Saturday, 6 April 2019

TARIHIN NUFE 7: LABARIN MALLAM DANDO 3

TARIHIN NUFE: LABARIN MALLAM DANDO
Kashi na bakwai

SADIQ TUKUR GWARZO
Tun bayan wancan yaƙi, sai Sarki Majiya ya koma Juguma da zama, anan ya cigaba da mulki har ya rasu.
  Akwai watarana da Mallam Dando ya aika masa da cewa "Ka komo garinka Raba da ka tashi". Sai Sarki Majiya ya mayar masa da cewa "Mu Nufawa ɗabi'armu ba mu komawa garin da yaƙi ya ci sai an ƙone shi, don haka zan zauna a Juguma".
Amma dalilin yaƙi tsakanin Mallam Dando da Etsu Isa akan kuɗin haraji ne wanda ƴaƴan Mallam Dando suka rinka zagayawa suna karɓa.
Etsu Isa yace "Ashe Mallam Dando yana son mulkin duniya ne tun da har yake aika ƴaƴansa cikin ƙasashe domin su karɓi haraji? Yana neman duniya domin kan sa ne ba domin mu ba, shine har muka biye masa muka kori ƴan uwanmu suka gudu wani wuri shikuma ya karɓe sarautar su?"
Don haka sai ya aike masa da cewa "Ni bana son ƴaƴanka su ƙara karɓar haraji a ƙauyen mu bayan wannan shekarar".
 Mallam Dando ya aiki manzon sa ga Sarki Majiya a lokacin da ya koma ƙasar Basa da zama da cewa " Ka dawo ƙasar ka da zama, ka sani yanzu babu amana tsakanina da Etsu Isa, bayan na taimakeshi yanzu ya zama abokin gaba ta".
A lokacin ne Sarki Majiya ya koma Juguma da zama saboda al'adar su ta Nufawa da ta sanya ba zai iya komawa Raba ba. Har mutuwa ta riske shi kuwa yana Juguma inda aka naɗa ɗansa Chado ya gaji shugabancin sa.
Shi kuwa Etsu Isa sai ya shirya yaƙi zuwa Raba don tumɓuke Mallam Dando a mulki.
Mallam Dando ya shiga Halwa ta kwana uku da yaji labarin zuwan sa. Ya fita halwa aƙarshen rana ta uku ya bi turba , ƴaƴansa suka fitad da sansani  suna biye dashi  riƙe da makamai har zuwa bakin kogi.
A wannan rana yaƙi yazo har bakin kogin nan ta wani waje da ake kira Jabara, a ranar ne ɗan Mallam Dando Ibrahim ya rasu a idon ubansa, a lokacin da ake tsaka da gwabza yaƙi. Da yaƙi yayi tsamari kuwa sai Etsu Isa ya gudu da tawagarsa ya koma Kaniya da zama. Bai ƙara ɗagawa Mallam Dando kai ba har mutuwa ta riske shi yana sarkin Kaniya, inda aka naɗa ɗansa Mu'azu magajinsa.
Shima Mallam Dando ya cigaba da zama a Raba har mutuwarsa, inda ɗansa Muhammad Saba ya gajeshi tare da ɗorar da yaƙi ga sauran ƙasashen Nufe, har takai ya samu iko sama da kusan ɗaukacin sarakunan dake ƙasar Nufe kafin daga bisani faɗace faɗace su raunana shi tsakanin sa da ƴaƴayen sarakunan nan da ubansa ya gwabza dasu watau Majiya da Etsu Isa da kuma tsakanin sa da ƴanuwansa ƴaƴan Mallam Dando masu biɗar sarauta.


No comments:

Post a Comment