Sunday, 7 January 2018

HIKAYAR WANI SARKI DA WANI MUTUM


LABARIN MU NAYAU; ABU DAYA
A zamanin da, anyi wani Sarki a wani gari mai ilimi, yana son koyawa al'ummar sa darasi. Don haka sai ya sanya aka dauko wani dutse qato aka ajiye a babbar hanyar shiga garin ba tare da al'ummar garin sun sani ba. Lokaci-zuwa-lokaci, sarkin yana zuwa ya labe a wajen don ganin ko akwai wanda zai dauke dutsen da kuma sauraron maganganun jama'a akan dutsen.
Da yawan mutane idan sunzo wucewa ta wurin sai dai suyi tsaki da baqar magana akan sarkin, wasu suce "Sarkin garinnan bashi da adalci, kalli yadda ya bari aka lalata hanya" da sauran maganganu na batanci.
Ana haka sai ga wani mutum yazo wucewa yana dauke da kaya- niqi-niqi akan sa. Da zuwa wajen dutsen nan sai ya sauke kayansa a gefe, sannan ya fara kici-kicin kawar da dutsen daga kan hanya. Yayi ta qoqari, dakyar ya samu galaba ya ture dutsen.
Ya tsaya yana haki yana dan hutawa kafin yaci gaba saboda wahalar da yasha, sai ya hango wata jaka ajiye adai-dai inda ya ture dutsen. Nan take ya garzaya gareta, ya dauka kuma ya bude. Sai ya ganta cike da gwala-gwalai, ga wata 'yar takarda a gefe an rubuta cewa ' wannan kyauta ce ga duk wanda ya matsar da dutsen nan'.
Mutumi dai bai gama gamsuwa ba, yana ta waige-waige ko zaiga mai jakar, can sai kuma Sarki ya fito daga inda yake boye. Cikin rawar jiki Mutumin ya fadi gaban sarki yana tuba da rantse-rantse, tsammanin sa jakar sarki ce aka sato shikuma ya tsinta.
Sarki ya rarrashe shi gami da kwantar masa da hankali, ya kuma jinjina masa ga aikin dayayi, sannan yace "Ka sani, wannan kyautar kace kuma bata kai abinda Allah yayi tanaji ba ga duk wanda ya kawar da wani abu akan titi wanda yake cutar da mutane"
"Don haka na jinjina maka matuka, lalle ya kamata sauran mutane suyi koyi dakai acikin sauran fannonin rayuwa. Bai kamata mutane su koma gefe ba suna aibanta gwamnati akan abinda zasu iya magancewa ba..""
Kashe gari Sarki yasa aka tara al'mmar garin duka, ya sanar dasu abinda ya faru, sannan yayi musu nasiha da su rinqa kokarin kawar da duk wani abu wanda yake cutar da al'umma ba lalle sai akan titi ba, har ma da bangaren asiniti, ilimi da kasuwanci. Yace mutane ayanzu sunfi fifita abinda zasu samu anan duniya sama da abinda Allah zai basu, idan da mutane sun san kyautar dana ajiye aqasan dutsen da haqiqa anyi rububin ture shi, a qarshe ya kuma sanar dasu cewa yin abu don Allah yana daga alamomin Imani kamar yadda manzon Rahama annabi Muhammad (s.a.w) ya fada.
Da fatan muma zamu dauki wannan darasi wajen cike ramukan titi masu haifar da hatsari, taimakawa da magunguna kyauta ga marasa lafiya dake asibiti, taimakawa 'yam makaranta da kayan karatu, tare da rangwame ga al'umma acikin kasuwanci. Allah yasa mu dace amin

Saturday, 6 January 2018

HIKAYAR TSUNTSUWAR SIHIRI KOKILA

HIKAYAR TSUNTSUWAR SIHIRI KOKILA.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
    08060869978

A wani tsohon zamani daya gabata, anyi wata alkarya a gefen tsaunin Sontolo, sunan birnin Gazarwa, sunan sarkin su kuwa Riji.
   Birnin Gazarwa birni ne mai daɗin zama da lambuna masu korayen ganyaye da ingantattun kayayyakin marmari. Ga koramu na kwaranyuwa, abin gwanin ban sha'awa.
   Haka kuma sarki Riji ya kasance mai adalci ne ga mutanensa.
   Mutanen wannan birni, sun camfa cewar duk wannan zaman lafiyar da walwalar da suke ciki gami da albarkar lambunansu, ya samu ne saboda wata tsuntsuwa mai suna Kokila.
   Kokila na rayuwa ne bisa wata bishiya babba, wadda take a cikin wani ni'imtaccen lambu.
 Lambun kuwa yana daf ne da fadar sarki Riji.
  Kokila tsuntsuwa ce makauniya, amma tana da murya mai zaki, kuma gwana ce wurin rera wakoki irin nasu na tsuntsaye.
   Bisa camfin mutanen Gazarwa, wakar da kokila ke rerawa ke kunshe da sihirin samar da zama lafiya gami da ni'ima awannan gari nasu.
  To, acan bayan tsaunin Sontolon kuma dai, akwai wani garin har ila yau mai suna Maladawa.
  Sunan sarkin Maladawa Jangero, kuma ya kasance mai aikata zalunci ga mabiyansa, saboda haka ma garin nasa ya kasance sam babu lumana da zama lafiya, kowa kagani a garin cikin ɓacin rai yake da fushi, don haka da zarar ka taɓa shi zakuyi husuma da faɗa, sannan amfanin gonarsu kuma ko kyau ba yayi.
  Watarana sarki Jangero ya shirya tafiya izuwa wani wuri, akan hanyarsa ta dawowa sai ya ratsa ta Kasar Gazarwa, ai kuwa sai ya kamu da shaukin ni'imar dake gonakin wannan kasa.
  Ko daya dawo gida, sai yake ta santi, har yana burin inama kasarsa zata kasance kamar Gazarwa.
   Nan take Sarki Jangero ya kira wazirinsa, yace masa Tun da nake jin labarin Gazarwa, ban taɓa sanin haka take ba sai lokacin dana ratsa ta cikinta, don haka inaso kayi mini binciken hanyar da Sarkinsu yabi wajen mayar da daular kamar haka.
   A wannan rana, wazirin Jangero bai kwana gida ba, sai ya ɓadda kama izuwa siffar fatake, ya nufi garin Gazarwa.
  Da isarsa, sai ya rinka tambayar al'ummar garin fahimtarsu game da wannan ni'ima da suke ciki acikin hikima, yana kuma zagaye garin yana ta dube-dube abinsa.
   Daga karshe, bayan ya kammala tattara bayanai, sai ya komo gida.
   "Ran sarki ya daɗe, na samo sirrin bunkasar kasar Gazarwa" waziri ya faɗa ga Sarki Jangero cikin russunawa a sanda ya same shi a fada.
   "Yawwa, yi maza ka sanar dani.." Jangero ya umarci wazirinsa.
   Waziri yace "Ai wannan sirri yana jikin wata tsuntsuwar sihiri ne dake garin, sunanta Kokila".
   Daga nan ya kwashe labarin duk hanyar da yabi izuwa Gazarwa, da kuma zantukan da mutanen kasar suka sanar masa.
   Sarki Jangero yayi shiru yana tunani bayan yaji wannan labari, sannan yace "to kuwa idan haka ne, dole ne na maido da wannan tsuntsuwar izuwa masarauta ta"
   Sannan ya kalli yankin da fadawansa ke zaune, ya nuna na tsakiya yana mai cewa "Sarkin yaki, yi maza kaje ka soma shirya dakaru, zamuje yaki Gazarwa domin kwato wannan tsuntsuwa mai sihiri"
   Waziri yayi gyaran murya, sannan ya sake rankwafawa gaban sarki, yana cewa "Ranka ya daɗe, ban tari numfashin kaba, amma ina ganin matsawar mukayi yaki da Gazarwa, mune da Asara"
 Daga nan sai Yayi shiru yana jiran umarnin sarki, amma da yaji sarkin baice komai ba, sai yaci gaba da cewa
 "Kasancewar akwai adawa da rashin zama lafiya a tsakanin sojojin mu akoda yaushe, hamayya tayi yawa tsakankaninsu, sojojin kasar da zamu kaiwa yaki kuwa cike suke da kaunar juna da haɗin kai, don haka ban jin zamuyi nasara a yanzu"
   Sarki ya gyaɗa kansa sama yana mai cewa "haka ne waziri, amma menene abinyi".
   Waziri yaci gaba da cewa "inaganin zaifi kyau ka nemi Sarki Riji ya baka aron wannan tsuntsuwa na tsawon wasu kwanaki cikin maslaha, nasan shi mai karimci ne, zaiyi wuya ya hanaka".
 "Shikenan, haka nan za'ayi".  Sarki Jangero ya faɗa.
 Daga nan aka cigaba da fadanci, ba'a sake tayar da maganar ba har aka tashi fada.
  Sati ɗaya da faruwar wannan lamari, Sarki Jangero ya haɗa tawaga sannan ya nufo Gazarwa. A tare dashi kyaututtuka me masu tarin yawa.
   Sarkin Gazarwa Riji ya taryi bakonsa cikin karramawa, ya shirya masa bukukuwa don kayatar dashi tare da gabato masa da abinci kala-kala.
  Bayan an natsa, sarakunan biyu suka ware domin tattaunawa.
   "Mai martaba Sarkin Gazarwa, gani nayi muna kusanci da juna, amma bamu taɓa kawowa juna ziyara ba, wannan yasa na fara kawo ziyara gareka.."
  Inji Sarki Jangero.
 "Ai kuwa ka kyauta Mai martaba, wannan ziyara ta sada zumunci matuka a tsakanin mu" Sarki Riji ya faɗa cikin annushuwa.
   "Sai dai kuma, na kamu da wata bukata yayin shigowa ta gareka.." Inji sarki Jangero.
  "Haba ɗan uwa.." sarki Riji ya katse shi. "Faɗi bukatar ka kowacce irice, zaka sameta a gareni".
  " Ina son ka bani aron Kokila." inji Sarki Jangero.
"Kokila???"
 Sarki Riji ya tambaya cikin kaɗuwa..
  "Kwanaki kaɗan kurum zatayi a gareni.. Ina son sihirinta ya samarwa kasata zaman lafiya da yalwar arziki, gami da farin ciki... Ka taimakeni ya Maimartaba Sarki.."
  Sarki Jangero ya faɗa yana mai magiya ga Sarki Riji.
 "Shikenan.." Sarki Riji ya amsa masa. "Zan baka arom kokila"
  Abinda ya faru kenan, da Sarki Jangero ya shirya komawa gida aka haɗo masa kyaututtuka tare kuma da tsuntsuwar sihiri Kokila.
 Amma dai, zuciyar sarki Riji cike take da sosuwar rabuwa da wannan tsuntsuwa, har ma sai daya zubda hawaye daga idanuwansa. Don haka ya umarci wasu amintattun bayinsa su biyar dasu tafi tare da sarki Jangero izuwa kasarsa Maladawa, su zamo masu hidima ga Kokila, kuma su tabbatar tana samun matukar kulawar daya kamata a koda yaushe.
   Koda Sarki Jangero ya isa gida, bai tsaya wata-wata ba ya karɓe Kokila daga hannun bayin Sarki Riji, sannan yasanya aka cusata cikin wani keji na bakin karfe aka rufe.
   Shugaban bayin Sarki Riji ya rugo da gudu gaban sarki Jangero, ya faɗi yana afi, yana cewa "Ranka ya daɗe, ina rokonka ka fitar da tsuntsuwar nan daga wannan kejin, domin hakan zai kuntata mata ne duba da yadda ta saba rayuwa cikin sakewa a lambu".
   "Kai shashasha, rufe mini bai!"  Sarki Jangero ya daka masa tsawa.
  Sannan yaci gaba da cewa "Yanzu kokila mallaki nace, dole nayi abinda naso da ita".
  Daga nan ya juya ga wazirinsa, yace "ina umartar daka sanya min waɗannan bayi a kurkuku, anan zasu ruɓe har tsawon rayuwarsu, kokila kuwa babu mai raba ni da ita".
   Waziri ya russuna gaban sarki, yace "Ran sarki ya daɗe, a lura da abinda za'a aikata.. Ina ganin matukar kayi haka, sarki Riji ba zai kyale ba"
  "Ai kuwa ba zai iya kawo mana hari ba akan tsuntsuwa. Nasan shi mutum ne mai son zama lafiya, bana tunanin zai sanya rayuwar dubun nan mutane cikin haɗari akan tsuntsuwa guda ɗaya tak.."
 Inji Sarki Jangero.
  A karshe, babu yadda Waziri ya iya, dole yabi umarnin takadirin sarkinsa.
  Sai dai kuma Kokila ta rasa walwala, duk da cewar an kawo mata 'ya'yan itatuwa da furanni kala-kala, amma taki yin wakar data saba balle ayi tsammanin sihirinta zai soma aiki.
  Don haka a kullum, tashin hankula kurum ake samu a wannan kasa, k'ararraki suka yawaita a kotuna, fursunoni kuma suka cika dankam..
  Wannan yasa Sarki Jangero yasa anemo masa mafarautan tsuntsaye, suka duba masa kokila amma sam basu samu wata lalura daga gareta ba.
  Ana haka sai labari ya riski Sarki Jangero na wani tsoho mai suna Baba, mai shekaru sama da ɗari, wanda akace shi gwani ne a siddabaru da kuma gane matsaloli ko waɗanne iri ne.
  Rannan sai ya kira wazirinsa yace yazo ya rakashi ga Baba domin a duba masa matsalolin dake damun kasarsa.
  Bayan sun ɗanyi tafiya gefen gari akan dawakai  suka iske sashin wata bukka, sannan daga nesa Waziri ya nunawa sarkin cewa ga inda Baba yake can.
  Don haka Sarki Jangero ya sauko daga kan dokinsa, ya nufi cikin bukkar kai tsaye.
  Da isarsa, wani tsoho ya gani zaune, ko wanne gashi na jikinsa yayi fari saboda tsufa, amma sam babu alamar rakwarkwaɓewa ajikinsa.
  Sarki Jangero ya gabatar da kansa ga Baba, sannan ya sanar masa duk labarin sa.
  "yanzu kai ka gamsu da cewar akwai sihiri a sautin tsuntsuwa kokila wanda yake samar da zama lafiya a kasa?"
  Baba ya tambayi sarki bayan ya gama jin labarin sa.
  "Kwarrai kuwa", inji sarkin. "Abinda kowa ke cewa kenan, gashi kuma na kawo ta masarautata don na samu biyan bukata amma takiyin sauti ko kaɗan".
  "Amma dai Kai shashasha ne.." Inji Baba.
  Sarki Jangero ya daka masa tsawa, "kai tsoho!!!", yayin daya mike tsaye zumbur cikin fushi yana kokarin zare takobinsa "nine fa Sarkin Maladawa Jangero, duk garin nan babu wanda baya shakka ta, kayi kaɗan ka kira ni da shashasha.."
  Ko kallansa Baba baiyi ba, amma sai shima ya dakawa sarkin tsawa yana mai cewa "Yi mana shiru!!! Ka zauna kurum kaji abinda zan faɗa maka"
  Aikuwa babu shiri, kwarjinin muryarƁBaba ta sanyayawa Jangero jiki, sai ya koma ya zauna.
  "Kayi sani cewa Babu wani siddabaru a jikin tsuntsuwa kokila dake sanya zama lafiya a Gazarwa.
Wannan sirri yana tare da adalcin sarki Riji ne.. Yadda yake kyautatawa talakawansa, yake watsa soyayya da albarka ga mabiyansa, shiyasa kowannen su koyi daga gareshi har ni'ima take kwarara a garesu daga sama".
   Baba yaci gaba da cewa "yanzu kwana nawa kokila tayi a tare dakai?".   Sarkin yace "wata ɗaya".
  ƁBaba yace "to na horeka kaje kaga Gazarwa, zaka samu babu abinda ya sauya daga ni'imar cikinta da zaman lafiyar dake gareta".
  Saboda haka, zaifi kyau ka mayarwa da Sarki Riji tsuntsuwar sa ka kuma nemi yafiya, inyaso sai ka koyo sirrin halayensa na tafiyar da mulki".
   Sarki Jangero yayi godiya ga Baba, sannan ya koma gida.
  Kashe gari ya sake shiri saboda rashin natsuwa dangane da halin rashin zama lafiya da kasarsa take ciki yasa aka fito masa da bayin sarki Riji dake garkame a kurkuku, aka fito da tsuntsuwa kokila, sannan ya nufi Gazarwa da hanzari. Babban Burinsa shine aminci ya wanzu a masarautarsa.
  Da zuwansa kuwa ya nemi afuwar sarkin Gazarwa Riji bayan ya kwashe gaskiyar labari ya faɗa masa.
   Sarki Riji yace "haba ɗan uwa, ai wannan ba komai bane. Hakika kana da damar gyara kasar ka ta zama amintacciya kamar wannan".
   Daga nan suka shiga tattauna hanyoyin wanzar da soyayya gami da adalci a kasa.
  Tun daga nan, Sarki Jangero ya saduda, ya daina zaluntar talakwansa, ya zama abin kauna a garesu, kuma kafin wani lokaci sai da zaman lafiya ya samu a ko ina a kasarsa, albarkar noma ta wanzu duk shekara.. Har ma iskar kasar sai data sauya daga mai zafi izuwa iska mai daɗin shaka...

 
   

ALAKAR FIR'AUNA DA HAUSAWA 3

SHIN FIR'AUNAN DA YAYI ZAMANI DA ANNABI MUSA (A.S) BAHAUSHE NE?

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
    08060869978

Kashi na Uku.

Ana iya bin diddigin alakar Misirawa da sauran kabilu ciki kuwa harda hausawa ta hanyar komawa tsoffin zantukan da masana tarihi suka faɗa game da wannan yanki na Afirka.
   Da fari dai, an samu cewa akwai masarauta a Misira shekaru sama da dubu shidda da suka gabata, daga nan aka sake ruwaito cewar an samu ɓullar wata masarauta mai suna 'Nubia' ko 'Kush' ta bakaken fata wadda take karkashin ikon misira, daga baya kuma ta ɓalle daga gareta a wani lokaci wanda karfin daular misira ya fara raunana, har kuma aka ruwaito cewar Waccan masarauta ta Kush ta karɓe iko da Misira a wani lokaci, inda aka samu jerin wasu fir'aunoni bakaken fata (sarakunan misira) waɗanda asalinsu daga Masarautar bakaken fata sukema fito.
   A wancan tsohon zamani, an samu wanzuwar hijira ta misirawa izuwa daular bakaken fata da akace tana wani gari mai suna Napata, saboda raunin daular tasu, bisa mararin samun kuɓuta da cigaban rayuwa, tun daga wuraren shekaru dubu biyu zuwa dubu da ɗari biyar kafin haihuwar Annabi Isa A.S, har zuwa zamanin da Fir'auna Thutmose III ya hau mulki, ya tafi da yaki kasar bakaken fata, ya juma cinye Nubia tare da kafa wani karamin gari mai suna 'Dukki gel' don kare misira daga harin ramuwar gayya a gaba.
  Daga nan sai daular bakake ta tashi izuwa baya daga misira, inda ta kafu a Meroe, wani birni dake kasar Sudan a yanzu.
  Tun daga lokacin kuma akace mutane suka rinka kwararowa yankunan yammaci da gabashi na Afirka domin samun rayuwa mai sauki, saboda azabar yake-yake da azabtarwar masu mulki.
   Marubucin littafin 'Races in Africa' C. G Seligman ya faɗi a shafi na 30 yadda mutane suka rinka kwararowa lokuna da sak'unan afirka da sunan farauta, har ma yace mutanen na rayuwa rukuni-rukuni akalla su 50 zuwa 100.
  Yace kuma Suna da karancin suturu, don haka da ganyaye suke rufe tsiraici, suna kuma da al'adu irin nasu.
  Sannu a hankali, daular Meroe tayi sanyi, daga baya ma wata daula mai suna Aksum ta kafu har kuma ta karɓe ikon ta.
   Ita daular Aksum, kamar gamin gambizar larabawa ne da bakaken fata. Tunda masana tarihi ciki harda Munro Hay marubucin littafin 'Aksum:  An african Civilization of Late Antiquity' sun faɗa cewar Sabiyawa da Kabilun Kudancin larabawa da kuma zaunannun mutanen kasar bakar fata ne suka haɗu a wannan daula suka gina ta.
  Zuriyar da suka haifa kuwa  aka sanyawa suna Abesha.
 Koda yake, littafin 'Book of Aksum' ya faɗa cewar wani mai suna Itiyopis ɗan Kush jikan Annabi Nuhu shine ya soma kafa birnin daular Aksum mai suna Mazaber, wanda ke tsakanin kasashen Ethiopia da Eritrea a halin yanzu. Don haka, tana iya yiwuwa daga bisani mutane suka cika garin har kuma suka haifar da zuriya mai suna Abeshawa.
  Daga nan, mun samu a littafin 'The History of Ethiopia' na A. H. M Jones da Elizabeth Monroe  cewar a zamanin Annabi Sulaiman (wuraren shekaru 900 kafin haihuwar Annabi Isah A.S) alaka ta auratayya ta auku da sarauniyar Sheba, ta daular Aksum har kuma sun samar da zuriya tsakani.
  Haka kuma, daga baya zamanin Annabi Musa A.S (wajajen shekaru 600 kafin haihuwar Annabi Isah A.S) sai akace shima ya auri bakar fata daga daular Aksum kamar yadda yazo a littafin 'History of churches and Monestries of egypt' na Abu Saleh, cewar sarakunan Habashawa jinin Annabi Musa A.S ne, yayinda wasu sukace ai mahaifiyar Annabi Musan ma bakar fata ce daga zuriyar Abesha.
   Ita kuwa waccan kalma ta 'Abesha', itace ta koma 'Habeshat', ta sake sauyawa zuwa 'Habeshi, sannan ta koma 'Habesh', daga baya kuma ta zama 'Habasa' har kuma wasu ke kallonta a matsayin wacce ta sake sauyawa izuwa 'Hausa'..
   Sauyawar Abesha ko Habasa izuwa Hausa na iya zama ta dalilin tasowar wasu daga cikin wancan kabila daga daular Aksum izuwa nan kasar hausa, ta yadda zasu rinka kiran kansu da Habasawa, daga baya kuma a kirasu da Hausawa.
   Don haka, idan har ta tabbata Hausa itace Habasa, babu mamaki idan har alaka ta samu tsakanin su da misirawan lokacin fir'aunan Annabi Musa.
   Dr. Edward Glasser dai shahararen masanin tarihi ne ɗan kasar Austria, ya kuma faɗa cewar Kalmar 'Habesha' ta fito ne daga yaren Mahri, kuma abinda take nufi shine 'Haɗuwa'.
   Daga Habesha ne kuma akace zuriyar Tigra, Agew, Beta Israel da Amhara na kasar ethiopia da Eritrea suka fito.
  Saboda haka, matsawar binciken kimiyya na kwayoyin halittu zai nuna alaka tsakanin kabilun Tigra, Agew, Beta da Amhara kamar yadda alakar harshe ta nuna akwai wani abu tsakaninsu, to tabbas zamu gamsu cewar Habasawa ne suka yo kaura izuwa kasar hausa har kuma suka canza  izuwa Hausawa, sannan kuma suna da alaka da misirawa bama fir'aunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S kaɗai ba.
  Ko kuma duk ba haka ba, kai tsaye Hausawa na iya samo alaka ta tale-tale da Alummar Khemites, waɗanda aka gamsu da cewar sune asalin tushen Misirawa kamar yadda Farfesa Yusuf Adamu ya bada sharshi a Zauren Binciken Tarihin Hausa. Kenan, da kakanni Hausawa, dana midirawa duk ɗaya ne.
  Karshe.
(NB Rashin fahimtane wani yaji aibu don ance Hausawa da Fir'auna nada alaka domin An samu Annabawa fiyayyun Mutane sunyi alaka da mutane masu girman saɓo, kuma da yawan masu amfani da harshen Hausa babu jinin Hausawa na asali a jinin jikinsu. Don haka sai akula da aikata wauta).

ALAKAR FIR'AUNA DA HAUSAWA 2

SHIN FIR'AUNAN DA YAYI ZAMANI DA ANNABI MUSA (A.S) BAHAUSHE NE?

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
    08060869978

Kashi na biyu

  Kimiyyar gwajin kwayoyin halittu, wani ilimi ne wanda ke bin diddigin sauye-sauye da kuma kwayoyin halittun da ɗa kan gado daga iyayensa.
  Don haka, baya da yadda ake amfani da ilimin wajen gane cututtukan dangi da kuma samar musu da magani, akanyi amfani da ilimin wajen bin diddigin dangi da zuri'a da alakar dake tsakanin kabilu.
    Wani binciken baya-bayan nan da wasu masana suka gabatar masu suna Adebowale Adeyemi, Guanjie Chenchen, Yuanxiu Chen da kuma Charles Rotimi da suka fito daga jamiar Ibadan da kuma 'National Genome center' tare da Jamiar Horward, masanan sunce akwai matukar kamance-ceniya tsakanin mafi yawan kabilun afirka.
  Shine ma har binciken ke cewar da alama kabilun Yarabawa, inyamurai, Akan dana Gaa-Adangbe na kasar Ghana, asalinsu daga tsatson mutum ɗaya suka fito saboda kamance-ceniyar dake tsakanin kwayoyin halittunsu.
 Don haka, magana mafi inganci bisa kwayoyin halittar hausawa shine wadda wasu gungun masana suka gudanar akan hausawa mazauna sudan.
   Da fari, Binciken ya nuna cewar kashi arba'in na kwayoyin halittun hausawa dake zaune a sudan sunyi dai-dai dana kabilun sudan ɗin. (Hassan et al 2008)
(Don haka kashi sittin ne gauraye daga kasar hausa, arba'in ɗin kuwa sune na usulin kakannin bahaushe)
   Akwai kuma makamancin binciken daya nuna cewa kwayoyin halittar Hausawa ya nuna cewa su 'yanuwan juna ne da wasu kabilu masu amfani da yaren Nilu mazauna Nigeria, Cameroon, Central Chad da kuma kudancin Sudan. (Toshkoff et al 2009).
   Bakaken fatar chadi dana kamaru dama nan Nigeria duk ana tsammanin sun gangara yankunan da suke rayuwa  ne shekaru da dama da suka gabata daga daulolin sudan.
 Sukuwa mazauna sudan, duk da gaurayuwar kwayoyin halittun larabawa dana sauran kabilu a tattare dasu, an gamsu da cewa su jikokin tsoffin bakaken fata ne na tsohuwar daular nan ta 'Meroa' ko ace 'Kush' wadda ta shahara a duniya wadda akace ta wanzu a sudan ɗin shakaru sama da dubu biya da suka gabata.
   Ta haka, sai ake hasashen cewa kakannin hausawa da kakannin sudawa da kakannin waɗancan kabilu mazauna cameroon da chadi sun fito ne daga tsatson Uba ɗaya, amma hijirar data rinka aukuwa tsakankanin mutanen_da shine sanadiyar rarrabuwarsu ta yadda yanzu kowa yayi nesa da kowa. Hasashen kuma na nuna cewar wannan rarrabuwa ta auku akalla da shekaru dubu huɗu baya zuwa sama, tayadda a iya wancan lokacin ne kowacce kabila tayi chakuɗuwar auratayya da sauran kabilu har kashi sittin na kwayoyin halittarsu ya sauya, kashi arbain ne kaɗai zuwa yanzu bai jirwaya ba, wanda shine na kaka-da-kakanni.
  Babbar hujjar hakan itace  samuwar wasu kabilun daga jikin waɗancan na ainihi, tunda ansani sarai ana ɗaukar tsawon lokaci kafin faruwar hakan.
 Sai kuma tsawon zamanin da daular bakaken fatar tayi a raye har kuma ta rushe. Kamar abinda Marubuci Morton H. Fried ya faɗa a littafinsa mai suna 'The Notion of the Tribe' cewar akwai kabilu na ainihi (primary tribe), akwai kuma kabilu samammu daga na ainihi (secondary tribe).
    Don haka idan har kabilun yahudawa guda goma sha biyu sun fita daga jikin Annabi Yakuba A.s (Israel), to muna iya cewa kabilar Annabi yakuba da yarensa shine kabila ta ainihi, samammun kabilun kuwa sune waɗanda 'ya'yansa sha biyu da jikokinsa suka ɗauka bayan rarrabuwarsu ga wajen zama
     Don haka, binciken ba komai ke nunawa ba sai cewar wancan kaso na kwayoyin halittun dake jikin Fir'auna Remesis II da akace yayi zamani da Annabi Musa, wata alaka ce ta jini wadda ta auku tsakanin kabilun daya fito, da kuma yankin Afirka wanda Hausawa suka fito tun tsawon zamani daya shuɗe.
  Saboda haka, a takaice, binciken kimiyya anan yana nuna mana cewar akwai alaka ta jini tsakanin Fir'aunan da kuma hausawa, koda kuwa tana iya kasancewar ba daga Hausawa kai tsaye Firaunan ya fito ba, ko kuma alakar ta auku ba, amma dai an samu tunda aka samu irin kwayoyin halittunsa ajikin hausawa haka na nufin kakan-nin hausawa na tale-tale suna da alaka ta jini dashi..

ALAKAR FIR'AUNA DA HAUSAWA 1

SHIN FIR'AUNAN DA YAYI ZAMANI DA ANNABI MUSA (A.S) BAHAUSHE NE?

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
    08060869978

Kashi na ɗaya.

Babu jimawa, farfesa Umar Elzakzaky Al-Bahaushe yayi hasashen cewa kwayoyin halittun hausawa dana tsoffin misirawa sunyi kamanceceniya, har ma yace yana kallon kamar firaunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S bahaushe ne.
  A wani rubutu da Dan Jarida Ibrahim A. Waziri ya taɓa wallafawa a jaridar weekly Trust ta ranar 22, ga watan disambar shekara ta 2007, an ruwaito Farfesa Umar El Bahaushe yana cewa "Gaskiya ce bayyanan-niya cewar asalin kalmar 'Hausa' na iya samo tsatsone daga kalmar 'Habasha'" kalmar da ake amfani da ita wurin zayyana wani yanki wanda a yanzu ake kira Ethiopia.
   Haka kuma, ya bada misalin koda kalmar nan ta Hausa  'kwankwaso' tana da ma'ana ɗaya a yaren Amharic na waccan kasa waɗanda akace sun samo salsala ne daga Sarauniya Kandace wacce Annabi Sulaimanu A.S ya aura har kuma suka haifi ɗa dashi.
 Farfesa Umar El zakzaky Al Bahaushe yace" kwayoyin halittar Fir'auna Seti I, wannan daya yayyanka yahudawan zamaninsa, da kuma na magajinsa Fira'una Remesis II, wanda yayi zamani da Annabi Musa A.S sunyi kamanceceniya da kwayoyin halittar mutanen kano na yau, musamman ma na cikin kwaryar badala."
   Sai dai Farfesa Munzali Jibrin, Farfesa Abdullahi Elkanawy da wasu masana da dama sunyi watsi da wannan bincike. Ga abinda ya fito daga makalar masanan kamar yadda suka gabatar a wani taro daya gudana a Arewa House dake kaduna:
   "Kuskure ne a hada asalin wancan Fir'aunan da kano tunda Gawar Mornoptah, dan Fir'auna Remeses II, fir'aunan da aka halakar a ambaliyar ruwa yayin da yake bin sawun Annabi Musa A.S don ya halaka shi, wadda Masani Loret ya gano a shekarar 1898 a tsohon birnin Thebes ta nuna cewar kwayoyin halittar ta sunfi kamanceceniya dana mutanen egypt ne ba mutanen kano ba".
   Koda yake, wasu daga shahararrun mutane a kasar Hausa sun rike a zuciyarsu cewar Tabbas akwai alaka tsakanin Habasha da Hausa, daga cikinsu kuwa akwai Marigayi Malam Aminu Kano da Marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama sule, amm waɗancan masana sunyi ikirarin cewar nwayoyin halittar jana'ar kano dai-dai da wani bincike da sukayi daga wata makabartar kano ɗin, ya nuna sunfi kamanceceniya ne da Sharifai, larabawan Madina ba Fir'auna Remesis ba.
   Akwai kuma wani rahoton masana wanda ya taɓa nuni da cewa shi kansa Annabi Musa (A.S) da yayi zamani da firaunan Misira Remesis II, yana da alaka da Hausawa. Watakila an faɗi hakan ne saboda kasancewar kowa daga masana ya gamsu da cewa  mahaifiyar Annabi Musa A.S bakar fata ce 'yar Habasha.
   Koda yake, wasu na ganin ba abin mamaki bane don an samu alaka ta jini tsakanin Fir'aunonin Misira da hausawa, kasancewar yadda fir'aunonin suka rinka yin yake-yake da kasar bakar fata ta waccan lokaci da ake kira Nubia, kamar misalin firauna Seti I wanda ya gabaci firaunan Annabi Musa A.S, ana ganin yasha tura sojoji yin yaki da Nubia, ciki kuma har da'ya'yansa, tana iya yiwuwa ta hanyar kamen bayi mata da saduwar auratayya zuriya ta fita daga garesu.
    To amma duk ba wannan ba, a shekarar 2013, Shafin DNA Tribes na yanar gizo ya wallafa cewa babban binciken da suka gabatar akan kwayoyin halittar Firauna Remesis II da ake tsammani dashi Annabi Musa A.S yayi zamani, ya nuna cewar kai tsaye kwayoyin halittarsa tafi kamanceceniya data mutanen tsakiyar Afirka.
  Daga nan sai suka ce, kwayoyin halittar kuma suna kamanceceniya da mutanen da suka fito daga Kudancin afirka da kuma Yammaci, watau inda kabilar Hausawa suke kenan.
  Amma kuma kwayoyin halittar gawar ɗansa dake kwance kusa dashi, ta nuna cewa yafi kamanceceniya kai tsaye da mutanen Afirka ta kudu, daganan sai Afirka ta tsakiya, sannan Afirka ta yamma inda hausawa suka fito.
  Wannan duk ga waɗanda suka fahimci kimiyyar kwayoyin halityu, ba komai yake nunawa ba sai cewar tabbas, akwai wani yanki na jinin bahaushe daga fir'aunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S da kuma ɗansa.
   Idan kuwa haka ne, fahimtar mu ga kimiyyar kwayoyin halitta da kuma duban mu ga asalin Habasha, da alakokinta da wannan kasa ta Hausa ne kaɗai zai iya tabbatar mana shin akwai alaka tsakanin Fir'aunan da yayi zamani da Annabi Musa A.S da Hausawa ko Babu?

TARIHIN MARYAM BABANGIDA

MARYAM BABANGIDA

An haifi Marigayiya Maryam matar tashon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekarar 1948 cikin garin Asaba dake kudancin Nigeria.
Mahafiyar Maryam Bahaushiya ce mai suna Hajiya Asabe Halima Muhammaed daga jihar Niger, mahaifinta kuwa ɗan kabilar Ibgo ne, sunansa Leonard Nwanonyeƴ Okogwu.
 Bayan Maryam tayi karatun primary a Asaba, sai ta samu gurbin karatu a kwalejin Amina dake kaduna, daga baya kuma ta karasa karatun sakandiren a Kwalejin Horaswa ta Nigeria dake kaduna.
   Maryam ta samu shaidar Sakatariya a matakin diploma daga Jami'ar Chikago ta kasar Amurka, haka kuma ta samu shaidar karatun Na'ura mai kwakwalwa daga kwalejin NCR dake Ikko.
A ranar 6 ga watan Satumbar shekara ta 1969 aka ɗaura auren Maryam da Ibrahim Badamasi Babangida wanda yake rike da mukamin major na rundunar sojojin  Nigeria.
  A shekara ta 1983 da mijin  Maryam Ibrahim Babangida ya zama shugaban rundunar Sojojin Nigeria, Maryam ta taka gagarumar rawar gani a wannan mulki nasa.
  Da fari dai, ta zamo shugabar kungiyar matan jami'an sojin Nigeria, kuma da wannan mukamin ta soma gina makarantu, asbitoci da wuraren koyar da sana'u ga mata da kuma wurin renon kananun yara.
  Haka kuma a shekarar 1985, Maryam ta samu ɗaukakar matsayi izuwa mukamin da akace ita ta kirkira, watau 'First Lady' lokacin da mijinta Janar Babangida ya zama Shugaban tarayyar Nigeria bayan juyin mulki.
  Ana ganin Maryam ce ta bada shawarwarin yadda za'a kawata gidan shugaban kasa dake Dodon Barrack a Lagos a wancan lokaci, kafim daga baya su taso izuwa Abuja.
  Haka kuma lokacin da su  Gideon Orkar suka so hamɓarar da mijinta daga mulki, har da ita suka so halakawa, amma ta tsere ta ɓarauniyar hanya.
  A matsayin maryam na First Lady a tarayyar Nigeria tun daga shekarar 1985 zuwa 1993, tayi matukar kokari wajen ɗaukaka darajar mata na birni dana karkara a faɗin Nigeria.
  Ta samar da tsarin bada tallafi ga mata, da koyar da sana'o'i,  inganta walwalarsu,  da kuma uwa uba gina cibiyar 'Maryam Babangida National Centre for Women's Development' a shekarar 1993 domin bincike, horaswa da kuma tallafawa mata dogaro dakai.
  A littafinta mai suna 'Home Front: Nigerian Army Officers and Their Wives', wanda ta wallafa a shekarar 1988, Maryam ta nuna darajar 'ya'ya mata da kuma gudunmuwar da kowacce mace zata bayar wajen samun nasarar maigidanta.
  A baki ɗayan lokacin mulkin maigidanta, babu abinda Maryam tasa a gaba sai ciyar da mata gaba.
  A komai nata, tana kokarin yinsa domin amfanuwar matan Nigeria.
  Don haka ta zamo shugaba abar girmamawa ga ɗaukacin matan Nigeria.
 ƁHaka kuma bayan mijinta yabar mulki a shekarar 1993, ta koma gidansa na Minna tare dashi da zama. Sannan taci gaba da ayyukan tallafawa mata da kananun yara, inda ta fara kafa kwaleji mai zaman kanta mai suna 'El-Amin International School' a minna, sannan ta kaddamar da gidauniyar 'Better Life Program' (BLP) don mata a shekarar 2004.
   A iya tsawon rayuwar Maryam Babangida ta samu kyautukan girmamawa da dama, kamarsu 'Harlem Women Committee/ New Future Foundation Incorporated award' da kuma the 'International Recognition Award' a birnin New York cikin shekarar 1988
  A karshe, ta rasu a ranar 15 ga watan nuwambar 2009 bayan tasha fama da rashin lafiya mai alaka da cutar sankarar mahaifa tana da shekaru 61. Ta mutu tabar mijinta, da 'ya'ya huɗu.

TARIHIN AUDU BAKO

9. TARIHIN AUDU BAKO

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
   08060869978

An haifi tsohon gwamnan kano marigayi Audo Bako a barikin 'yan sanda na kaduna cikin shekarar 1924.
  Mahaifinsa ɗan sanda ne, kuma shine sarkin sabon garin kaduna.
  Audu Bako yayi karatun elemantare a Kaduna, sannan ya tafi Zaria yayi kwaleji acan, daga nan ya samu shiga rundunar 'yan sandan Nigeria a shekarar 1942.
 Da fari, Audu Bako ya soma zama malami a kwalejin horas da 'yansanda ta kaduna, sannan a hankali ya rinka samun ɗaukaka ta yadda har saida ya zama mataimakin Kwamishina mai kula da yankin Arewa.

   An naɗa Audu Bako a matsayin Gwamnan Kano da kakinsa na ɗansanda a shekarar 1967 bayan anyi wannan mummunan juyin mulki na shekara ta 1966.
 Tun da hawansa sai ya dukufa wajen inganta kananun hukumomi, da kuma samar da kyakkyawar hurɗa tsakanin gwamnati da sarakuna da kuma talakawan nasa duk kuwa da kasancewarshi shugaba da kakin sarki.
Audu Bako ne gwamnan daya gina kusan ɗaukacin manyan gine-ginen birnin kano. Misali, shine ya gina sakatariyar Audu Bako baki ɗayanta wadda ko a yanzu, yana da wuya a samu wani mahaluki da zaiyi irin wannan gagarumin aiki.
  Baya da haka, ya gina kwalejin aikin Gona a Dambatta wadda aka sanyawa sunansa.
  Haka kuma, Audu Bako ne Gwamnan kano na farko daya soma yunkurin ɗaukaka darajar 'ya'ya mata ta hanyar tsara musu hanyoyin samun ilimin zamani dai-dai da koyarwar Shehu Usmanu ɗan fodio. Sannan a zamanin mulkinsa ne aka soma tsara hanyoyin samun kuɗin shiga daga baki masu yawon buɗe ido. A shekarar 1969 Audu Bako ya soma gina madatsar ruwa ta Bagauda domin samar da ruwan noman rani a Kadawa.
Daga shekarar 1970 zuwa 1973 gwamnatinsa ta gina babban madatsar ruwa ta Tiga bisa burin haɓaka noman rani da yawon buɗe ido.
Ana yiwa Audu Bako lakabi da 'Uban Noman Kano' saboda manyan madatsaai na ruwa daya gina a faɗin jihar kano.
 
Audu Bako yayi ritaya a shekarar 1975 bayan juyin mulkin daya kawo karshen Rasuwar Janar Murtala da aka shirya wanda bai samu nasara ba, sannan ya soma aikin noma a sokoto.
   A shekarar 190 Allah ya yiwa Audu Bako rasuwa. Kuma har gobe shi abin tunawa ne duba da manyan gine-ginen daya yi a kano.