Wednesday, 10 January 2018

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 5

TARIHI: SARAUTAR SARAKUNAN MUSULUNCI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na biyar.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

3. SARAUTAR SARKIN MUSULMIƁALIYU BABBA DAN MUHAMMADU BELLO
Anyi masa mu baya'ar sarauta ne a birnin sokoto, cikin masallacin shehu Usmanu tsakanin bayan sallar azahar zuwa la'asar kwana bakwai da rasuwar basambonsa Atiku.
   Shidai ya kasance mai kyawawan ɗabiu, wanda baya wulakanta jama'a, kuma mai rikon addini da horo da ayyukan kwarrai, gashi da son zumunci..
   Yakin sa na farko zuwa Muniya ne.
 Yayi wasiku ga sarakuna na gabas ya sanya wurin gamuwa, sannan ya taso suka gamu a wani wuri d ake kira Riyojin kura, suka yi shiri suka aukawa Muniya, amma basu samu cinyeta ba suka komo da baya.
   Daga nan yayi shirin yaki zuwa Adabka, yaje da kansa ya yakesu yayi rinjaye akansu.
  Bayan ya dawo sai mutanen Tozai sukayi bore, bisa shugabansu Maiyaki.
 Sarkin Musulmi Aliyu yahau garesu ya fatattaki garin har sai da dukkansu suka gudu suka bar gagarumar ganima.
  Daga nan sai yakin Gummi. Ance Sarkinsu ya fita izuwa ɓawar Yari da gayyarsa duka, amma rundunar sarkin musulmi ta yi galaba akansu.
   Bayan ya koma gida sai yayi tattalin yaki zuwa Gobir, daya isa yaga lallai ko anyi yaki babu nasara sai ya dawo gida.
   Sa'ar da shekara ta kewayo sai ya shirya yaki zuwa Madarumfa ya gamu da sarakunan gabas, nan ma yaga jama'ar sa nada rauni, sai ya komo gida.
   Hakakuma ya sake ɗaura aniya zuwa Zauma da yaki, ya tura ɗan uwansa Ahmadu ɗan marigayi sarkin Musulmi Abubakar Atiku yaje yacisu da yaki.
   Daga nan ya haɗa runduna zuwa Tsibiri da yaki, yaje ya samu rinjaye akansu ya dawo.
   Sai kuma ya sake haɗa wata rundunar zuwa Gayari, ya tafi da kansa da dakaru yayi yaki dasu ya ribace su.
   Daya dawo gida kuma sai ya sake haɗa wata tawagar yaki, ya tura ɗan Uwansa Halilu ɗan Hassan ɗan shehu Usmanu zuwa Tagada da yaki, Allah ya basu nasara kuwa suka komo gida da ganima.
   Ana cikin haka sai sarkin Haɗeja Buhari ɗandidi yayi bore daga biyayyar sarkin musulmi. Sarkin musulmi ya tashi waziri Giɗaɗo zuwa gareshi da runduna. Yaje ya yakeshi ya kore shi, ya naɗa ɗanuwansa Ahmadu Dodo a kan sarauta.
   Bayan komawar waziri Abdulkadir ɗan Giɗaɗo sokoto, sai maishishshigi Buharin Haɗeja ya kara motsawa da fitina, nan ma sarkin musulmi ya aike masa da ɗan galadiman waziri Ahmadu Dangiɗaɗo, watau kani ga waziri Abdulkadir don ya yake shi.
  Suka tafi izuwa Haɗeja, suka sake shiri sarkun ta, sannan suka nufi maɓoyarsa bayan an koreshi a Takoka, amma dasuka gamu a wannan karon sai Buhari ya samu nasara akansu.
   Bayan nan, sai aka sake tura Waziri Abdulkadir ɗan Giɗaɗo ga Buharin Haɗeja da tawagar yaki, anan ma basu samu nasara akansa ba.
  To daga nan ne sai Masarautar kano ta karɓi ragamar yakin, shikuma sarkin musulmi Aliyu ya cigaba da mayar da hankulansa akan makwabtansa.
   A wannan lokacin, sarkin musulmi ya aike da tawagar yaki bisa jagorancin sarkin kabi Muhammadu Moyijo zuwa Tumba amma basu samu nasara ba suka komo gida. Babu jimawa kuwa sai aka sake tura wata tawagar bisa shugabancin Sarkin yaki Abdul Hasanu ɗan Aliyu Jedi, anan ma ba'a samu wata nasara gagaruma.
   Daga nan fa sai garuruwa suka soma yin bore ga sarkin musulmi. Saboda suna ganin kamar karfinsa ya ragu sosai.
 Acikin garuruwan da akwai kasar zamfara, da jerma da Kabi.
A lokacin kuma musulmai har sun fara karaya da tsoro.
   Sarkin musulmi Aliyu ya tafi da runduna zuwa Kabi don yakar su. Su kuwa kabawa suka gayyato yanuwansu daga mauri da Jerma, aka gwabza matsanancin yaki a Mera, musulmai sukayi nasara da ikon Allah, aka halaka sarkin su Namabe, aka wargatsa tawagar Augi.
   Bayan runduna ta koma gida, sai sarkin musulmi ya sake haɗa tawaga zuwa Argungu da yaki, akayi karamin yaki acan amma ba'a cita ba aka rabu.
  Babu jimawa da komowarsa daga yakin Argungu, sai akace masa sarkin Baura ya aukawa jihohin Burmi da yaki.
  Nan da nan ya haɗa runduna, ya tafi da kansa har zuwa Tumba, ya tarar sarkin Baura ya gudu, yasa aka bishi a dawakai amma ba'a riskeshi ba,  sai ya dawo gida.
   Haka kuma Sarkin musulmi Aliyu ya samu labarin Mai-shish-shigin nan Maiyaki tsohon sarkin Tozai daya gudu, ya tafi kwatarkwashi yana haɗa runduna don kawo hari.
 Sar Sarkin musulmi yayi shirin yaki ya nufi kwatarkwashi. A lokacin ana cikin tsananin zafin rana da kishirwa, mutanensa nata surutu amma bai kula suba. Sai da akazo za'a buga yaki, sai mutanen kwatarkwashi suka gane ashe Maiyaki ya gudu daga garesu. Don haka babu fafatawa mai tsanani suka mika wuya.
  Sarki Aliyu ya komo gida, akan hanyar sa ya shigo ta hanyar Burmi ya sauka Kasara, wasu daga rundunarsa suka kai yaki Mafara suka dawo, ya tashi izuwa Barbuni, ya sauka yayi umarni akai yaki zuwa Bakura, sannan ya komo gida.
   Yawan yakunan daya hau a zamanin sarautarsa guda 20 ne, ya gyara masallatai a zamaninsa da kuma ganuwar birane. Shine na farkon sanya kofofin karfe a gankwar birane don rufewa.
   A zamaninsa ne wasu mutanen kasar gabas sukayi hasashen zuwan Mahadi, suka ɗaura ɗamara suna jiran bayyanar sa don ya shige musu gaba ya kaisu garin Makkah.
 To amma daga bisani sai aka shafe lamuransu, 'yan kaɗan na mabiyansu ne sukayi saura kamar yadda akace Shehu Usmanu yayi busharar zuwansu a lokacin rayuwarsa.
  A karshe, Allah yayi masa rasuwa a Wurno yana zaman ribaɗi, yana da shekaru 53 da haihuwa, yana kuma da shekaru 17 bisa karagar sarauta.
  Da fatan Allah yajiqansa amin.

No comments:

Post a Comment