ADABI
Sheshin Malami uban Malamai, Farfesa Abdulkadir Ɗangambo, ya kawo a littafin sa mai suna 'Rabe-Raben Adabin Hausa da muhimmancin sa ga rayuwar Hausawa' cewa kalmar Adabi ta samo ne daga kalmar 'al-adab' ta larabci. Ma'anar ta a larabce shine 'ɗa'a, fasaha, ko ƙwarewa'.
To amma a hausance, ma'anar kalmar kamar yadda Farfesa Ɗangambon ya rubuta a wancan littafin shine "ya ƙunshi yadda al'adunsu (Hausawa), ɗabiunsu, harshen su, halayyar su, abincinsu, tufafin su, maƙwabtan su, huɗɗoɗinsu, da ra'ayoyin su da sauran abubuwa na dabarun zaman duniya don cigaba da rayuwa, kai har ma da abinda ya shafi mutuwa".
Dalili kenan da akan kira Adabi da 'madubin rayuwar dan adam', domin ana hasashen da zarar ka kalli adabin al'umma, to zaka fuskanci yadda take.
Don haka, adabi ya tattara bayani ne game da al'adu, rayuwa da fasaha ta al'umma.
Wannan ne silar da ake nazarin rubututtuka, wakoki da sauran hikimomin ɗai-ɗaikun al'umma a manyan makarantu, ana yin hakan ne domin ƙwaƙulo ilimai na adabi dake jibge a cikin su.
RABE-RABEN ADABI
1. Adabin Gargajiya
Shine adabin da Hausawan dauri ke da shi tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, wanda kuma nason sa ya biyo gar zuwa yanzu. Ga yadda ya rabu:-
A. Rubutun zube; wannan ya ƙunshi rubutu na Tatsuniyoyi, labarai, Almara, wasa ƙwaƙwalwa, ƙissoshi, wakoki da kaɗe-kaɗe da sauran su waɗanda aka taskance tun kafin zuwan turawa, misalin ayyukan Abdullahi Suka, Wali Ɗan Marna da Wali Ɗan Masani da sauransu.
B. Makaɗa
Sun rabu kaso da dama, misali:-
I. Makaɗan Fada: Misakin Ɗankwauro
II. Makaɗan jama'a: Misalin Dr Mamman Shata
III. Makaɗan Maza: Misalin Ɗan anace mai waƙar ƴan dambe
IV. Makaɗan ban dariya: Misalin Ƴan kama
C. Kayayyakin kiɗan Hausawa sun haɗar da kayayyakin dokawa misalin ganga, kalangu, jauje, dundufa, da kayayyakin gogawa misalin goge, kukuma, da kuma kayayyakin busawa misalin siriƙi, da algaita.
2. Adabin Zamani
Shine adabin da ya zowa Hausawa sabili da shigowar sabuwar wayewa sanadiyyar mamayar turawan mulkin mallaka musamman wanda ya soma a farkon ƙarni na goma sha tara.
Ga yadda adabin ya rabu:
A. Rubutattun waƙoƙi
Misalin Rubutattun waƙoƙin Aliyu Na Mangi, Sa'adu Zungur, Khalid Imam, Murtala Uba
B. Rubutun zube: misalin labarin littattafai irin su Magana Jari na Abubakar Imam, In da so da ƙauna na Ado Ahmad Gidan Dabino, Idan so cuta ne na Farfesa Yusuf M Adamu, Sihirtacce na Bala Anas Babinlata, Mace Mutum na Rahama A Majid
B. WASAN KWAIKWAYO
Misalin littattafan wasan kwaikwayo irin su Zamanin nan Namu, Mallam Zalimu
No comments:
Post a Comment