Monday, 3 January 2022

ASALIN KISHI

 ASALIN KISHI


Daga Sadiq Tukur Gwarzo


GABATARWA

  A shekarar 2013, wani rahoton binciken masana da Farfesa Daniel Freeman na Jamiar Oxford tare da marubuci Jason Freeman suka wallafa a jaridar 'The Guardian' ta ƙasar Amurka, mai taken 'Jeolousy: It's in your gene', ya nuna cewa kishi gadajjen abu ne wanda kowanne ɗan adam ke tare da shi a cikin ƙwayoyin halittar sa. Binciken da masana suka gudanar  ya nuna cewa mata sun fi bayyana kishi sama da maza, wannan kuwa a kimiyyance muna iya danganta shi da yanayin mutumtakar jinsinan biyu wajen jure yanayai na zuciya da ɗaukar matakai a game dasu.

Mujallar BBC Science Focus ta taɓa yin nazari game da dambarwar masana akan 'shin kishi abu ne da ɗan adam yayo gadon sa ko wanda ya koya bisa zamantakewar sa a muhallin sa?'. Shine har suka kawo hujjojin kowanne ɓangare, ciki har da masu kallon yadda wasu sarakuna a zamanin baya su ke baiwa baƙinsu matayen su don su tara da su, da yadda wasu ke faɗin cewa basu taɓa jin kishi game da abokan tarayyar jima'in su ba, sai dai bisa la'akari da hujjojin masu cewa 'gadon kishi ɗan adam yayi', waɗanda suka haɗa da yadda maza a mafi yawan lokuta suke son kyakkyawar mace (satirical theory) mai jiki sama da sauran mata, da yadda wannan soyayyar ta maza kan haifarwa da mata daraja musamman daga ƴaƴayen da dangantakar ta samar musu saboda tarawar jima'i, sai ya zamana wajibi ga mata su fi buƙatuwar samun kaɗaitacciyar dangantaka wadda zata basu ƴaƴaye, wanda hakan kan tilasta jikkunan su samar da ƙwayoyin halittun da zasu fi son wanzuwar su kaɗaitattu ababen so a wurin abokanan zaman su (maza).  Wannan ne silar samuwar kishi a ɓangaren mata, wanda kan faru da zarar mace ta hangi yiwuwar faruwar wani abu wanda zai iya dakushe mata wancan muradi nata da tayi gado daga ƙwayoyin halittu. 

Sai kuma yadda aka lura da samun ɓurɓushin kishi daga wasu dabbobi misalin Gibbon waɗanda dangantakar su ta ƙwayoyin halittu ke tuƙewa da ɗan adam, don haka aka fi danganta kishi ga 'Natural Selection', watau watsuwar ƙwayoyin halittu.

  Ƙarin hujja akan haka shine yadda a baya-bayan nan wani rahoton bincike ya tabbatar da cewa kishi shine silar da yara ƙananu ke yawan kuka/rikici da dare domin kange mahaifansu daga tarawa wadda zata kai su ga samar musu da ƙani ko ƙanwa, da kuma yadda yara ke ƙara yawaita rikici bayan mahaifiyar su ta sake haihuwa.

Mutane da yawa da zarar an ambaci kishi sun fi danganta shi a tsakanin ma'aurata, musamman tsakanin kishiyoyi, amma a zahiri kishi ya wuce haka. Don haka a taƙaice, wannan ɗan rubutu zai kalli wasu daga taƙaitattun zantuka game da asalin kishi a kimiyyance da tasirin sa gami da yadda ya kamata a tunkare shi.

MA'ANAR KISHI

Masana da dama sun fassara ma'anar kalmar kishi gwargwadon fahimtar su, amma bisa tamu fahimtar, kishi na nufin wani yanayi na zuciya wanda yake cike da tsoro da firgici da tsana da ƙyamata, wanda ya ke bijirowa a duk sa'ar da wani ya fahimci samuwar wani abu mai barazana ga darajar sa ko matsayin sa, ko damar sa, ko mabiyan sa ko wani abu muhimmi da yake tutiya da shi.

ASALIN KISHI

Ko da yake, masani mai bincike Emanuel Eisner ya faɗi cewa ƙwayoyin halittar mu kusan ɗaya suke da na kakannin mu waɗanda suka rayu kimanin shekaru 600 da suka gabata, amma haɓakar yanayin kishi a zuciyoyin mu yana da alaƙa da sauyawar abubuwan da suka rinƙa faruwa ga ɗaukacin jikkunan mu na tsawon waɗancan shekaru, wanda hakan ke nufin cewa akwai ɗaukacin banbanci a tsakanin abinda mutumin yanzu zai yi kishi akansa da na mutumin da ya rayu shekaru 600 baya, wannan ya samu ne daga sauyawar muhallai, da buƙatu da muradun mu ne, amma kuma ɗaukacin jigon kishin sam-sam bai sauya ba.

Masani Aaron Sell na jamiar Griffith da ke Australia, ya yi nazari akan asalin kishi, inda har ya gano kishi ne silar aikatuwar wasu munanan laifuka da rashin zama lafiya irin wanda ake fama da su a halin yanzu. 

Misali akan haka shine KISA. 

Kimanin kashi 90% na kashe-kashe da ake yi a wannan duniyar maza ke aikata su, amma an lura da cewa mata ne akan gaba wajen kashe ƙananun yara (Infanticide) da kuma abokanan auratayyar su (spousal homicide).

Mu kalli Spousal Homicide: Wananan kalma na nufin yanayin kisan kai da kan faru tsakanin ma'aurata, walau miji ya kashe matar sa, ko mata ta kashe mijinta. 

Bincike ya tabbatar da cewa mata aka fi samu da kashe mazajen su.

Haka nan, Bincike ya nuna cewa sama da dubunnan shekaru, mazajen da suka rayu a wannan duniyar suna cike da kishin matayen su, don haka sun kasance cike da kokari wajen ganin sun mallaki akalar matayen su, watau sun kange su daga tarayyar da basa so. Wasu mazan kan yi haka ta hanyar tsoratarwa, ko nuna ƙarfi ga mata waɗanda akasari sune a ƙarƙashin su, wannan ya sa har zuwa yanzu akan samu yanayan da namiji zai saki mace, sannan ya bi sabon mijin da ta aura ya kashe ko ya yiwa lahani, saboda ya sake ta ne cikin fushi, yana mai burin ta shiga wani yanayi wanda zai sa ta yin nadamar rabuwa da shi ba don baya son ta ba, amma da zarar ya ganta cikin yanayi mai daɗi saɓanin yadda yayi muradi, sai kishi ya taso masa, wanda a wasu lokutan ya kan zama silar aikata munanan ayyuka.

 Su kuwa mata kasancewar su raunana ga maza, sai suka fi amfani da kisa a ɓangaren su wajen gudanar da nasu kishin na kange mazajen su daga tarayyar jima'in da ba sa so. Duk da cewa an lura da cewar mata masu ƙarancin shekaru kuma waɗanda basu haihu da yawa ba ne suka fi aikata hakan, amma sau tari ɓacin ran da ke tunkuɗa su aikata wannan mummunan aiki daga gundarin kishi ya ke.

Mai bincike Anne Campbel ta gudanar da cikkaken bincike game da silar rikicin mata, abinda ta tafi akai shine mata sun ɗora rayuwar su kachokan ne akan maza (uba, ɗan uwa, miji da sauran su), don haka matsawar mace tana da namijin da zai mata yaƙi, ba za a ganta cikin rikici ba. Saboda haka ana iya cewa babban abinda ke tunkuɗa mata aikata wancan ta'addancin na kashe mazajensu bai wuce yadda suke ɗaukar tozarci ne a gare su idan har suka samu raguwar daraja ko kawar da kai daga wanda suka ɗorawa so da aminci a garesu, don haka sukan gwammace halaka mazajen su duk a cikin kishi.

Amma a game da kisan ƙananun yara da mata kan yi (infanticide), shahararrun masanan nan Martin Daly da Margo Wilson sun yi bincike akai, inda suka bayyana cewa samuwar kishiyar uwa a gida na sanya yaro cikin haɗarin fuskantar kisa a ƙalla da kashi saba'in, da kuma haɗarin fuskantar cin zarafi da kashi 40. Wannan ma duk kai tsaye ana iya cewa daga kishi ne wanda ke faruwa a tsakanin matan gida wanda kuma yake shafar yaran.

Don haka, a ƙarshen binciken Masani Aaron ya tafi akan cewa ɗan adam bai ginu da ƙwayoyin halittun yin kisa don kange wanda yake so daga wata tarayya da ta saɓawa son zuciyar sa ba, sai dai kisan ya kasance a matsayin makami da wasu yanayai munana na zuciya kan tunkuɗa wasu mutane su yi riƙo da shi gwargwadon juriyar su ga wutar kishin da ke ruruwa a zukatan su. Wannan kuwa yanayi akan same shi a sauran sassan rayuwa ba ga auratayya ba kaɗai.

Haka nan, masana sun kalli yawaitar tashe-tashen hankula tare da danganta su da kishi, wanda yake faruwa sabili da tarayya akan abu guda da wasu mutane ke son mallaka, ko kaɗaituwa da shi da makamantan irin haka, don haka duk wanda ya ga akwai yiwuwar ya rasa wata martaba da yake tinƙaho da ita ko wani na son tarayya da shi ko kuma wani ya hau turbar fifita a wani lamari sama da nashi, sai kawai yayi martani da ayyuka waɗanda suka saɓawa hankali. Akwai irin waɗannan abubuwa da yawa a cikin kasuwanci, siyasa, malantaka da sauran lamurori na zamantakewar al'umma.

  Akwai ƙarin hujjoji masu nuni da cewa kishi daɗaɗɗen abu ne da ke cikin jini wanda yake yawatawa a jijiyoyin ɗan adam, daga misali shine kisan farko da ɗan adam ya soma aikatawa a duniya, watau tsakanin Ƙabila da Habila (Cain da Able), da kuma yadda yazo a tarihi wurare daban daban inda ɗanuwa ya kashe ɗanuwansa bisa wani dalili mai tuƙewa da kishi.

  Susan Dudley, masaniya ce mai bincike, ta gudanar da wani bincike dangane da wasu tsirrai (American sea rocket) wanda ya ƙara mana fahimra a game da asalin kishi.

  Susan ta ware wasu tukwane guda biyu ne, sannan a tukunya ta ɗaya ta shuka jinsin tsirrai guda guda biyu ƴan uwan juna, a tukunya ta biyu kuwa sai ta shuka mabanbantan jinsinan tsirrai. Bayan tsawon lokaci sai ta samu cewa tsirran da aka shuka a tukunyar da ke ɗauke da mabanbantan tsirrai sunfi saurin girma fiye da ɗayar. Wannan na nuna cewa akwai kishi har a tsakanin tsirrai, domin gashi tsirran da suke da alaƙa da juna sun hana junan su girma yadda ya kamata. Wannan fa ya faru ne a tsakanin tsirrai wanda kowa ya sani kashi 25 zuwa 30 na ƙwayoyin halittar su ɗaya yake da na bil'adama. Ina ga shi jansa ɗan adam? 

Don haka fahimtar ainihin yadda kishi ya samo asali na da buƙatar dogon nazari mai tuƙewa da asalin samuwar ɗan adam, amma dai a mafi rinjaye, ƙwayoyin halittar ɗan adam ne ke ɗauke da shi.

A INA AKE SAMUN KISHI

An fi samun kishi a tsakanin abubuwa biyu masu alaƙa da juna.

 Misali, mutum ya fi kishi da mutum, dabba ta fi kishi da dabba, haka ma tsirrai sun fi yi a tsakanin su.

  Haka kuma, ko a cikin mutane, yawan zurfin alaƙa ke nuni da yiwuwar samun zuzzurfan kishi. Ko kuma ace, kishi ya fi samuwa a tsakanin wasu mutane da suke tarayya da wani abu, misalin jinsi, ƙabila, harshe, gari ɗaya ko ƙasa ɗaya, ko ƴanuwa da abokanai, ko a tsakanin wasu rukunin al'umma masu aiki ko sana'a iri ɗaya, da dai makamantan su.

Don haka za a ga cewa mace ta fi kishi da mace ƴaruwarta sama da namiji. Haka kuma sau tari, Bahaushe ya fi jin kishi ga abinda ya shafi ɗanuwan sa Bahaushe. A wani yanayin ma akan samu cewa mutum ya fi samun maƙiya daga ƴanuwan sa na jini . 

AMFANIN KISHI

  Masana sun kalli tasirin kishi, sun kuma tabbatar da cewa abu kamar sa wanda ya daɗe a duniya yana ta bibiyar ƙwayoyin halittar ɗan adam ba zai taɓa kasancewa mara amfani ba. Babban amfanin da aka fi dangantawa kishi shine; ankararwa da kuma zaburarwa domin tashi tsaye bisa naƙasun da akan iya haɗuwa da shi a lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Don haka, ɗan kasuwar da ya fahimci yiwuwar wani abokin kasuwancin sa zai danne shi a fannin kasuwanci, zai ji kishi a zuciyar sa, wanda hakan na nufin ya zaburar da shi domin fahimta gami da gyara abubuwa na kuskure da yake aikatawa gami da ɗorarwa akan ayyukan da zasu ƙara riƙe masa martaba a kasuwancin sa. Irin haka ne ga kishiya ta aure, ko malanta, ko ta duk wani abu da kishi kan iya bijirowa a cikin sa.

  Saboda haka kyakkyawan kishi abu ne da aka lura da cewa zai iya samar da cigaba ga mutane ko ga yankuna ko ga duk wani abu da ake kishi akan sa matsawar an yi amfani da shi bisa tsari kyakkyawa yadda ya kamata.

ILLAR KISHI

Mutane da yawa suna faɗawa cikin munanan ayyuka sabili da kishi. Wani kan kashe wanda yake kishi dashi, ko ya bi wasu hanyoyi da yake gani zai iya  wargaza lamurran abokin kishin sa. Wanda akan haka, wasu kan rasa rayuwar su, ko matsayi ko darajar su ko imanin su da Allah maɗaukakin sarki. Wasu ma na tsintar kawunan su a kurkuku ko a wani yanayi mara daɗi tun anan duniya duk bisa mummunan aikin da aka aikata saboda kishi.

  Babban illar kishi ga ɗan adam shine; hana girma ko haɓaka.

   Sau tari, mummunan kishi ne silar durƙushewa da rashin cigaban al'umma. Shine kuma kan zama silar yawaitar munanan ayyuka da rashin zama lafiya.

MAFITA GAME DA KISHI

Yana da kyau a sani cewa babu wani ɗan adam da ba ya jin kishi matsawar yana da lafiyar ƙwaƙwalwa. Sannan babu wata ni'ima ko fifiko da Allah zai yi ga wani ko wata wadda ba zata sanya kishi a zukatan mutane musamman masu wani abu iri ɗaya da shi ba. Mafitar ɗaya ce; a mayar da dukkan lamurra ga Allah.

Masani Berit Brogard yana da dabarar  'normalism the feelings' wajen kashe mummunan kishi, watau ɗaukar irin waɗannan yanayai a matsayin abu gama gari wanda bai kamata a tayar da hankali akan sa ba. 

Don haka da zarar tunanin sa ya bijirar masa da wani abu na kishi, sai ya kwantarwa da zuciyar sa hankali, ya faɗa mata wannan abin fa 'is normal' ba abu ne mai buƙatar ɗaga hankali ba.

 Sanin kowa ne cewa kowanne ɗan adam yana da ƙaddarar sa, wani mai kyau wani mara kyau. Don haka, sunnar rayuwa ce irin abin nan da ake cewa 'yau gareka gobe ga wanin ka'. Watau komai na tafiya da lokaci. Idan yanzu kai ne ke sharafi, to ai a baya ba kai bane, don haka nan gaba ma wani ne zai yi ba kai ba.

Abu na gaba shine buƙatar rage abinda masana ke kira 'endowment effect', watau yanayai da kan sa mutum ya ji cewa shi kaɗai ya isa da abu kaza ko jin cewa abu kaza mallakin sa ne shi kaɗai tilo, kamar yadda aka fi samu a tsakanin ma'aurata. 

Ya kamata mace ta sani cewar an halartawa namiji ƙarin aure a duk sanda ya samu sukuni, haka shima namiji ya sani cewar mace na da damar samun annushuwa da wanin sa idan ƙaddarar rabuwa ta auku a auratayyar su.

Kuma ya kamata kishi ya zamo silar zaburar da mutane aikata kyakkyawan ayyuka ba munana ba.

Sannan mutum ya ɗora faruwar lamurra dukkan su ga Allah maɗaukakin sarki, walau ga kansa ko ga wanin sa.

Ƙarshen wannan muƙala kenan.

Ina mai adduar Allah ya jikan babban marubuci Alh Bashir Usman Tofa wanda aka yi jana'izar sa ayau litinin 2/1/2022.

Ga masu buƙatar ƙara samun sani gaɓe da wannan muƙala, akwai kwas mai taken 'Introduction to Mental Health' wanda muka samar kyauta a kwalejin Hausa ta yanar gizo mai suna AAGHOLI akan adireshin (https://www.aagli.com.ng)

Nine naku Sadiq Tukur Gwarzo (Public Health Nurse, mamba Global Goodwill Ambassadors)


  



I

No comments:

Post a Comment