a wannan wun. (Asalin labarin dai shi ne kamar yadda yazo a littafi mai tsarki Alkurani cewa, tun lokacin da aka halicci Annabi Adamu aka sanarda shi sunayen dukkan abubuwa).

Tammat bi Hamdullahi

(Da fatan Allah ya bamu zama lafiya amin)





Monday, 9 August 2021

BINCIKE A DUTSEN BAƘOSHI

 BINCIKE A DUTSEN BAƘOSHI

Sadiq TUkur Gwarzo

Asalin Garin Dutsen Baƙoshi

Abisa Tarihi, wannan yanki ya jima sosai yana ɗauke da mutane masu rayuwa a wuraren ta yadda zai yi wuya a iya gane lokacin da aka soma zama a yankin.

Mutane sun rayu a wuraren a warwatse, har daga baya wayewa tazo musu na haɗa kai da fuskantar matsalolin zamanin, suka kafa gari.

Ɓur-ɓur Bamaguje ne da yayi zamani da Dala, shima ya zauna a saman wani dutse wanda dake yammacin Tsaunin garin Baƙoshi, ko kuma ace mazaunin Aljanna Mararaka. Ance suna da siffa mai girma wadda har sukan iya girgiɗe bishiyar giginya su saɓo ta a kafaɗa, ko kuma su girgiza su ciro ɗan giginya su yi jifa dashi.

Hasashe ya nuna garin ya soma kafuwa ne a bayan tsaunin garin Dutsen ɗan Baƙoshi shekaru sama da dubu  da suka gabata. Har zuwa yanzu kukoki na nan a kufan garin masu nuna wanzuwar gari a wajen.

Yaƙe-yaƙe ne silar da mutanen garin suka baro tsohon gari tare da dawowa inda garin yake a yau. A zamanin wani mai suna Baƙoshi shine sarki. Sai jama'ar garin suka kafa gari tare da yi masa ganuwa domin samun tsaro daga mahara.

Akwai wani dutse a kofar Fadar garin na yanzu wanda akace Baƙoshi ne ya ɗauko shi a saman kansa ya kawo kofar gidan sa, kuma nan ne wurin zaman sa inda yake ganawa da jama'a har zuwa rasuwar sa.

   Sunan Baƙoshi ya fito a cikin fadawan Barbushe, a littafin Kano chronicle, da cewa tun a lokacin a duk shekara mutane na niƙar gari zuwa gindin dutsen Dala domin yiwa Aljana Tsumburbura bauta.

Don haka muna iya auna shekarun kafuwar sabon garin kenan da zamanin Barbushe na saman tsaunin Dala.

Marina

Akwai tsohuwar marina dake saman dutse a zangon garin, baya da ganuwar garin kenan, har yanzu ana iya ganin raɓukan baba da katsi waɗanda akayi amfani dashi.

Maƙera

Akwai ɓurɓushin maƙera da Dr Mahmud ya hango a saman tsaunin garin Baƙoshi, masanan sun tsinci uwar maƙera a saman tsaunin wamda ke tabbatar da wanzuwar maƙera masu sarrafa ƙarafa a wajen. 

Falalen Mararaka

Falalen Mararaka, Wuri ne mai kyawun gani, yana ɗauke da duwatsu masu ƙayatarwa, kuma anan ne gidan Aljanna Mararaka yake da iyalinta. Har yanzu masu bori da tsubbu suna zuwa domin neman taimako daga gareta. Akwai ramuka da suka yi akan dutsen inda suke tsima magunguna domin bayar dasu ga jama'a, akwai turaruka da akan iya gani waɗanda masu neman biyan buƙata daga Aljanna mararaka suke ajiyewa hadiya zuwa gareta.

Daman tun da jimawa mun samu labarin akwai alaƙa tsakanin aljana Mararaka ta saman dutsen Baƙoshi da kuma Aljanna Tsumburbura ta saman tsaunin Dala, dukkansu ance bauta musu ake yi, to amma salon bautar da ake yi garesu ya sha bam-bam da juna.

  Ita Aljana Mararaka dake dutsen ɗan Baƙoshi har yanzu tana da matukar tasiri a wannan yanki, ana ganin ayyukanta kuma ana neman taimakonta saɓanin Aljanna Tsumburbura ta saman dutsen Dala wadda ko kaɗan ba a jin ɗuriyar ta.

Tsohon Masallacin Dutsen Baƙoshi

A tsohon ginin masallaci dake kofar fadar garin, ginin hausa na tubali da maginam dauri suka gina. Katangar masallacin mai kauri ce, a wani wajen ta haura mita ɗaya, a wani wajen kuma ta gaza mita ɗaya da kaɗan. Ana hasashen tsufan masallacin na ita tasamma shekaru 500, wanda hakan ke nuna jimawar addinin musulunci a garin duk kuwa da cewar bai hana mu'amala da iskokai ba.

SARAUTA

Daga kan Baƙoshi aka soma shugabanci a wannan gari, don haka da ɗansa ya gajeshi sai ake kiransa da 'Ɗan Baƙoshi'  Kuma har zuwa yau, da wannan suna ake kiran dagacin wannan gari mai tsohon tarihi.

Wednesday, 4 August 2021

ADABIN WASAN KWAIKWAYO

 WASAN KWAIKWAYO

Wannan na daga cikin rabe-raben adabi, gundarin sa kamar  ya samo ne daga kalmomin 'drama' ko 'play' na turanci, ma'anar su bai wuce 'aikata shiryayyen wasa' ba musamman a dandali  domin nishaɗantarwa da ilimantar da masu kallo.

Ana gabatar da wasan kwaikwayo a dandali, talbijin, radiyo ko duk wani taron jama'a. Babban abu dai a game da shi shine ya zamo an yi ne ga wasu mutane waɗanda suke kallon sa kai tsaye ko kuma suke sauraro.

Masani Brion Crown  ya fassara wasan kwaikwayo da cewa "Wasan kwaikwayo hanya ce ta gabatar da abubuwan da suka shafi rayuwa a cikin nishaɗi da ban dariya tare da motsa sassan jiki da kuma rakiyar sauti".

Soma taskance wasan kwaikwayo a duniya ya samo ne tun a zamanin Masani Aristotle na ƙasar Girka (c. 335 BCE), kuma tun daga wancan zamani an gamsu da cewa kowacce ƙabila tana da yanayi da siga na gabatar da wasan kwaikwayo ga al'ummar ta.

A wani yanayin, ana iya cewa wasan kwaikwayo ya dogara ne kachokan bisa kalmomin da ake musanyawa a cikinsa, waɗanda mafi akasari ake shirya su cijin hikima domin zaburar da masu kallo/sauraro bisa halayya, ayyuka, ko shirye-shirye na masu gabatar da wannan wasan kwaikwayo. 

   

ADABIN ZUBE

 RUBUTUN ZUBE

  Rubutun zube wani jigo ne ma adabi wanda ya tattara mabanbantan abubuwa kama daga rubutattun labarai, hikayoyi, da sauran su.

  Mallam Yakubu Musa Muhammad ya rubuta a littafin sa 'Adabin Hausa' cewa "Zube; ya haɗar da tatsuniya, hikaya, maganganun azanci, azancin magana da sarrafa harshe.."

  Akan raba Adabin zube izuwa rubutattun Tatsuniya, Labarun Gargajiya, Barkwanci da Tarihi, ko kuma a rarraba shi gida uku izuwa Almara, Ƙissa da Hikaya.

*Azancin Magana na nufin wata magana da akeyi mai ma'ana saɓanin gundarin maganar, misalin karin magana (i.e, Kowanne Allazi..) , zambo (i.e, mai bakin zalɓe..), ba'a (i.e hassada bata hana samu), habaici (i.e, yaro bari murna karen ka ya kama zaki) da sauransu.

* Sarrafa harshe ya tattara zantukan azanci da hikima waɗanda ake amfani dasu wajen siffantawa, ƙawatawa, bayyanawa da sauran su.

* Ƙissa: maanar ta shine wani jinsin labari na gaskiya wanda babu sofanen ƙarya a cikinsa musamman wanda ya shafi addini. Missali, maimakon ace labarin Annabawa sai a kira shinda Ƴissoshin Annabawa.

*Almara: maanar sa shine, jinsin labari wanda yake shiryayye domin janyo hankulan mutane, a wasa musu ƙwaƙwalwa ta hanyar samar musu da wata gagarumar matsala a cikin labarin wadda take buƙatar nazari da tunani wajen warwareta.

*Hikaya: Maanar ta shine jinsin labari na gaskiya amma wanda aka yi masa ƙari da wasu abubuwa don ƙawatashi ko zuzutashi. A wani fannin kuma akan samu labarai na hikima da ake kira hikayoyi waɗanda suka ƙunshi dabbobi da tsuntsaye waɗanda ake bayar dasu domin koyawa alumma darasi.

Tatsuniya: Labarai ne ƙirƙirarru da ake bayarwa musamman ga yara domin koyar dasu halaye kyawawa da tunkuɗe su daga munanan halaye.

 

ILIMIN SANIN RUBUTACCIYAR WAKA

 ILIMIN SANIN RUBUTACCIYAR WAƘA

  Ita dai rubutacciyar waƙar hausa ta samu tasiri ne daga waƙoƙin larabci, domin kuwa ba a san ta ba sai da musulunci da ilimin larabci suka shigo ƙasar nan, watau musamman lokacin jihadin Shehu Usmanu.

   Tun daga nan har zuwa yau, idan aka bincika marubuta waƙoƙin hausa za a tarar ba zasu rasa wani tasiri na harshen larabci ko addinin musulunci ba.

   Wani abin ban sha'awa kuma shine, harshen Hausa harshe ne mai iya karɓar kowanne irin salo da harshen larabci yazo dashi, ya zauna daram kamar dama anan aka halicce shi.

   Bugu da ƙari, ma'aunin waƙar hausa rubutacciya da amsa amon ta duka irin na waƙoƙin larabawa ne, sai fa daga bisani ne mawaƙan hausa suka saɓa da irin waƙoƙin larabci, har ma aka samu sabbin jigogi waɗanda suka shafi lamuran yau da kullum.

    Abubuwan da ake sa rai aga sun tabbata kafin a hukunta cewa rubutacciyar waƙar hausa tayi yadda ake sonta guda 9 ne, amma na ƙarhen bai zama tilas ba. 

Ga abubuwan kamar haka:-

1. Buɗewa da rufewa da yabon Ubangiji da Salatin Annabi (S.A.W).

 Misali: Na fara da sunan Zuljalali maƙagin duniya,

   Ina salati ga Khairul Anami hasken idaniya.

2. Ma'auni; ta yadda za a iya yanyanke ta kuma baitocinta su zamo kai-da-kai.

  Misali: 

*Dawil:

 Mutum haka ma in yaga bashi da ko zare,

Ya kan roƙi Allah safe da daddare.

*Madid:

Ko ina, duk an sani kai ka mulki,

Duk ƙasar nan babu mai arziƙin ka.

*Da sauran su; kamar su Basiɗ, Watir, Kamil, Hazaj, Rajaz, Ramal, Mumsarih, Hafit, Muƙtabib, Mutaƙarrab, Muɗarid.

3. Waƙa ta kasance tana amsa amo, tana kuma da ƙafiya.

4. A shirya baitocin waƙa dai-dai da ɗangogin waƙa guda bakwai.

   Misali: Gwauruwa itace mai baiti ɗango ɗaya.

Ƴar tagwai mai ɗango biyu,

Ƴar uku mai uku,

Ƴar huɗu mai guda huɗu,

Ƴar biyar mai biyar,

Tahamsi mai shidda,

Sai Tarbi'i mai guda bakwai.

5. Ambaton jigon waƙa tun daga farkon ta.

  Misali: "Nayi shiri tsaf zan ja hankali,

                Akan mata masu yawon dandali".

6. Warwarar jigon waƙa

Watau a kawo ɗangogi waɗanda suka tafi dai-dai da jigon da ake waƙar akan sa.

7. Ambaton sunan mawaƙi da tarihin yin waƙar a ƙarshen ta.

8. Salon mawaƙin ya kasance yana da ƙarfi, watau yana yin bayani mai gamsarwa.

9. Gwanin ta da iya sarrafa harshe.

Sadiq Tukur Gwarzo ya ciro wannan bayanin daga littafin 'WAƘA A BAKIN MAI ITA' wanda kamfanim ɗab'i na NNPC ya wallafa a shekarar 1979.

MA'ANAR ADABIN HAUSA DA RABE-RABEN SA

 ADABI

  Sheshin Malami uban Malamai, Farfesa Abdulkadir Ɗangambo, ya kawo a littafin sa mai suna 'Rabe-Raben Adabin Hausa da muhimmancin sa ga rayuwar Hausawa' cewa kalmar Adabi ta samo ne daga kalmar 'al-adab' ta larabci. Ma'anar ta a larabce shine 'ɗa'a, fasaha, ko ƙwarewa'.

   To amma a hausance, ma'anar kalmar kamar yadda Farfesa Ɗangambon ya rubuta a wancan littafin shine "ya ƙunshi yadda al'adunsu (Hausawa), ɗabiunsu, harshen su, halayyar su, abincinsu, tufafin su, maƙwabtan su, huɗɗoɗinsu, da ra'ayoyin su da sauran abubuwa na dabarun zaman duniya don cigaba da rayuwa, kai har ma da abinda ya shafi mutuwa".

   Dalili kenan da akan kira Adabi da 'madubin rayuwar dan adam', domin ana hasashen da zarar ka kalli adabin al'umma, to zaka fuskanci yadda take.

  Don haka, adabi ya tattara bayani ne game da al'adu, rayuwa da fasaha ta al'umma.

  Wannan ne silar da ake nazarin rubututtuka, wakoki da sauran hikimomin ɗai-ɗaikun al'umma a manyan makarantu, ana yin hakan ne domin ƙwaƙulo ilimai na adabi dake jibge a cikin su.

   RABE-RABEN ADABI

1. Adabin Gargajiya

Shine adabin da Hausawan dauri ke da shi tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, wanda kuma nason sa ya biyo gar zuwa yanzu. Ga yadda ya rabu:-

A. Rubutun zube; wannan ya ƙunshi rubutu na Tatsuniyoyi, labarai, Almara, wasa ƙwaƙwalwa, ƙissoshi, wakoki da kaɗe-kaɗe da sauran su waɗanda aka taskance tun kafin zuwan turawa, misalin ayyukan Abdullahi Suka, Wali Ɗan Marna da Wali Ɗan Masani da sauransu.

B. Makaɗa

Sun rabu kaso da dama, misali:-

I. Makaɗan Fada: Misakin Ɗankwauro

II. Makaɗan jama'a: Misalin Dr Mamman Shata

III. Makaɗan Maza: Misalin Ɗan anace mai waƙar ƴan dambe

IV. Makaɗan ban dariya: Misalin Ƴan kama 

C. Kayayyakin kiɗan Hausawa sun haɗar da kayayyakin dokawa misalin ganga, kalangu, jauje, dundufa, da kayayyakin  gogawa misalin goge, kukuma, da kuma kayayyakin busawa misalin siriƙi, da algaita.

2. Adabin Zamani

Shine adabin da ya zowa Hausawa sabili da shigowar sabuwar  wayewa sanadiyyar mamayar turawan mulkin mallaka musamman wanda ya soma a farkon ƙarni na goma sha tara.

Ga yadda adabin ya rabu:

A. Rubutattun waƙoƙi

Misalin Rubutattun waƙoƙin Aliyu Na Mangi, Sa'adu Zungur, Khalid Imam, Murtala Uba 

B. Rubutun zube: misalin labarin littattafai irin su Magana Jari na Abubakar Imam, In da so da ƙauna na Ado Ahmad Gidan Dabino, Idan so cuta ne na Farfesa Yusuf M Adamu, Sihirtacce na Bala Anas Babinlata, Mace Mutum na Rahama A Majid 

B. WASAN KWAIKWAYO

Misalin littattafan wasan kwaikwayo irin su Zamanin nan Namu, Mallam Zalimu