Wednesday, 10 January 2018

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 2


TARIHI: SARAUTAR SARKIN MUSULMI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na biyu.

Sadiq Tukur Gwarzo, GGA.

   YAKE-YAKEN SARKIN MUSULMI MUHAMMAƊU BELLO

Da yake tun kafin rasuwar shehu Usmanu ɗan fodio a shekarar 1817 a sokoto, ya kasance kamar ya rarraba mulkin wasu masarautun ne dake karkashin sa tsakanin manyan mabiyansa, tunda kusan a iya cewa kaninsa Waziri Abdullahi Fodio ke jagorantar Gwandu, ɗansa Muhammdu Bello ke jagorantar Sokoto mazaunin shehu, sai shugabannin yakinsa Aliyu Jedi da Abdussalam Ba'are a Kware.
  Don haka, da shehu ya rasu sai wasu garuruwan sukayi bore, suka ce sam shehu suka sani jagoransu, don haka tunda ya rasu yanzu suna da 'yancin kansu, da yawansu suka kiyin biyayya ga Muhammadu Bello kamar yadda muka kawo cewa an samu rarrabuwa akalla gida huɗu ciki har da Abdullahi fodio wanda sai daga baya yayi mubaya'a gareshi.
   Saboda haka a shekarar farko da mulkin Muhammadu Bello, zamfara tayi masa bore.
 Sarkin musulmi yahau garesu zuwa Burmi ya gwabza yaki dasu.
   A shekarar nan kuma Abdulsalam Ba'are wanda shine a zamanin da Shehu nada rai ya soma kaiwa sarkin Gobir yumfa harin yaki, ya shiga haɗa kai da tsoffin magautansa, ya nemi taimakonsu bisa samun nasara akn Muhammadu Bello.
  Sarkin musulmi Muhammadu Bello yakai masa hari. Akace ya tarfashi kusan kwana biyar a kware suna yaki, daga baya akacishi da yaki a Bakura.
   A shekara ta biyu akaci Kadoye da yaki, mutanen Kebbi kuma sukayi ridda suka koma bautar gumaka dasu da Gobirawa.
  A wannan shekara akaci Kalabaina da yaki.
  A shekara ta uku Sarkin Azbin Ibra ya kawowa sokoto yaki.
Wazirin Sokoto Junaidu ya faɗa cewar "Yana daga karamar Muhammadu Bello samun daidaituwa da abinda yake bushara dashi kamar yadda Waziri Giɗaɗo ya rubuta a littafinsa 'Kashful Bayan' cewar ranar wata juma'a Muhammadu Bello ya baiwa shi wazirin da wasu jama'a labarin zuwan Ibra, inda yace: kada ɗayanku ya makara daga wannan rana, domin ni ina ganin rakumma da sirduna ana bisa garesu tsakankanin ɗakunan musulmai".
   Aikuwa sa'ar da Ibra ya kawo yaki, Muhammadu Bello yayi hawa Izuwa 'Dandoye inda ya sauka, aka gwabza gagarumin yaki, daga karshe Ibra ya sheka da gudu har dokinsa ya faɗi da rawaninsa, suka bar rakumma da sirduna a matsayin ganima, har takai kowanne musulmi na iya kama guda goma..
   A shekara ta huɗu akayi yakin Dakurawa, musulmai suka isa har Matankari da yaki, kuma sukaci garuruwan Azbinawa.
  Acikin tane Zamfarawa suka yi harin Gandi.
   A cikinta kuma Muhammadu ɗan Abdullahi da Muhammadu Buhari suka ɗauki runduna suka tafi garuruwan Yawuri da yaki, suka ci birane masu yawa har ma suka Zarce kasar Nufe da yaki.
  Sa'ar da suke komowa sai suka taras da Zamfarawa da gayyarsu na mutanen yawuri suna dakonsu a iyakar kasar Nufe, ai kuwa anan akayi dagar Ibeto.
  Aka gwabza faɗa matsananci, aka wanzu ana ɗauki ba daɗi ga juna, daga karshe Zamfarawa suka karye, rundunarsu ta tarwatse, suka ɗai-ɗaita, suka gudu suka bar ganima mai yawa...

No comments:

Post a Comment