Wednesday, 6 December 2017

TARIHIN KASUWANCI A KANO 1

TARIHIN KASUWANCI A KANO

  Tsakure daga littafin 'Kano cibiyar Kasuwanci ta Africa' wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo (Allah yajiqansa da Rahama ya wallafa).

  Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Maigirma Farfesa Sani Muhammad zaharaddin, babban limamin Kano ya faɗa a ta'alikin littafin cewar:-
Ana yiwa Kano kirari da "ka misulu alfin, Jalla Babbar hausa, Gari ba kano ba Dajin Allah! Yaro ko dame kazo an fika."
 Haka kuma marigayi ɗan kishin kasa Sa'adu Zungur yana cewa a wakarsa Arewa Mulukiyya ko Jamhuriyya:
Ya! Sarki Alhaji Bayero,
   Ga 'yan birni da kanawiyya
Tun Bagauda na Saran kano,
   Suka fara fataucin dukiya.

TARIHIN ZUWAN LARABAWA KANO
  A shekara ta 1453 miladiyya, a zamanin sarkin kano Yakubu ɗan Abdullahi Barja, sarkin kano na goma sha shidda a mulkin kanawa, waɗansu larabawa mutanen kasar Gadamus masu fatauci suka zo daga Tarabulus (Libya), suka sauka a kano. Sune larabawan farko da suka fara zuwa kano.
   Da saukar waɗannan fatake, sai sukaje wurin sarkin kano Mallam yakubu, a jujin 'yan Labu, a lokacin ba'a gina gidan sarautar kano na yanzu ba, suka ce da sarki a cikin harshen larabci su fatake ne, suna so su zauna a kano domin suyi ciniki.
  A wannan lokaci kuwa, limamin kano Mallam Muhammadu Hashimu ne yake fassarawa sarkin kano abinda waɗannan fataken larabawa ke faɗa a matsayin tafinta. Daga nan sai sarikin kano yakubu yayi farin ciki kwarrai da gaske, sannan yace da shamakin kano ya kaisu sararin nan dake yamma da unguwar Garke watau Dandali, suyi gidaje su zauna acan.
  Sabili da waɗannan mutane suna da jar fata, sai mutanen kano suka sa musu suna Turawa. Don haka koda larabawan suka zauna a wannan wuri, sai mutane suka sanyawa wurin Dandalin Turawa. Dalilin sunan dandalin turawa kenan yau kusan shekaru 553 kenan.
   Tun daga wancan lokaci ne larabawa suka cigaba da zuwa kano fatauci. Kamar misali akwai Yamalawa mutanen Yamen, da larabawan Tunis duk sun riski kano, amma kowaɗanne akwai nau'in kasuwancinsu.
 Su larabawan Libya mafi yawan abinda suke siyarwa kayan alatu ne irin na sarakai da kayan kamshi da kayan zaki.
   Sai dai ya kamata a sani, da wahala ace ga lokacin da aka soma samar da kasuwanci a kano. A zamanin da, mutanen kano sunfi riko da noma fiye da wata harkar kasuwa, amma ana aiwatar da sana'o'i na gargajiya misalin rini, jima, kira da sak'a. Waɗannan su suka haifar da ainihin kasuwanci, domin mutum zaiyi abu ya siyar ga jama'a.
  Koda yake, a wancan lokacin, ba'a fara amfani da kuɗi ba a kano, ana yin cinikin furfure ne, watu ban gishiri in baka manda.
  Daga baya ne lokacin da fatake ƙlarabawa ko Asbinawa da Agalawa suka zo kano, kasuwanci ya fara kankama a kano.
  Haka ma, sauyawar akalar kasuwancin kasar hausa daga izuwa kano kamar yadda littafin 'Kano civil war and the British Over Rule 1882-1940' na Muhammad F.A ya ruwaito ya taimakawa kano matuka gaya, domin an samu cewar fatake sun yiwa katsina tawaye ne, suka koma kano ɗungurungum da kasuwancinsu.
   Zuwan turawa kano kuwa, da kuma yadda suka samar da farin kuɗi a shekara ta 1930 don yin musanje ya haɓaka kasuwanci sosai a kano. Domin a zamanin ne kanawa suka samu buɗewar ido ainun a harkar, har ya zamana suna yiwa kansu jagoranci, abinda ya sanya kano ta k'ara bunksa kuma kenan har ake mata kirari da Tumbin giwa ko dame kazo an fika.
  Kai bama nan ba, har daga kasashen Kasabalanka ta Morocco da Yunana ta Girka fararen fata sunzo fatauci kano, bari kuma kuji yadda suka zo...


TARIHIN KASUWANCI A KANO

  Tsakure daga littafin 'Kano cibiyar Kasuwanci ta Africa' wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo (Allah yajiqansa da Rahama ya wallafa).

No comments:

Post a Comment