MARYAM BABANGIDA
An haifi Marigayiya Maryam matar tashon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekarar 1948 cikin garin Asaba dake kudancin Nigeria.
Mahafiyar Maryam Bahaushiya ce mai suna Hajiya Asabe Halima Muhammaed daga jihar Niger, mahaifinta kuwa ɗan kabilar Ibgo ne, sunansa Leonard Nwanonyeƴ Okogwu.
Bayan Maryam tayi karatun primary a Asaba, sai ta samu gurbin karatu a kwalejin Amina dake kaduna, daga baya kuma ta karasa karatun sakandiren a Kwalejin Horaswa ta Nigeria dake kaduna.
Maryam ta samu shaidar Sakatariya a matakin diploma daga Jami'ar Chikago ta kasar Amurka, haka kuma ta samu shaidar karatun Na'ura mai kwakwalwa daga kwalejin NCR dake Ikko.
A ranar 6 ga watan Satumbar shekara ta 1969 aka ɗaura auren Maryam da Ibrahim Badamasi Babangida wanda yake rike da mukamin major na rundunar sojojin Nigeria.
A shekara ta 1983 da mijin Maryam Ibrahim Babangida ya zama shugaban rundunar Sojojin Nigeria, Maryam ta taka gagarumar rawar gani a wannan mulki nasa.
Da fari dai, ta zamo shugabar kungiyar matan jami'an sojin Nigeria, kuma da wannan mukamin ta soma gina makarantu, asbitoci da wuraren koyar da sana'u ga mata da kuma wurin renon kananun yara.
Haka kuma a shekarar 1985, Maryam ta samu ɗaukakar matsayi izuwa mukamin da akace ita ta kirkira, watau 'First Lady' lokacin da mijinta Janar Babangida ya zama Shugaban tarayyar Nigeria bayan juyin mulki.
Ana ganin Maryam ce ta bada shawarwarin yadda za'a kawata gidan shugaban kasa dake Dodon Barrack a Lagos a wancan lokaci, kafim daga baya su taso izuwa Abuja.
Haka kuma lokacin da su Gideon Orkar suka so hamɓarar da mijinta daga mulki, har da ita suka so halakawa, amma ta tsere ta ɓarauniyar hanya.
A matsayin maryam na First Lady a tarayyar Nigeria tun daga shekarar 1985 zuwa 1993, tayi matukar kokari wajen ɗaukaka darajar mata na birni dana karkara a faɗin Nigeria.
Ta samar da tsarin bada tallafi ga mata, da koyar da sana'o'i, inganta walwalarsu, da kuma uwa uba gina cibiyar 'Maryam Babangida National Centre for Women's Development' a shekarar 1993 domin bincike, horaswa da kuma tallafawa mata dogaro dakai.
A littafinta mai suna 'Home Front: Nigerian Army Officers and Their Wives', wanda ta wallafa a shekarar 1988, Maryam ta nuna darajar 'ya'ya mata da kuma gudunmuwar da kowacce mace zata bayar wajen samun nasarar maigidanta.
A baki ɗayan lokacin mulkin maigidanta, babu abinda Maryam tasa a gaba sai ciyar da mata gaba.
A komai nata, tana kokarin yinsa domin amfanuwar matan Nigeria.
Don haka ta zamo shugaba abar girmamawa ga ɗaukacin matan Nigeria.
ƁHaka kuma bayan mijinta yabar mulki a shekarar 1993, ta koma gidansa na Minna tare dashi da zama. Sannan taci gaba da ayyukan tallafawa mata da kananun yara, inda ta fara kafa kwaleji mai zaman kanta mai suna 'El-Amin International School' a minna, sannan ta kaddamar da gidauniyar 'Better Life Program' (BLP) don mata a shekarar 2004.
A iya tsawon rayuwar Maryam Babangida ta samu kyautukan girmamawa da dama, kamarsu 'Harlem Women Committee/ New Future Foundation Incorporated award' da kuma the 'International Recognition Award' a birnin New York cikin shekarar 1988
A karshe, ta rasu a ranar 15 ga watan nuwambar 2009 bayan tasha fama da rashin lafiya mai alaka da cutar sankarar mahaifa tana da shekaru 61. Ta mutu tabar mijinta, da 'ya'ya huɗu.

No comments:
Post a Comment