TARIHIN NUFE: LABARIN MALLAM DANDO
Kashi na shidda
SADIQ TUKUR GWARZO
Daga nan sai Mallam Dando ya cigaba da zagaye ƙasar Nufe yana wa'azi da bayar da maganai. A haka ya ƙara samun kyautar wata mace baƙa kyakkyawa ta fuskar bada magani, ya mayar da ita ƙwarƙwarar sa. Itace ta haifa masa ɗa namiji Ibrahimu. Jimillar ƴaƴayen da aka haifarwa Mallam Dando cikin Nufe takwas ne, maza bakwai da mace ɗaya.
Bayan wannan, sai yaƙi ya auku tsakanin Sarki Majiya da Sarki Idrisu wanda ake kira da suna Etsu Isa. Sarki Majiya ya fita zuwa Gbara ranar litinin cikin watan sha'aban, yayi yaƙi sosai da Etsu Isa inda ya kora shi har zuwa Ilorin, a lokacin kuwa Mallam Dando ya shiga tawagar Etsu Isa, don haka tare dashi akayi wannan gudun neman mafaka. Sa'annan Sarki Majiya ya koma garinsa Raba, su kuma suka cigaba da zaman su a Ilorin.
Ana haka sai wata rana Sarki Majiya yake cewa da mutanen sa " Ku sani ni sarki ne cikakke, ba ni da wani abokin faɗa, gabas da yamma, kudu da arewa".
Sai wani mabushin Bansanagi, watau Sarewa, yace masa "Ka da kace ba ka da wani abokin faɗa da maƙiyi, ko ka mance da Sarki Isa da Mallam Dando waɗannan da suke zaune a cikin Ilorin?"
Daga nan sai Sarki Majiya ya aika da takardu zuwa ga Sarkin Ilorin yace "Ina neman Sarki Isa da Mallam Dando, ina so ka aiko mini dasu".
Shikuma Sarkin Ilorin sai ya rubuta takardar sulhu zuwa ga Sarki Majiya, amma sai Sarki Majiya yaƙi Sulhu. Ya sake rubuta takarda cewar "Na baiwa Mutanen Ilorin duka gaba".
Sai kuwa Sarkin Ilorin yace "Allah shine muke neman taimako duka a wurinsa, ya taimake mu in yaso".
Sarki Majiya ya fidda yaƙi ranar Jumua cikin watan shawwal, ya sauka a bakin wani rafi da ake kira da suna Ansa. Da saukar sa sai mayaƙan Ilorin suka riske shi, suka auka masa da yaƙi.
Da fari sarkin ya soma cin galabar su inda har ya shiga cikin garin Ilorin, amma sai suka ƙara ƙaimi inda suka kore shi kora mai tsanani, ya koma wajen gari.
Sarkin Ilorin ya tara malaman Ilorin duka yace ko akwai wani malami wanda zai taimakeni akan wannan abokin gaban?"
Duka suka ce "Ba mu da wani taimako wanda zamu taimake ka dashi"
Sai Mallam Dando yace masa "Ni fa ina da taimakon da zan bayar, domin na fuskanci malamai da kuɗi zambar ɗari uku da dubu bakwai na sami asiri"
Sarkin Ilorin ya ce "To kuwa Zan ba ka zambar dubu saba'in". Mallam Dando yace "Ijarata da kai abin da aka samu a cikin damfamin Sarki Majiya"
Sarkin Ilorin ya ce " Na ƙara maka da damfamin Sarki Majiya na biyu idan da akwai".
Sa'an nan Mallam Dando yace a nemo masa mazaje uku, ya fita wajen gari dasu da shirin yaƙi, suka sauka nesa da sansanin Sarki Majiya, sannan yace da mazajen su haƙa masa rami mai zurfi dai dai da tsawon mutum, sannan yayi bukkah ya ɗibiya ta akan ramin ya shiga cikin ramin kwana uku, sannan ya fita zuwa Ilorin da hantsi.
Da shigar sa ya riski Sarkin Ilorin yace masa "Ina sarkin Yaƙin Ilorin?" Sarki yace Aliyu shine Sarkin yaƙi. Sai Mallam Dando yace a nemo masa hankaka, sarkin yaƙi ya biyo ni da tawagar sa da hanzari"
Ai kuwa nan take akayi kamar yadda yace. Mallam Dando ya aikata asiri a bakin hankakan, ya baiwa Aliyu Sarkin yaƙi shi yace masa " kada ka saki hankakan nan har sai ka kusanci sarki Majiya"
Sarkin yaƙi Aliyu ya fita ta kan ganuwa kusan faɗuwar rana, ya zagaya ta yamma yabi wuraren da Sarki Majiya yayi sansani sannan ya saki hankakan nan, ya tashi fir zuwa laimar sarki Majiya, ya yi ƙara, nan take hankulan kowa na tawagar ya tashi, suka ruɗe, dukkan su suka bazama a guje yaƙin su ya karye, mutanen Ilorin suka samu riba dasu.
Suka kama dawaki zambar ishirin da huɗu, da mataye ɗari takwas dake cikin damfamin Sarki Majiya.
Sai Mallam Danbo da Etsu Isa suka fita daga cikin Ilori suka koma Raba da zama bayan korar Sarki Majiya. Mallam Dando ya ce wa Sarki Isa "zauna a wannan gari" Sarki Isa yace ni bani zama cikin garin abokan gaban mu. Ni ina nufin zama a wani wuri ne da ake ce masa Jangi" Watau ya yiwa Mallam Dando Musu.
Daga nan Mallam Dando ya zama mai iko da Juguma, ƴaƴansa ke karɓo harajin sauran ƙasashe duka, har daga baya kuma saɓani ya ƙara aukuwa tsakanin sa da Etsu Isa wanda yayi silar aukuwar yaƙi gagarumi a tsakanin su.

No comments:
Post a Comment