BINCIKE A DUTSEN BAƘOSHI
Sadiq TUkur Gwarzo
Asalin Garin Dutsen Baƙoshi
Abisa Tarihi, wannan yanki ya jima sosai yana ɗauke da mutane masu rayuwa a wuraren ta yadda zai yi wuya a iya gane lokacin da aka soma zama a yankin.
Mutane sun rayu a wuraren a warwatse, har daga baya wayewa tazo musu na haɗa kai da fuskantar matsalolin zamanin, suka kafa gari.
Ɓur-ɓur Bamaguje ne da yayi zamani da Dala, shima ya zauna a saman wani dutse wanda dake yammacin Tsaunin garin Baƙoshi, ko kuma ace mazaunin Aljanna Mararaka. Ance suna da siffa mai girma wadda har sukan iya girgiɗe bishiyar giginya su saɓo ta a kafaɗa, ko kuma su girgiza su ciro ɗan giginya su yi jifa dashi.
Hasashe ya nuna garin ya soma kafuwa ne a bayan tsaunin garin Dutsen ɗan Baƙoshi shekaru sama da dubu da suka gabata. Har zuwa yanzu kukoki na nan a kufan garin masu nuna wanzuwar gari a wajen.
Yaƙe-yaƙe ne silar da mutanen garin suka baro tsohon gari tare da dawowa inda garin yake a yau. A zamanin wani mai suna Baƙoshi shine sarki. Sai jama'ar garin suka kafa gari tare da yi masa ganuwa domin samun tsaro daga mahara.
Akwai wani dutse a kofar Fadar garin na yanzu wanda akace Baƙoshi ne ya ɗauko shi a saman kansa ya kawo kofar gidan sa, kuma nan ne wurin zaman sa inda yake ganawa da jama'a har zuwa rasuwar sa.
Sunan Baƙoshi ya fito a cikin fadawan Barbushe, a littafin Kano chronicle, da cewa tun a lokacin a duk shekara mutane na niƙar gari zuwa gindin dutsen Dala domin yiwa Aljana Tsumburbura bauta.
Don haka muna iya auna shekarun kafuwar sabon garin kenan da zamanin Barbushe na saman tsaunin Dala.
Marina
Akwai tsohuwar marina dake saman dutse a zangon garin, baya da ganuwar garin kenan, har yanzu ana iya ganin raɓukan baba da katsi waɗanda akayi amfani dashi.
Maƙera
Akwai ɓurɓushin maƙera da Dr Mahmud ya hango a saman tsaunin garin Baƙoshi, masanan sun tsinci uwar maƙera a saman tsaunin wamda ke tabbatar da wanzuwar maƙera masu sarrafa ƙarafa a wajen.
Falalen Mararaka
Falalen Mararaka, Wuri ne mai kyawun gani, yana ɗauke da duwatsu masu ƙayatarwa, kuma anan ne gidan Aljanna Mararaka yake da iyalinta. Har yanzu masu bori da tsubbu suna zuwa domin neman taimako daga gareta. Akwai ramuka da suka yi akan dutsen inda suke tsima magunguna domin bayar dasu ga jama'a, akwai turaruka da akan iya gani waɗanda masu neman biyan buƙata daga Aljanna mararaka suke ajiyewa hadiya zuwa gareta.
Daman tun da jimawa mun samu labarin akwai alaƙa tsakanin aljana Mararaka ta saman dutsen Baƙoshi da kuma Aljanna Tsumburbura ta saman tsaunin Dala, dukkansu ance bauta musu ake yi, to amma salon bautar da ake yi garesu ya sha bam-bam da juna.
Ita Aljana Mararaka dake dutsen ɗan Baƙoshi har yanzu tana da matukar tasiri a wannan yanki, ana ganin ayyukanta kuma ana neman taimakonta saɓanin Aljanna Tsumburbura ta saman dutsen Dala wadda ko kaɗan ba a jin ɗuriyar ta.
Tsohon Masallacin Dutsen Baƙoshi
A tsohon ginin masallaci dake kofar fadar garin, ginin hausa na tubali da maginam dauri suka gina. Katangar masallacin mai kauri ce, a wani wajen ta haura mita ɗaya, a wani wajen kuma ta gaza mita ɗaya da kaɗan. Ana hasashen tsufan masallacin na ita tasamma shekaru 500, wanda hakan ke nuna jimawar addinin musulunci a garin duk kuwa da cewar bai hana mu'amala da iskokai ba.
SARAUTA
Daga kan Baƙoshi aka soma shugabanci a wannan gari, don haka da ɗansa ya gajeshi sai ake kiransa da 'Ɗan Baƙoshi' Kuma har zuwa yau, da wannan suna ake kiran dagacin wannan gari mai tsohon tarihi.
No comments:
Post a Comment