Monday, 29 April 2019

TARIHIN BAUCHI 4

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na huɗu

Kalumbu mayaƙi ne daya tara taron mayaƙa masu yawa da raƙuma da dawakai marasa adadi, ya rubuta takarda ya aikewa sarkin musulmi Muhammadu Bello ɗan Usmanu bn Fodio da cewa " Ka sani, ni na mallaki abinda yake tsakanin mimi biyu (watau abinda yake tsakanin Mirsa da Malle)" yana mai bashi tsoro, yana yi masa narko da waɗansu baitoci dake cikin Nabinga, yace " Ni ina yi muku tsoro, kada rana ɗaya ta samu gareku domin tsananin ƙina, ranar nan kuwa wuyarta kamar ta ranaku masu yawa ce, saboda wuyar ta za a ga taurari da rana, gari zai zama haske ba haske ba, duhu ba duhu ba, har ku motsad da yaƙi mai hauhawa wanda bashi da misali, yana da kamar dare wanda yake cuɗanya da wani dare".
   Ko da manzon Kalumba ya riski Sarkin Musulmi da wannan sako, sai ya karɓi takarda ya karanta dukkan abinda ke ciki, sannan bayan ya gama ya juya bayanta, ya mayar da amsa da cewa "Na juyad da lamari na ga Allah, babu kuma ƙarfi ga saɓon Allah, dukkan su masu samuwa ne da ikon Allah". Sannan ya baiwa ɗan aike ya koma da ita.
   Sa'ar da Kalumba ya samu martanin sarkin Musulmi sai ya keta takardar bayan ya kammala karantawa, sannan ya hau da rundunar sa zuwa Kano. Ya sauka a ƙasar kano, duk inda ka duba sai jama'a da dawaki kawai ake gani. Jama'ar kano hankalinsu ya tashi, suka firgita firgici mai tsanani.
  Ana haka sai Sarki Musulmi Muhammad Bello ya aikewa Sarkin Bauchi Yakubu da yake yaƙia Das da cewa ya tafi wurin Kalumba ya yaƙe shi. Yakubu yace yaji kuma yabi.
 Daga nan sai Yakubu tara jama'arsa ya shaida musu halin da ake ciki tare da neman shawarar su, inda nan ma suka nuna goyon bayan su ga bin umarnin Sarkin Musulmi Bello.
  Babu jimawa sai Yakubu ya tashi da tawagar sa zuwa Bauchi, ya shiga tara ƴam baka, da ƙarin mayaƙa, sannan ya tashi ya ƙetare ƙasar sa zuwa Kano, ya sauka a wani wuri da ake kira Gantsa inda sansanin Kalumba yake. Rumdunoni biyu suka fuskanci juna, sannam aka soma shirin fafatawa.

Sunday, 28 April 2019

TARIHIN BAUCHI 3

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na uku
  Daga nan sai Yakubu yasa aka gina ramin ganuwa kusa da Inkel da ya ke da zama, akayi gini a wurin tare da sanya masa ƙofofi huɗu, sannan ya taso daga Inkel ya zauna acikinsa tare da jama'ar sa..   Wannan gari yanzu haka shi ake kira da suna BAUCHI.
   Mutane kuwa sai suka rinƙa zuwa gareshi rukuni rukuni suna yi masa mubayi'ar girma har sai da suka yawaita, ya zama suna fita wajen gari suna yin gidaje.  Yaƙi kuma ya rinƙa fita da hare hare zuwa yankunan kafirai.
   Yakubu ya aiki Muhammadu Kusu, da Dawaki Hammada da Yari su tafi yaƙi zuwa zaranda da Felu da Geji da Bulu, suka karkashe su tare da kamo ƴaƴansu bayi. Sannan Suka komo wurin Yakubu cikin aminci da tarin ganima.
   Bayan wannan, sai ya aiki Sarkin Yara Ibrahim ya tafi dutsen Boli da yaƙi. Da ya isa waɗansu sukayi sulhu dashi, waɗansu kuma suka ƙi don haka ya yaƙe su. Sannan ya wuce har zuwa Lago da Gabari yayi yaƙi dasu. Daga ƙarshe ya koma wurin Yakubu da ganima mai yawa.
   Haka kuma saɓani ya auku tsakanin Mallam Yakubu na Bauchi da Sarkin Gwambe Buba Yero,inda har sai da aka gwabza yaƙi a tsakani.
  Yakubu ya ƙetara kogi ya cimma Gwambawa da yaƙi, akayi kashe kashe, daga bisani akayi sulhu. Gwambawa sukayi alƙawari ba zasu ƙara tada fitina irin wannan ba..
Bayann wannan kuma sai Yakubu ya sake shiryawa ya tafi yaƙi zuwa Bununu, da Lere da Pursum da Bukuru sannan ya koma gida. Babu jimawa kuma ya sake tashi yaƙi zuwa Yamyam Ramu da Yamyam Jini. Daga nan sai ya shige Montal da Yargam da wasu wuraren mazauna duwatsu da suke biye da Yargam har zuwa Unkwai da Ɗan chandam.
Daga nan sai Yakubu ya ɗauki haramar yaƙi zuwa Lafiya da Awai da sauran wuraren gishiri. Bayan dawowar sa gida Bauchi ne mutane suka ƙaru wurinsa jama'a jama'a, da suka haɗar da Hausawa da Fulani, da Barebari dama sauran ƙabilu. Hakan yasa Yakubu ya ƙara girman Bauchi daga ƙofa huɗu zuwa ƙofa tara.
  Bayan wannan sai Yakubu ya ɗaura haramar yaƙi sannam ya tafi zuwa Das, ya zauna cikinta yana yaƙi da mutanem ta yaƙi mai tsanani har tsawon shekaru biyu, ya zama yana bin mutanen Das cikin duwatsu yana kisa.. ana kan haka ne kuma fitinar Kulumbu ta motsa tsakanin sa da Sarkin Musulmi na lokacin Muhammadu Bello. 

Friday, 26 April 2019

TARIHIN KASAR BAUCHI 2

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na biyu
  Sa'ar da lamarin Shehu Usmanu ya bayyana, mutane suka taru a wurinsa har suka yi yawa, sai sarakunan Hausa suka fara fushi da hakan, suka zama masu fitinar jama'ar Shehu Usmanu, suna aike musu da hari, suna kisa da kame su gami da siyarwa a matsayin bayi
   Da wannan abu ya tsananta sai jama'a suka yiwa Shaihu mubaya'ar yaki, suka soma gina ramin ganuwa da ɗaura tuta.
  Anan ne Shehu ya Umarci Yakubu ya koma gidasa Bauchi ya kira jama'ar sa zuwa biyayya ga Shaihu. 
   Yakubu ya tashi ya tafi ga mutanensa a Bauchi da ake kira Gerawa, ya kiraye su amma basu amsa kira ba. Sai waɗansu mutane daban ne suka amsa, acikin su akwai Mallam Adamu, da Ibrahimu, da Abdun-Dumi, da Hassan, da Faruku, da Muhammad Kusu, da Muhammad Yaro, da Hammada, da Mallam Badara, da waɗansun su da dama.
   Yakubu ya ja taron jama'ar sa zuwa wani wuri da ake kira Warunje ya zauna, sannan ya tashi zuwa Inkel, mutane na ta zuwa wurinsa a hankali suna yi masa mubayi'a.
  Daga nan sai ya shirya yaki zuwa wani gari da ake kira da suna Kanyallo, ya yaƙe su yayi galaba akansu, ya ƙone gidajensu ya washe dukiyarsu, sannan ya koma wurin zamansa. Wannan kuwa shine farkon yakin sa.
Bayan wannan sai ya ƴara shirya wani yaƙin, inda ya sarauta Galadima Faruku a matsayin Sarkin Yaƙi sannan ya aike su zuwa Miri, da zuwan su kuwa sai suka faɗa musu da yaƙi.
   Anan ma suka karkashe mutanen Miri, suka kamo ƴaƴansu, suka rushe gidajensu, Sarkin su ya gudu, ya tura iyalan gidansa cikin kogon dutse sannan ya karkashe su, daga bisani kuma ya kashe kansa.
  Galadima Faruku ya komo wurin Yakubu da ganimar yaƙi mai yawa cikin murna da farin ciki.
   Daga nan sai Yakubu ya shirya wani yaƙi zuwa Gubi.
  Su kuwa mutanen Gubi ance Kafirai ne masu girman kai, gasu jaruman gaske masu ƙarfin rai, babu mai iya samun su.
   Haka kuma suna zaune ne a wani wuri mai yawan duwatsu da wuyar shiga saboda santsin wurin shigar da kuma ƙafe-ƙafe gami da ƙayoyi.
   Amma duk da haka, sai da Yakubu yaci galaba akan su. Ya kore su suka bar gidajensu zuwa cikin duwatsu, shikuwa ya shiga cikin gidajen nasu, ya kashe na kashewa, ya kama na kamawa. Sannan ya koma gida Inkel cikin aminci da nasara.
  Ai kuwa wannan yaƙi shine ya tsoratar da dukkan kafiran ƙasar Bauchi, musamman mazauna saman duwatsu.

Tuesday, 23 April 2019

Tarihin Bauchi 1

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na ɗaya
ASALIN SUNAN BAUCHIN YAKUBU
Kafin muji asalin Bauchi, zamu fara ne da sanin sarkin Bauchi Yakubu wanda sunan sa yafi shahara tare dana ƙasar.
Ance a karni na goma sha takwas daf da soma yakin jihadi a kasar Hausa, wasu malamai biyu masu suna Mallam Adamu da Mallam Isyaku suka tashi daga Borno zuwa Ganjuwa, inda suka zauna ƙarƙashin kulawar sarkin garin na wasu ƴan shekaru.
  Bayan nan sai suka tashi suka koma Kufu da zama, daga nan kuma sai suka ƙarasa Jetar.
  Anan Jetar ne Mallam Isyaku yayi abota da wani mutum da ake kiransa da suna Daɗi. Shikuwa yana zaune ne a wani wuri da ake kira Tirwin.
   Mallam Isyaku ya kan ziyarci abokinsa Daɗi a Tirwin, sai rannan Mallam Isyaku ya tafi wirin Daɗi inda ya tarar dashi tare da yaron sa mai suna Yakubu.
 Bayan sun gaisa sun soma firar duniya, sai Daɗi yace masa "Wannan yaro da ka gani ɗa ne gareni, kuma shi ne idanuna, Allah kuwa ya sanya sonsa da yawa cikin zuciyata. Ina da ƴaƴa da yawa banda shi amma ina so Allah ya albarkace shi a inda yake duka. Yanzu kuwa na baka shi, ka zama uba da shugaba a gareshi, shi kuma ya zama ɗanka mai-yi-maka hidima, domin ya sami albarkar ka. Inda kake so duka ka tafi dashi, dukkan abinda kake so ya yi maka duka ka sanya shi yayi, domin kuwa ɗanka ne, kai ne mahaifinsa".
   Abinda akayi kenan. Mallam Isyaku ya tafi gidansa tare da Yakubu ya cewa matar sa "Ga ɗanki nan".
Duk inda Mallam Isyaku zashi Yakubu na tare dashi, suna cikin haka har labarin Shaihu Usmanu ɗan Hodiyo ya zo musu. Mallam Isyaku ya tafi tare da Yakubu zuwa wurin Shehu Usmanu, ya zauna acan shekara da Shekaru yana karatun ilim.
  Rannan sai Mallam Isyaku yayi niyyar tafiya ganawa da iyalinsa, amma baya da niyyar jimawa acan. Don haka ya tsammaci cewar idan ya tafi da Yakubu zai hana shi dawowa da sauri, hakan yasa ya shaidawa Shaihu Usmanu muradinsa tare da barin Yakubu a hannunsa. Daga nan sai yayi wa Yakubu bayani sannan ya tafi..
   Allah da ikonsa, sa'ar da Mallam Isyaku ya riski wani gari mai suna Yalwan ɗan Ziyal dake ƙasar Kano, sai cutar ajali ta ka ma shi, anan ya rasu. Don haka sai Yakubu ya cigaba da zama wurin shehu yana karatu, ya zama tamkar ɗa a gidan shehu. Har ma shehu ya aurar masa da ɗiyar abokinsa Mallam Bazamfare watau Yaya.

Monday, 15 April 2019

TARIHIN FULANI SULLUBAWA

TARIHIN FULANI SULLUƁAWA

SADIQ TUKUR GWARZO

Sulluɓawa kuwa jam'i ne na sulluɓe, kalmar da akace an samo ta daga kakansu ko ace asalin wanda zuriyar ta fito daga tsatsonsa mai suna Sisillo. Shikuwa Sisillo, ai miji ne ga bafullatanar nan ta jinsin Toronkawa mai suna Chippowo, kanwa ga bafullatani batoranke Mallam Usmanu Toroddo, waɓda yake kakan-kakan shehu Usmanu Mujaddadi ɗan fodio.
 Don haka ake ɗaukar jinsunan sulluɓawa da toronkawa na fulani a matsayin 'yanuwan juna. (Ado-Kurawa 1989:45-49).
  Asalin sulluɓawa wangarawa ne, watau ana iya cewar kakanninsu ne suka taɓa zuwa kano zamanin Sarkin Kano Muhammadu Kanajeji har suka kawowa garin musulunci. Amma suna da alaka da yarukan Mandigo dana Mandika na yankunan Mali.
   Sunan asalin yarensu shine wakore, daga baya suka nutse cikin fulatanci yayinda suka mance yarensu suke yara fulbe (Usman 1974: 168-169).
  Izuwa yanzu kuwa yana da wuya ko a gidan sarautar kano da jikokin marigayi mallam Ibrahim Dabo ke mulka kaji ana fulatanci, domin tuni sun rikiɗe izuwa hausa zuryan.
  An kuma samu cewar jinsin sulluɓawa, sunfi kowanne jinsi tsari mai kyau acikin kabilun fulani tun kafin jihadin shehu Usmanu, domin kuwa suna da shugabancinsu mai suna 'Sarkin Sulluɓawa' a duk inda suke.
  Kuma a zandam suka soma zama, daga bisani suka rinka kwararowa yankunan katsina, zariya, sokoto da rima da sauran yankunan hausawa.
  Sannan kuma, tun da jimawa suna rike ne da addinin musulunci bisa kyakkyawar turba. Don haka da yakin jihadi ya ɓarke, 'yan kaɗan daga cikinsu ne suka goyi da bayan sarkin gobir, amma mafi yawansu suna cikin waɗanda suka bada gagarumar gudunmuwa wajen samun nasara, don haka nema ɗansu ya samu zamowa sarkin kano.
Wasu jimsunan fulanin da yadda ake gane su sune:

UDAWA : Jakai, rakuma da shanu suke kiwo. Kusan kasar su Niger amma suna fantsaowa har Nigeria.
Bararoji: Suna da fararen shanu, suna siyar da magunguna. Wasunsu nada jakuna.
Hana Gamba: Sunfi kama da Buzaye, suma siyar da magunguna bayan kiwo.
Yaɓeji: Masu fararen shanu
Bakolo: Shanun su babu ƙaho

Saturday, 6 April 2019

TARIHIN NUFE 7: LABARIN MALLAM DANDO 3

TARIHIN NUFE: LABARIN MALLAM DANDO
Kashi na bakwai

SADIQ TUKUR GWARZO
Tun bayan wancan yaƙi, sai Sarki Majiya ya koma Juguma da zama, anan ya cigaba da mulki har ya rasu.
  Akwai watarana da Mallam Dando ya aika masa da cewa "Ka komo garinka Raba da ka tashi". Sai Sarki Majiya ya mayar masa da cewa "Mu Nufawa ɗabi'armu ba mu komawa garin da yaƙi ya ci sai an ƙone shi, don haka zan zauna a Juguma".
Amma dalilin yaƙi tsakanin Mallam Dando da Etsu Isa akan kuɗin haraji ne wanda ƴaƴan Mallam Dando suka rinka zagayawa suna karɓa.
Etsu Isa yace "Ashe Mallam Dando yana son mulkin duniya ne tun da har yake aika ƴaƴansa cikin ƙasashe domin su karɓi haraji? Yana neman duniya domin kan sa ne ba domin mu ba, shine har muka biye masa muka kori ƴan uwanmu suka gudu wani wuri shikuma ya karɓe sarautar su?"
Don haka sai ya aike masa da cewa "Ni bana son ƴaƴanka su ƙara karɓar haraji a ƙauyen mu bayan wannan shekarar".
 Mallam Dando ya aiki manzon sa ga Sarki Majiya a lokacin da ya koma ƙasar Basa da zama da cewa " Ka dawo ƙasar ka da zama, ka sani yanzu babu amana tsakanina da Etsu Isa, bayan na taimakeshi yanzu ya zama abokin gaba ta".
A lokacin ne Sarki Majiya ya koma Juguma da zama saboda al'adar su ta Nufawa da ta sanya ba zai iya komawa Raba ba. Har mutuwa ta riske shi kuwa yana Juguma inda aka naɗa ɗansa Chado ya gaji shugabancin sa.
Shi kuwa Etsu Isa sai ya shirya yaƙi zuwa Raba don tumɓuke Mallam Dando a mulki.
Mallam Dando ya shiga Halwa ta kwana uku da yaji labarin zuwan sa. Ya fita halwa aƙarshen rana ta uku ya bi turba , ƴaƴansa suka fitad da sansani  suna biye dashi  riƙe da makamai har zuwa bakin kogi.
A wannan rana yaƙi yazo har bakin kogin nan ta wani waje da ake kira Jabara, a ranar ne ɗan Mallam Dando Ibrahim ya rasu a idon ubansa, a lokacin da ake tsaka da gwabza yaƙi. Da yaƙi yayi tsamari kuwa sai Etsu Isa ya gudu da tawagarsa ya koma Kaniya da zama. Bai ƙara ɗagawa Mallam Dando kai ba har mutuwa ta riske shi yana sarkin Kaniya, inda aka naɗa ɗansa Mu'azu magajinsa.
Shima Mallam Dando ya cigaba da zama a Raba har mutuwarsa, inda ɗansa Muhammad Saba ya gajeshi tare da ɗorar da yaƙi ga sauran ƙasashen Nufe, har takai ya samu iko sama da kusan ɗaukacin sarakunan dake ƙasar Nufe kafin daga bisani faɗace faɗace su raunana shi tsakanin sa da ƴaƴayen sarakunan nan da ubansa ya gwabza dasu watau Majiya da Etsu Isa da kuma tsakanin sa da ƴanuwansa ƴaƴan Mallam Dando masu biɗar sarauta.


TARIHIN NUFE 6: LABARIN MALLAM DANDO 2

TARIHIN NUFE: LABARIN MALLAM DANDO
Kashi na shidda

SADIQ TUKUR GWARZO

Daga nan sai Mallam Dando ya cigaba da zagaye ƙasar Nufe yana wa'azi da bayar da maganai. A haka ya ƙara samun kyautar wata mace baƙa kyakkyawa ta fuskar bada magani, ya mayar da ita ƙwarƙwarar sa. Itace ta haifa masa ɗa namiji Ibrahimu.  Jimillar ƴaƴayen da aka haifarwa Mallam Dando cikin Nufe takwas ne, maza bakwai da mace ɗaya.
Bayan wannan, sai yaƙi ya auku tsakanin Sarki Majiya da Sarki Idrisu wanda ake kira da suna Etsu Isa. Sarki Majiya ya fita zuwa Gbara ranar litinin cikin watan sha'aban, yayi yaƙi sosai da Etsu Isa inda ya kora shi har zuwa Ilorin, a lokacin kuwa Mallam Dando ya shiga tawagar Etsu Isa, don haka tare dashi akayi wannan gudun neman mafaka. Sa'annan Sarki Majiya ya koma garinsa Raba, su kuma suka cigaba da zaman su a Ilorin.
Ana haka sai wata rana Sarki Majiya yake cewa da mutanen sa " Ku sani ni sarki ne cikakke, ba ni da wani abokin faɗa, gabas da yamma, kudu da arewa".
 Sai wani mabushin Bansanagi, watau Sarewa, yace masa "Ka da kace ba ka da wani abokin faɗa da maƙiyi, ko ka mance da Sarki Isa da Mallam Dando waɗannan da suke zaune a cikin Ilorin?"
Daga nan sai Sarki Majiya ya aika da takardu zuwa ga Sarkin Ilorin yace "Ina neman Sarki Isa da Mallam Dando, ina so ka aiko mini dasu".
Shikuma Sarkin Ilorin sai ya rubuta takardar sulhu zuwa ga Sarki Majiya, amma sai Sarki Majiya yaƙi Sulhu. Ya sake rubuta takarda cewar "Na baiwa Mutanen Ilorin duka gaba".
Sai kuwa Sarkin Ilorin yace "Allah shine muke neman taimako duka a wurinsa, ya taimake mu in yaso".
Sarki Majiya ya fidda yaƙi ranar Jumua cikin watan shawwal, ya sauka a bakin wani rafi da ake kira da suna Ansa. Da saukar sa sai mayaƙan Ilorin suka riske shi, suka auka masa da yaƙi.
Da fari sarkin ya soma cin galabar su inda har ya shiga cikin garin Ilorin, amma sai suka ƙara ƙaimi inda suka kore shi kora mai tsanani, ya koma wajen gari.
   Sarkin Ilorin ya tara malaman Ilorin duka yace ko akwai wani malami wanda zai taimakeni akan wannan abokin gaban?"
  Duka suka ce "Ba mu da wani taimako wanda zamu taimake ka dashi"
 Sai Mallam Dando yace masa "Ni fa ina da taimakon da zan bayar, domin na fuskanci malamai da kuɗi zambar ɗari uku da dubu bakwai na sami asiri"
  Sarkin Ilorin ya ce "To kuwa Zan ba ka zambar dubu saba'in". Mallam Dando yace "Ijarata da kai abin da aka samu a cikin damfamin Sarki Majiya"
  Sarkin Ilorin ya ce " Na ƙara maka da damfamin Sarki Majiya na biyu idan da akwai".
 Sa'an nan Mallam Dando yace a nemo masa mazaje uku, ya fita wajen gari dasu da shirin yaƙi, suka sauka nesa da sansanin Sarki Majiya, sannan yace da mazajen su haƙa masa rami mai  zurfi dai dai da tsawon mutum, sannan yayi bukkah ya ɗibiya ta akan ramin ya shiga cikin ramin  kwana uku, sannan ya fita zuwa Ilorin da hantsi.
  Da shigar sa ya riski Sarkin Ilorin yace masa "Ina sarkin Yaƙin Ilorin?" Sarki yace Aliyu shine Sarkin yaƙi. Sai Mallam Dando yace a nemo masa hankaka, sarkin yaƙi ya biyo ni da tawagar sa da hanzari"
  Ai kuwa nan take akayi kamar yadda yace. Mallam Dando ya aikata asiri a bakin hankakan, ya baiwa Aliyu Sarkin yaƙi shi yace masa " kada ka saki hankakan nan har sai ka kusanci sarki Majiya"
Sarkin yaƙi Aliyu ya fita ta kan ganuwa kusan faɗuwar rana, ya zagaya ta yamma yabi wuraren da Sarki Majiya yayi sansani sannan ya saki hankakan nan, ya tashi fir zuwa laimar sarki Majiya, ya yi ƙara, nan take hankulan kowa na tawagar ya tashi, suka ruɗe, dukkan su suka bazama a guje yaƙin su ya karye, mutanen Ilorin suka samu riba dasu.
   Suka kama dawaki zambar ishirin da huɗu, da mataye ɗari takwas dake cikin damfamin Sarki Majiya.
Sai Mallam Danbo da Etsu Isa suka fita daga cikin Ilori suka koma Raba da zama bayan korar Sarki Majiya. Mallam Dando ya ce wa Sarki Isa "zauna a wannan gari" Sarki Isa yace ni bani zama cikin garin abokan gaban mu. Ni ina nufin zama a wani wuri ne da ake ce masa Jangi" Watau ya yiwa Mallam Dando Musu.
 Daga nan Mallam Dando ya zama mai iko da Juguma, ƴaƴansa ke karɓo harajin sauran ƙasashe duka, har daga baya kuma saɓani ya ƙara aukuwa tsakanin sa da Etsu Isa wanda yayi silar aukuwar yaƙi gagarumi a tsakanin su.

TARIHIN NUFE 5: LABARIN MALLAM DANDO

TARIHIN NUFE: LABARIN MALLAM DANDO
Kashi na biyar
SADIQ TUKUR GWARZO
Alƙalin Gwari Ummaru ya ruwaito cewa Farkon labarin Fulanin Nufe ya soma ne da Mallam Dando, wanda yazo ƙasar Nufe daga ƙasar Hausa.
Ance shi mutum ne matsakaici wajen tsawo da haske, bashi da kaurin jiki kuma. Ya iske Nufe a zamanin da Sarki Majiya ke mulki. Sai ya zama almajirin sa.
A zamanin da Mallam Dando yazo ƙasar Nufe yana da ƴaƴa uku, Majigi, Abdu Ɓuya, da Etsu Usmanu. Ya rinƙa yawo garuruwan Nufe yana wa'azi har ya isa Daba.
A wannan garin kuwa akwai wata mahaukaciya tana ɗaure cikin mari, ana kiranta da suna Fatsumako.
 Masu magani sunyi har sun gaji ba tare da ta samu sauƙi ba.
Rannan Mallam Dando na shigewa inda take sai tayi ƙara har ya jiyo muryar ta, sai ya tambaya "wanene yake ƙara haka?" sai akace masa "Wata mahaukaciya ce wadda masu magani suka kasa warkad da ita"
  Sai Mallam Dando yace "Ku bani ita ina warkad da ita, in Allah ya yarda".
Da waliyanta suka ji sai suka amsa masa da cewa "Mun baka ita". Mallam Dando ya koma gida ya yi rubutu a alluna biyu, ya wanke, ya zuba a cikin ƙoƙuna biyu ya aika musu. Yace ƙwarya ɗaya ayi mata wanka da ita. Ɗayar kuwa a bata tasha. Sannan ya haɗa musu da turare na hayaƙi da za a yi mata turare dashi.
  Iyayanta suka aikata kamar yadda manzon Mallam Dando ya sanar musu.
  Da aka kwana uku sai Mallam Dando ya tafi don ya ganta, sai yace da iyayen ta "ku kwance mata marin nan". Iyayenta suka yi wa Mallam Dando musu kaɗan, sa'an nan suka yarda suka kwance ta. Mallam Dando ya kaita cikin kafe yace ta zauna nan.
Daga baya sai ya nemi aurenta suka amince masa, bayan sunyi aure ya tafi da ita Juguma suka kwana ɗaki ɗaya. Daga nan bata sake komawa cikin halin hauka ba. Ta sami cikin ɗa Mustafa, sannan ta haifi Muhammadu Saba.
A zamanin da ta haifi Muhammad Saba sai sarki Majiya Zubairu yace yana sonsa, don haka abar shi a hannun sa ya girma.
Akwai wata rana da Sarki Majiya ya shirya zuwa yaƙi Kukuku, mallam Dando ne ya bashi asiri ya kai ya zuba acikin ƙasar, sannan yaci su da yaƙi ya samu dukiya mai tarin yawa. Daya komo gida sai ya aikewa Malamin kuyangi guda biyu a matsayin kyauta.
 Mallam Dando ya karɓe su yayi godiya, ɗaya ya mayar da ita sa ɗakan sa, ita ce Habibatu, ɗaya kuma ya aikewa Atiku ɗan Shaihu Usmanu, hasken zamani, kogin talikai, babban waliyi, itace ta haifi Ummaru Nagwamatse. Wannan duk anyi shine bayan rasuwar sarkin Musulmi Muhammad Bello ɗan Shehu Usmanu Ɗan Fodio.