TARIHI: SARAUTAR SARKIN MUSULMI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.
Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
Gabatarwa.
Kamar yadda mukaji a tarihin jihadin shehu Usmanu ɗan fodio, sarautar sarkin musulmi ta soma ne daga kan shi Shehun kansa, inda ya zamo babban mai bada umarni ga dukkan wata daula da dakaru masu biyayya a gareshi suka kafa ko suka karɓe har tsawon rayuwarsa.
Daga wancan lokacin ne kuma aka samar da tsarin sarautar sarkin musulmi ta zamo sama da sauran sarakunan kasashen hausa, ta yadda duk wanda ya ɗare kan waccan karaga, shine da ikon bada umarni a sauran dauloli.. Wannan abu ya cigaba da kasancewa har lokacin da turawa sukazo kasar hausa, suka karɓe ikonta duka.
Don haka, rubutun zaiyi duba ne tun daga rasuwar Shehu Usmanu izuwa yaki da turawa.
Haka kuma, an ciro mafi yawan tarihin me daga littafin 'Tarihin fulani' wanda Wazirin Sokoto Junaidu ya wallafa, da kuma wasu rubuce-rubuce na masana.
1. SARKIN MUSULMI MUHAMMADU BELLO
Sarkin musulmi Muhammadu Bello ɗan Shehu Usmanu ɗan fodio ne, kuma shine ɗa ga matar Shehu Usmanu ta huɗu mai suna Hauwa, koda yake ana kiranta da Inna Garka.
Haka kuma kamar sauran 'ya'yan shehu Usmanu shahararru irinsu Nana Asma'u da Abubakar Atiku, shima yayi karatun sane a gaban mahaifinsa a Degel har lokacin da akayi hijira izuwa Gudu a shekarar 1803-4.
A lokacin da Allah ya karɓi rayuwar Sarkin musulmi na farko a kasar hausa, kuma mujaddadin musulunci na kasar, watau Shehu Usmanu, sai takaddamar wanda zai gajeshi ta tashi, ciki kuwa har da mabiya kanin shehu kuma wazirinsa Abdullahi bn Fodio da kuma ɗansa Muhammadu Bello.
Ance Muhammadu Bello a Wurno ya kafa sansani yayin da magoya bayansa suka hana kowa shiga sokoto inda cibiyar sarautar take, har dashi kansa Abdullahi fodio.
A wancan lokaci, sai rundunar musulunci ta rarrabu izuwa gidaje kamar huɗu, munafukai suka yawaita samar da zagwan kasa domin wargatsa jihadin da aka soma, amma daga bisani sai Abdullahi fodio ya ajiye adawa da ɗan yayan nasa, inda yayi masa mubaya'a kuma suka haɗu sukaci gaba da yaki tare don jaddada addinin musulunci a kasar hausa.
A zamanin sarautar Muhammadu Bello me wani malami mai suna Alhaji Umar Tall, wanda daga bisani ya kafa daular Tukulur dake senegal ya ziyarci sokoto akan hanyarsa ta dawowa daga aikin Hajji.
Ance Sarkin musulmin ya tarbeshi da martabawa, harma Alhajin yayi rubuce-rubuce a game da haka, sannan Alhajin ya cigaba da zama a sokoto a matsayin Alkali da kuma jagoran yaki har izuwa rasuwar sarki Muhammadu Bello, sannan ya auri ɗiyar sarkin ma a lokacin zamansa a sokoto.
Haka kuma a zamanin Sarki Muhammadu Bello dai, baturen nan mai bincike watau Hugh Clapperton ya ziyarci fadar sarkin musulmi a sokoto a shekarar 1824.
A wancan lokaci, Hugh Clipperton ya rabu da abokin tafiyarsa Denham Oudney wanda akace ya mutu a wuraren wani kauye mai suna Mirmur, wandake tsakanin Katagum da Kano.
Clapperton ya rubuta irin karramawar da sarkin yayi masa da kuma irin hazakarsa ta mulki a ziyararsa ta farko, amma da Hugh ya koma a shekarar 1826 akan hanyarsa ta zuwa ga Alkanemi na Borno, sai sarkin ya hanashi wucewa saboda yakin dake tsakaninsu da masarautar Borno a wancan lokacin. Ana haka ma sai Baturen ya kamu da jante har ya mutu...

No comments:
Post a Comment