Sunday, 28 April 2019

TARIHIN BAUCHI 3

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na uku
  Daga nan sai Yakubu yasa aka gina ramin ganuwa kusa da Inkel da ya ke da zama, akayi gini a wurin tare da sanya masa ƙofofi huɗu, sannan ya taso daga Inkel ya zauna acikinsa tare da jama'ar sa..   Wannan gari yanzu haka shi ake kira da suna BAUCHI.
   Mutane kuwa sai suka rinƙa zuwa gareshi rukuni rukuni suna yi masa mubayi'ar girma har sai da suka yawaita, ya zama suna fita wajen gari suna yin gidaje.  Yaƙi kuma ya rinƙa fita da hare hare zuwa yankunan kafirai.
   Yakubu ya aiki Muhammadu Kusu, da Dawaki Hammada da Yari su tafi yaƙi zuwa zaranda da Felu da Geji da Bulu, suka karkashe su tare da kamo ƴaƴansu bayi. Sannan Suka komo wurin Yakubu cikin aminci da tarin ganima.
   Bayan wannan, sai ya aiki Sarkin Yara Ibrahim ya tafi dutsen Boli da yaƙi. Da ya isa waɗansu sukayi sulhu dashi, waɗansu kuma suka ƙi don haka ya yaƙe su. Sannan ya wuce har zuwa Lago da Gabari yayi yaƙi dasu. Daga ƙarshe ya koma wurin Yakubu da ganima mai yawa.
   Haka kuma saɓani ya auku tsakanin Mallam Yakubu na Bauchi da Sarkin Gwambe Buba Yero,inda har sai da aka gwabza yaƙi a tsakani.
  Yakubu ya ƙetara kogi ya cimma Gwambawa da yaƙi, akayi kashe kashe, daga bisani akayi sulhu. Gwambawa sukayi alƙawari ba zasu ƙara tada fitina irin wannan ba..
Bayann wannan kuma sai Yakubu ya sake shiryawa ya tafi yaƙi zuwa Bununu, da Lere da Pursum da Bukuru sannan ya koma gida. Babu jimawa kuma ya sake tashi yaƙi zuwa Yamyam Ramu da Yamyam Jini. Daga nan sai ya shige Montal da Yargam da wasu wuraren mazauna duwatsu da suke biye da Yargam har zuwa Unkwai da Ɗan chandam.
Daga nan sai Yakubu ya ɗauki haramar yaƙi zuwa Lafiya da Awai da sauran wuraren gishiri. Bayan dawowar sa gida Bauchi ne mutane suka ƙaru wurinsa jama'a jama'a, da suka haɗar da Hausawa da Fulani, da Barebari dama sauran ƙabilu. Hakan yasa Yakubu ya ƙara girman Bauchi daga ƙofa huɗu zuwa ƙofa tara.
  Bayan wannan sai Yakubu ya ɗaura haramar yaƙi sannam ya tafi zuwa Das, ya zauna cikinta yana yaƙi da mutanem ta yaƙi mai tsanani har tsawon shekaru biyu, ya zama yana bin mutanen Das cikin duwatsu yana kisa.. ana kan haka ne kuma fitinar Kulumbu ta motsa tsakanin sa da Sarkin Musulmi na lokacin Muhammadu Bello. 

No comments:

Post a Comment