WASAN KWAIKWAYO
Wannan na daga cikin rabe-raben adabi, gundarin sa kamar ya samo ne daga kalmomin 'drama' ko 'play' na turanci, ma'anar su bai wuce 'aikata shiryayyen wasa' ba musamman a dandali domin nishaɗantarwa da ilimantar da masu kallo.
Ana gabatar da wasan kwaikwayo a dandali, talbijin, radiyo ko duk wani taron jama'a. Babban abu dai a game da shi shine ya zamo an yi ne ga wasu mutane waɗanda suke kallon sa kai tsaye ko kuma suke sauraro.
Masani Brion Crown ya fassara wasan kwaikwayo da cewa "Wasan kwaikwayo hanya ce ta gabatar da abubuwan da suka shafi rayuwa a cikin nishaɗi da ban dariya tare da motsa sassan jiki da kuma rakiyar sauti".
Soma taskance wasan kwaikwayo a duniya ya samo ne tun a zamanin Masani Aristotle na ƙasar Girka (c. 335 BCE), kuma tun daga wancan zamani an gamsu da cewa kowacce ƙabila tana da yanayi da siga na gabatar da wasan kwaikwayo ga al'ummar ta.
A wani yanayin, ana iya cewa wasan kwaikwayo ya dogara ne kachokan bisa kalmomin da ake musanyawa a cikinsa, waɗanda mafi akasari ake shirya su cijin hikima domin zaburar da masu kallo/sauraro bisa halayya, ayyuka, ko shirye-shirye na masu gabatar da wannan wasan kwaikwayo.
No comments:
Post a Comment