TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU
Kashi na ɗaya
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
A wani rohoton bayan bincike da wasu gungun masana suka gabatar game da kwayoyin halittar mutanen zariya a ɗakin taro na 'Arewa House' dake Kaduna karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi El-kanawy da Farfesa Muzzah Jibrin, sun bada bayanin cewar akwai kamance-ceniya tsakanin kwayoyin halittar zazzagawa da kabilun gwari dana igala.
A nasu ba'asin, sun faɗi cewar babu abin mamaki akan haka tunda kowa ya sani sarauniyar zazzau Amina ta taɓa tafiya kasar Igala yaki har aka kasheta acan, don haka tana iya yiwuwa anan aka kame sojojinta a matsayin bayi har kuma auratayya ta shiga tsakani tayadda zuwa yanzu kwayoyin halittun suka cakuɗu da juna.
Sai dai a mafi ingancin zance, anfi ganin cewar zazzagawa, Gwarawa da kabilar Igala sun samo tsatso ne daga tsoffin kabilun da suka soma zama a yankin da ayau ake kira Zaria. Daga baya zariya ta dunkule ta zama kasar hausa, sannan kabilun Igala da Gwari ma duk suka sauya tare da zamowa abinda suke ayau.
Binciken kimiyya a wasu tsoffin wurare dake cikin gundumar zaria ya nuna cewar lokaci mai tsawo kimanin shekaru ɗaya zuwa dubu biyu da suka gabata, akwai mutane zaune a yankin Kufena, Madarkachi, Turunku, Kargi, Tukur-Tukur da Wuchichchiri.
Zuwa yanzu, babu wanda keda tabbacin asalin mazauna waɗancan wurare hausawa ne, amma an gamsu da cewar jikokin sune suka dunkule tare da haifar da daular zazzau.
Masana irinsu Mallam Usman Sulaiman sunbi diddigin tsoffin bayanan da masu bincike suka wallafa kuma suka taskance dangane da wuraren dama yadda daular Zazzau ɗin ta kafu tun asali da rayuwar daular har lokacin zuwan turawa, ga kuma abinda muka samu:-
Tarihin Mazauna Tsohuwar Zazzau.
1. TURUNKU:- Tukurunku yanki ne dake kudancin birnin Zaria mai cike da tsaunika da ni'imar kasa. Ana ganin waɗannan abubuwa sune suka ja hankalin mutane shekaru da dama da suka gabata suka zauna a yankin.
Ana kuma kallon wannan wuri a matsayin tsohuwar cibiyar masarautar zazzau wadda ta haɓaka da makurar wayewa tun lokacin da mutum na farko ya fara rayuwa a wurin sama da shekaru dubu ɗaya da suka gabata izuwa lokacin sarautar sarki Bakwa Turunku na zazzau.
Wasu maruwaita na ganin cewar ainihin mazaunan Turunku kabilar kadarawa ne, domin sune suke kiran sarkin su da suna 'Bugwon', don haka daga baya ne mutane suka maishe da sunan ya koma 'Bakwa'.
Amma wasu na ganin mutanen Toranke na kasar mali sun taɓa kwace garin a zamanin Muhammadu Askiya har kuma hakan ya tilastawa mutanen yankin guduwa zuwa yankin Kufena. Don haka sai ake cewa da wurin 'Toranke' don nuna waɗanda keda ikon sa. Daga baya sai sunan ya sauya izuwa Turunku.

No comments:
Post a Comment