TARIHI: SARAUTAR SARAKUNAN MUSULUNCI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.
Kashi na shidda.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
4. SARAUTAR SARKIN MUSULMI AHMADU DAN ATIKU
Kwanaki uku da rasuwar sarkin musulmi Aliyu sai aka yiwa Ahmadu ɗan Abubakar Atiku ɗan shehu Usmanu mubaya'ar sarauta. Yayi alkawari da tsayar da gaskiya da adalci, ya hori mutane da abubuwa huɗu: na ɗaya su bar sayar da gonaki, na biyu subar amsar gunki, na uku su amsa kiran alkalai, na huɗu su amsa kiransa idan ya nemesu tafiya izuwa yakin jihadi.
Akwai daga yake-yakensa yakin Karaziru, da Yakin Sauwa, da yakin ruwan Bore, da yakin Gumi.
Shine sarkin daya rayad da Cimmola, ya gina birni acikinta, da masallatai har ake sallar jumu'a aciki.
Kuma a acikin wannan gari Cimmola ya rasu bayan yayi shekaru bakwai da wata biyu da kwana 26 yana sarauta, yana da shekaru 60 da haihuwa.
Da fatan Allah ya rahamsheshi Amin.
5. SARAUTAR SARKIN MUSULMIƁALIYU NA BIYU
Shine Aliyu ɗan sarkin musulmi Muhammadu Bello, kuma shi ya kasance ɗan uwan Sarkin musulmi Aliyu na farko ne.
Anyi masa mubaya'ar mulki a Chimmola bayan kwanaki huɗu da rasuwar Sarkin musulmi Ahmadu ɗan Abubakar Atiku.
Daga nan sai ya taso izuwa Wurno da zama, shine na shidda da sarautar sarkin musulmi idan aka soma lissafi da shehu Usmanu, amma na biyar daga Muhammdu ƁBello.
Yayi watanni goma sha ɗaya da kwanaki 19 bisa sarauta ya rasu yana da shekaru 60 da haihuwa. Kabarinsa na nan a wurno kusa dana mahaifinsa.
Da fatan Allah ya jikansa Amin.
6. SARAUTAR SARKIN MUSULMI AHMADU RUFAI DAN SHEHU USMANU.
Kwanaki biyar da rasuwar sarkin Musulmi Aliyu, sai akayiwa Ahmadu Rufa'i ɗan shehu Usmanu mubaya'ar mulki a masallacin wurno.
Bai jima awurno ba ya komo sokoto da zama, ya gyara masallatai da gina sababbi, ya rayar da garin sosai, kullum kuma yana cikinsa har ma ana cewa aduk tsawon zamanin sarautar sa kimanin shekaru biyar bai fita daga sokoto ba sai sau uku kacal.
Na farko domin tafiya ginin birnin Silame.
Na biyu domin korar kafirrai daga Kware sanda suka sauka a wata alkarya mai suna kayama.
Na uku ya kara fita zuwa Kware domin ta'aziyyar ɗan uwansa Mallam Isa ɗan shehu Usmanu bin fodio.
A zamaninsa, an samu zama lafiya da kwanciyar hankali a daular musulunci.
Shine sarkin daya soma yanke hannuwan 'yamfashi idan an kamo su tun bayan rasuwar Shehu Usmanu.
Ya rasu yana da shekaru 61, bayan ya shafe shekaru 5 da watanni 6 da kwanaki 20 bisa sarauta. Kabarinsa na sokoto shima.
Daftan Allah ya jikansa amin.
7. SARAUTAR SARKIN MUSULMI ABUBAKAR NA BIYU, MAI RABAH DAN SARKIN MUSULMI MUHAMMADU BELLO.
Daga nan kuma sai aka yiwa Abubakar mubaya'ar sarauta a sokoto.
A zamaninsa anyi yake-yake a kalla guda uku.
Sune:- Yakin gidan karari, da yakin Farintau da yakin Madarumfa.
Wannan sarki ya zamo mai tsoron Allah da kamanta adalci ga mabiya, ya rasu a wurno yana da shekaru 63 da haihuwa. kabarinsa na nan kusa dana mahaifinsa Muhammadu Bello a wurno. Dafatan Allah yajikansa amin.
8. SARAUTAR SARKIN MUSULMI MU'AZU DAN MUHAMMADU BELLO
Daga nan sai akayiwa Jikan shehu na karshe a jerin sarakunan musulunci sarauta, watau Mu'azu ɗan muhammadu Bello a wurno.
A lokacinsa yayi yaki mai tsanani da Sabon Birni, amma bai samu nasarar cinyeta ba kuma yayi kokarin samar da zama lafiya ga masarautarsa.
A karshe ya rasu yana da shekaru 68 da haihuwa bayan yacika shekaru 4 da watanni 9 yana mulki.
Kabarinsa yana nan a sokoto kusa da hubbalen shehu.
Allah yajikansa amin
9. SARAUTAR SARKIN MUSULMI UMMARU DAN ALIYU DAN MUHAMMADU BELLO.
Daga nan sai akayiwa Ummaru mubaya'a nan cikin masallaci Bello a sokoto.
A yake-yakensa akwai yakin Sabon Birni, inda yaje domin ɗaukar fansar uba gareshi, marigayi sarkin musulmi Mu'azu.
Haka kuma ya kai yaki Argungu da Madarumfa.
A zamanimsa ne turawa suka yawaita shigowa kasar sokoto, har aka gane cewa su ba sharifai bane kamar yadda a baya suke ɓoye kansu domin su samu ikon yawo cikin kasa da yin ciniki.
A waɗannan zagaye na turawa suka san kasa dukkanta, suka san koramu da garuruwan kasar hausa, suka isa ga sarkin Musulmi sukayi cinikayya da mu'amala dashi har zuwa rasuwarsa.
A zamaninsa turawa sun bashi agogo don sanin lokaci, da wani gado mai yin fifita da mafitai idan an zauna akansa, da gambuna masu fenti da sauransu.
Haka kuma a zamaninsa, yakan yi zama lokaci lokaci da sarakunan gabas a kauran Namoda.
Kuma a kauran Namoda ɗin ya rasu, yanada shekarun haihuwa 69 bayan yayi shekara 9 da watanni 10 bisa kan sarauta.
No comments:
Post a Comment